Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Wannan rubutun ci gaban rubutun baya ne na "Kyawawan dabi'un Annabi (S.A.W.A); Abin koyi ga Mutanen wannan zamani".
Taimakon Annabi (S.A.W.A) ga wata mata wadda ba Musulma ba; ƙiyayya ba ta hana girmama ɗan Adam ba
Hujjatul Islam Hussaini Qummi ya ci gaba da kawo wani labari daga salon rayuwar Manzon Allah (S.A.W.A), ya ce: A cikin tafsirin Furat Kufi, an kawo labarin wata mata mai suna Sara, wadda bayan Yaƙin Badar ta zo Madina wurin Manzon Allah (S.A.W.A) tana neman taimako. Annabi ya tambaye ta ko ta musulunta? Ta ce a’a. Sai Annabi ya tambaye ta ko ta yi hijira? Ta ce a’a; har yanzu tana kan addininta ne, kuma kawai ta zo wurin Annabi ne saboda tana cikin matsalar kuɗi."
Ya ci gaba da cewa: "Sara na daga cikin matan da suke rayuwa a Makka ta hanyar rera waƙoƙi a majalisun nishaɗi da shagulgula. Bayan Yaƙin Badar da kashe mutane da yawa daga mutanen Makka, waɗannan majalisu sun daina gudana, saboda haka ba ta da wani hanyar samun kuɗi.
Bayan Manzon Allah (S.A.W.A) ya ji matsalarta, ba wai kawai bai ƙi amincewa da buƙatarta ba ne, har ma bai tura ta wajen wani ba. Annabi ya kira danginsa, Banu Hashim da Banu Abdul-Muttalib, ya ce musu: Ku biya bukatun wannan mata, ku samar mata da tufafi da kuɗin rayuwa."
Hujjatul Islam wal Muslimin Hussaini Qummi ya ce: "Wannan ɗabi’a tana nuna cewa kyawawan ɗabi’un Annabi ba su takaita ga abokai da Musulmi ba kawai. Manzon Allah (S.A.W.A) a fagen ɗabi’a da mutuncin ɗan Adam, ya nuna karamci da rahama har ga wanda ba Musulmi ba ne kuma bai yi hijira ba."
Abubuwa biyu da suka sa Manzon Allah (S.A.W.A) ya yi nasara: Kyawawan ɗabi’u da ƙarfafan hujjoji
Ya yi nuni da wannan aya:
«وَ بِمَا رَحْمَةٍ مِنَ اللَّهِ لِنْتَ لَهُمْ وَ لَوْ کُنْتَ فَظًّا غَلِیظَ الْقَلْبِ لَانْفَضُّوا مِنْ حَوْلِکَ»
“Saboda wata rahama daga Allah ce ka yi musu taushi; da a ce kai mai kaushin hali ne, mai taurin zuciya, da sun watse daga gare ka.”
Ya ce: "Idan aka tambaye mu cewa, Annabin da ya sauko daga kogon Hira, wanda a farkon kiransa ya kasance shi kaɗai, kuma mafiya kusa da shi suna cikin sahun maƙiyansa, da me ya samu irin wannan gagarumar nasara a duniya? Amsa ita ce yana da abubuwa biyu masu muhimmanci: kyakkyawar ɗabi’a da kuma hujja."
Hujjatul Islam wal Muslimin Hussaini Qummi ya ƙara da cewa: "Kyawawan ɗabi’un Manzon Allah (S.A.W.A) sun kasance masu karamci har suna tasiri ko a kan maƙiya. A gefe guda kuma, Annabi yana da ƙaƙƙarfan tunani da hujja mai ƙarfi. Alƙur’ani Mai Girma ma ya jaddada waɗannan abubuwa biyu; rahama, taushin hali da kyawawan ɗabi’u tare da kira da hujjar Allah."
Kyakkyawar mu’amalar Annabi (S.A.W.A) da masu sukar sa bayan Yaƙin Hunain
A wani ɓangare na jawabinsa, ya yi magana kan labarin Yaƙin Hunain, ya ce: "Sheikh Mufid (R.A.) ya kawo wani labari a littafin “Al-Irshad” wanda yake bayyana kololuwar karamci da mutuncin Manzon Allah (S.A.W.A).
Bayan Yaƙin Hunain ya ƙare, Manzon Allah (S.A.W.A) bisa wata maslaha da yake dubawa, ya raba ganimar yaƙi tsakanin Muhajirun, amma bai ware wani kaso ga Ansar ba; duk da cewa Ansar sun yi manyan hidimomi ga Musulunci da Manzon Allah (S.A.W.A).
Ya ci gaba da cewa: "Ansar su ne waɗanda bayan hijira suka ba Manzon Allah (S.A.W.A) Madina, suka kuma ba shi kariya. Da a ce Ansar ba su karɓi Manzon Allah (S.A.W.A) ba, ba su ba shi Madina ba, da yanayin ci gaba da gwagwarmayar Musulunci ya kasance mai matuƙar wahala. Saboda haka dabi’a ce su tambayi wannan hukunci, har ma su nuna damuwa."
Ya ƙara da cewa: "Wasu daga cikin Ansar sun yi wasu maganganu a tsakaninsu waɗanda ba su dace da matsayin Manzon Allah (S.A.W.A) ba. Labarin waɗannan maganganu ya isa ga Annabi, amma Manzon Allah (S.A.W.A), duk da kasancewarsa a kololuwar iko da kuma bayan nasarar Yaƙin Hunain, bai zarge su ko wulaƙanta su ba.
Annabi (S.A.W.A) ya saurari masu sukar (Naƙadi) sa a wani taro na musamman
Hujjatul Islam wal Muslimin Hussaini Qummi ya ce: "Manzon Allah (S.A.W.A) ya nemi Amirul Muminin (A.S.) ya shirya wani taro na musamman da Ansar, kuma kada wani mutum da ba daga Ansar ba ya halarta.
Da Ansar suka fahimci cewa Manzon Allah (S.A.W.A) ya shirya wani taro na musamman da su, sai suka yi tunanin cewa Annabi yana son ya zarge su ko ya tsawatar musu.
Amma mu’amalar Manzon Allah (S.A.W.A) ta kasance dabam. Da ya shiga taron, da farko ya yi magana kan hidimomi da sadaukarwar Ansar, ya kuma tunasar da su manyan ni’imomin da Allah Ya ba su ta hannun Manzon Allah (S.A.W.A).
Ya ce: "A yayin fuskantar masu sukar sa, Manzon Allah (S.A.W.A) da farko bai yi watsi da kyawawan ayyukansu da hidimominsu ba, sannan ya yi bayanin dalilin hukuncinsa. Wannan hanya tana daga cikin muhimman misalan kyawawan ɗabi’un Annabi wajen gudanar da al’amuran shugabanci da zamantakewa; wato har ma a gaban waɗanda suka nuna rashin gamsuwa da hukuncinsa, ya mu’amalance su cikin karamci, adalci da ƙauna."
Hujjatul Islam wal Muslimin Hussaini Qummi ya jaddada cewa: "Wannan salon rayuwa yana nuna cewa Manzon Allah (S.A.W.A) bai manta da ɗabi’a ba ko a kololuwar iko. Iko a wajen Annabi ba yana nufin wulaƙanta masu adawa ba ne; a maimakon haka, yayin da ikonsa yake ƙaruwa, karamci, yafiya da kyawawan ɗabi’unsa su ma suna ƙara bayyana."
Kyawawan ɗabi’un Annabi; abin koyi ga yau
Ya ƙara da cewa: "Lokacin da mutum yake nazarin salon rayuwar Manzon Allah (S.A.W.A), ya kamata ya sanya kansa cikin yanayin da Annabin yake rayuwa a ciki; Annabin da a farkon tafarkinsa ya kasance shi kaɗai, mafiya kusa da shi maƙiya ne, kuma maƙiya ba su bar wata hanya ba wajen hana yaɗuwar kiran Allah. Duk da haka, Annabi da ɗabi’a, rahama, hujja, haƙuri, tawali’u da karamci ya sami damar jawo zukata zuwa Musulunci.
Hujjatul Islam wal Muslimin Hussaini Qummi ya ce: "Salon rayuwar Manzon Allah (S.A.W.A) yana koya mana cewa kyawawan ɗabi’u, tawali’u, yafiya, girmama mutuncin mutane da kyakkyawar mu’amala da masu adawa ba alamar rauni ba ne, a’a, suna daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da ƙarfi da nasara."
Manzon Allah (S.A.W.) a kololuwar iko ya kasance bawan Allah mai tawali’u, kuma har ma ga waɗanda suka cutar da shi sosai bai hana kansa rahama da karamci ba. Saboda haka, sanin halayen Manzon Allah (S.A.W.A) da sake nazarin salon rayuwarsa na ɗabi’a, musamman a yayin da ake gab da ranar tunawa da wafatin (shahadar ) Cikamakin Annabawa (S.A.W.A), muhimmiyar buƙata ce ga al’ummar Musulmi."
Ra'ayinka