A cewar rahoton sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, tattakin ya fara ne a safiyar Juma'a, 31 ga Yuli, 2026, kuma bayan kammala tafiyar ranar farko, mahalarta sun sauka a garin Dutsen Wai domin kwana.
A duk tsawon tafiyar, mahalarta sun kasance suna rera baitocin waƙoƙin juyayin Imam Hussain (A.S.), tare da tuna irin ta'asar da rundunar Yazid (LA) ta aikata a kan Imam Hussain (A.S.) da iyalansa a filin Karbala a shekara ta 61 bayan Hijirar Manzon Allah (S.A.W.W.).
A nasa jawabin, wakilin almajiran Jagora Sayyid Ibraheem Yaqub Zakzaky (H) na Da'irar Bauchi, Sheikh Ahmad Yusuf Yashi, ya yi bayani kan zaluncin da aka yi wa Ahlul Baiti (A.S.) da kuma ƙoƙarin da azzalumai suka yi na kashe hasken addinin Allah.
Ya bayyana cewa sadaukarwar Imam Hussain (A.S.) ta kasance domin farkar da al'umma daga barcin gafala, yana mai cewa a yau miliyoyin mutane a faɗin duniya suna amsa kiransa na tarihi: "Hal min Nasirin Yansuruna?", da amsa: "Labbayka Ya Hussain."
An kammala tattakin ranar farko cikin tsari da natsuwa, yayin da mahalarta ke ci gaba da shirye-shiryen ci gaba da tafiya a rana ta biyu.






Ra'ayinka