Asabar 25 Yuli 2026 - 22:01
Gwagwarmaya da Jajircewa a Gaban Maƙiyi na Daga Cikin Fitattun Darussan Rayuwar Imam Husaini (A.S) / Muhimmancin Sanin Yazidun Wannan Zamanin (2)

Hauza/ Hujjatul Islam Malakzade ya ce: "Daga wannan mahanga, Ashura tana da saƙo ga dukkan tsararraki. Saƙonta shi ne cewa yin shiru a gaban zalunci da karkacewa ba koyaushe yake nufin rashin shiga ba; wani lokaci yin shiru yana iya zama taimaka wa ɓangaren ƙarya. Don haka mumini ya kamata ya kasance mai basira, fahimta da kare mutuncinsa yayin da yake tsayawa a gaban maƙiyi.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | A sashen baya mun yi magana kan yadda Imam Hussain (A.S) da sahabbansa suka zaɓi yin gwagwarmaya maimakon bin fajirin shugaba duk da kuwa sun san ga abin da zai iya samun su. A wannan karon za mu ci gaba daga inda aka tsaya.

Gwagwarmaya tana nufin kare mutunci da darajar addini a gaban matsin lambar maƙiyi

Hujjatul Islam wal Muslimin Malakzade ya bayyana cewa a makarantar Ashura, gwagwarmaya tana da alaƙa ta kut-da-kut da ɗaukaka da mutuncin ɗan Adam. Ya ce: "Daga mahangar Imam Husaini (A.S.), gwagwarmaya tana nufin kare mutuncin ɗan Adam da na addini a gaban matsin lambar maƙiyi. Mumini na iya fuskantar wahala, killacewa, barazana har ma da kaɗaici, amma babu ɗaya daga cikin waɗannan da ya kamata ya sa ya miƙa wuya ga ƙarya."

Ya ci gaba da cewa: "Juyin Ashura yana koya mana cewa ma'aunin nasara ba kawai rinjaye na zahiri ko na soja ba ne. Wani lokaci mutum yana iya tsayawa kan gaskiya, duk da cewa a zahiri yana cikin tsirarun mutane, kuma hakan ya sa saƙonsa ya kasance abin tunawa har abada. Imam Husaini (A.S.) ya nuna da tsayuwarsa cewa mutunci da darajar mumini ba abin ciniki ba ne."

Wayar da kan jama'a domin kawar da gafala da ruɗi

Wannan malamin Hauza ya ci gaba da yin nuni da irin yadda Imam Husaini (A.S.) ya gudanar da tafiyarsa zuwa Karbala, yana cewa: "Wannan ma'ana ta bayyana ƙwarai a cikin rayuwa da ayyukan Imam Husaini (A.S.). A duk tsawon hanya, ya riƙa yin jawabai na wayar da kai domin bayyana wa mutane hakikanin maƙiyi da yanayin da al'umma ke ciki."

Ya ƙara da cewa: "Imam Husaini (A.S.) yana ƙoƙarin fitar da mutane daga gafala, ruɗu da rashin sani, yana bayyana musu gaskiya. Tafiyarsa ba don yaƙi kawai ba ce, a'a, ɗaya daga cikin manyan manufofinta ita ce farkar da al'umma da kuma bayyana ainihin fuskar zalunci da karkacewa."

Hujjatul Islam Malakzade ya ce: "Daga wannan mahanga, Ashura tana da saƙo ga dukkan tsararraki. Saƙonta shi ne cewa yin shiru a gaban zalunci da karkacewa ba koyaushe yake nufin rashin shiga ba; wani lokaci yin shiru yana iya zama taimaka wa ɓangaren ƙarya. Don haka mumini ya kamata ya kasance mai basira, fahimta da kare mutuncinsa yayin da yake tsayawa a gaban maƙiyi."

Gwagwarmayar Imam Husaini tana tare da ɗabi'a, shiryarwa da cika hujja

Hujjatul Islam Malakzade ya jaddada cewa tsayin daka a makarantar Ashura ba yana nufin neman tashin hankali ba. Ya ce: "Imam Husaini (A.S.), har a ranar Ashura, ya riƙa gabatar da huɗubobi, nasihohi da saƙonni masu yawa domin kiran rundunar maƙiya zuwa ga gaskiya. Wannan yana nuna cewa tsayawa a gaban maƙiyi ya kamata ya kasance tare da kyawawan ɗabi'u, shiryarwa da cika hujja."

Ya ƙara da cewa: "Imam Husaini (A.S.) bai kasance mai son tashin hankali ba. A'a, shi ne abin koyi na gwagwarmaya cikin mutunci, kare gaskiya da ƙin zalunci da karkacewa. Saboda haka, a makarantar Ashura, gwagwarmaya ba ta saɓawa ɗabi'a da mutuncin ɗan Adam, sai ma ya kasance mafi girman misalin shiryarwa, yi wa mutane fatan alheri da ƙoƙarin mayar da su zuwa tafarkin gaskiya."

Gwagwarmayar Imam Husaini ba ta taƙaitu ga fagen yaƙi ba kawai 

Wannan malamin Hauza ya bayyana cewa gwagwarmayar Imam Husaini (A.S.) ba ta takaitu ga kasancewa a filin daga ko yaƙi da maƙiyi ba kawai. Ya ce: "Daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata a fahimta game da makarantar Ashura shi ne cewa gwagwarmayar Imam Husaini (A.S.) ta bayyana ta hanyoyi daban-daban. Wani ɓangare daga ciki shi ne haƙuri a kan musibu, kiyaye natsuwa, kwanciyar hankali da cikakken imani ga Allah Maɗaukakin Sarki."

Ya ci gaba da cewa: "Duk lokacin da Imam Husaini (A.S.) yake ƙara kusantar lokacin shahadarsa, duk da cewa musibu da wahalhalu suna ƙaruwa, sai ya kasance mafi natsuwa, mafi kwarin gwiwa kuma mafi tsayin daka. Wannan saboda ya san yana tafiya ne a kan tafarkin yardar Allah kuma yana sauke nauyin da Allah Ya ɗora masa."

Hujjatul Islam Malakzade ya jaddada cewa wannan irin gwagwarmayar tana nuna cewa tushen juriya ta gaskiya shi ne zurfin imani da dogaro ga Allah. Duk wanda ya yi imani da Allah kuma ya dogara gare Shi, ba zai gaji da tsayawa kan gaskiya ba, domin abin da yake jingina da shi ba ƙarfin duniya ba ne, sai dai alƙawarin Allah da taimakonsa."

Sahabban Imam Husaini (A.S.) – Madubin tarbiyyar Husaini

Ya yi nuni da irin rawar da sahabban Imam Husaini (A.S.) suka taka a Ashura, yana cewa: "Sahabban Sayyidush Shuhada (A.S.) su ma madubi ne na wannan makaranta da tarbiyyar Husaini. Sun san sarai cewa suna fuskantar runduna mai yawa, mai ƙarfi kuma mai kayan yaƙi fiye da su sau da yawa, amma duk da haka ba su bar Imam ɗinsu ba, ba su daina taimakonsa ko kare manufofin gaskiya ba."

Ya ƙara da cewa: "Wannan tsayin daka da sadaukarwa yana nuna cewa mutumin da aka tarbiyyantar a makarantar Husaini ba ya auna gaskiya da yawan mutane, kayan duniya ko ƙarfin zahiri. Ma'auninsa shi ne gaskiya da yardar Allah. Sahabban Imam Husaini (A.S.) sun san cewa za su iya rasa yaƙin a zahiri, amma ba su taɓa yarda su miƙa wuya ga ƙarya ko su sayar da mutunci da gaskiya domin rayuwa cikin wulakanci ba."

Ya ƙarasa da cewa: "Tsayin dakar sahabban Imam Husaini (A.S.) sakamakon tarbiyyar Husaini ne; tarbiyyar da ke koya wa mutum cewa ƙimar gaskiya ta fi rayuwar mutum daraja, kuma kare gaskiya da manufofin Allah yana da daraja fiye da duk wata alaƙa ta duniya."

(Za a ci gaba a Sashe na 3.)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha