Laraba 12 Agusta 2026 - 11:12
Saƙon Manzon Allah (S) Shiriya ne da Mafita Ga Dukkan Zamani

Hauza/Abuja: Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya jaddada cewa saƙon Manzon Allah (S) saƙon shiriya ne da mafita a kowane zamani, yana mai cewa abubuwan da suke faruwa a duniya a yau suna da kamanceceniya da wasu daga cikin abubuwan da suka faru a zamanin Manzon Allah (S).

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin ne a yammacin Talata, 27 ga Safar 1448, wanda ya yi daidai da 11 ga Agusta 2026, a wajen rufe taron yini biyu karo na 18 da kwamitocin Mauludin Manzon Allah (S) da Makon Haɗin Kan Musulmi na Harkar Musulunci suka shirya a Abuja.

A cikin jawabinsa, Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya bayyana cewa saƙon Manzon Allah (S) saƙon shiriya ne da mafita ga kowane zamani. Ya ƙara da cewa abubuwan da suke faruwa a duniya a wannan lokaci suna da kamanceceniya da yanayin da ya kasance a zamanin Manzon Allah (S), inda siffofin muminai, mushrikai da munafukai suke bayyana a tsakanin mutane.

Shaikh Zakzaky (H) ya kuma yi magana kan yanayin duniya a yau, inda ya bayyana cewa duniya ta kasu gida biyu: ɓangaren waɗanda suke bin Allah da Manzonsa (S), da kuma ɓangaren Yammacin duniya, wakilan Shaiɗan.

A wani ɓangare na jawabinsa, Jagoran ya yi magana kan bikin Mauludin Manzon Allah (S) na bana, inda ya yi kira da a yi amfani da waɗannan lokuta wajen kusantar juna da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma, tare da wayar da kan jama’a game da abubuwan da suke faruwa a duniya.

Ya jaddada cewa kusantar juna da haɗin kai tsakanin mutane yana taimakawa wajen kawar da katangar rarrabuwar kai da kuma ƙarfafa zumunci a tsakanin al’umma.

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya kuma tunatar da al’umma game da wafatin Manzon Allah (S) da ya faru a ranar 28 ga Safar, tare da jajanta wannan babban rashi. Ya bayyana cewa tunawa da wafatin Manzon Rahama (S) da gudanar da zaman makoki domin tunawa da shi na daga cikin hanyoyin raya addini.

A ƙarshe, Jagoran ya bayyana cewa manufar tunawa da waɗannan muhimman abubuwan tarihi ba wai makoki kawai ba ne, a’a, ana yin hakan ne domin musulmi su ɗauki darasi da ibara daga rayuwar Manzon Allah (S) da abubuwan da suka faru a tarihinsa, su kuma yi amfani da waɗannan darussa a rayuwarsu ta yau.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha