A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da taron ne da yammacin ranar Laraba, 5 ga Agusta 2026, tare da halartar maziyartan Aba Abdillahil Hussain (A.S.) daga Najeriya da Iran, da kuma wasu daga cikin masu masaukin baki na ƙasar Iraki.
A farkon taron, an gudanar da karatun Alƙur’ani mai girma, sannan mawaka suka gabatar da waƙoƙin juyayi da tunawa da shahadar Imam Husaini (A.S.).
Bayani kan falalar ziyarar Imam Husaini (A.S.)
A yayin taron, Mallam Aliyu Tirmizi, wakilin Jagoran Harkar Musulunci ta Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a tattakin bana, ya gabatar da jawabi kan falalar ziyartar Imam Husaini (A.S.).
Ya ce: “An ruwaito cewa duk wanda ya ziyarci Imam Husaini (A.S.) alhali ya san haƙƙinsa, za a ba shi ladan hajji dubu sau dubu karɓaɓɓu, waɗanda aka yi tare da Imamuz Zaman (A.J.).”
Mallam Aliyu Tirmizi ya kuma yi magana kan halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, inda ya jaddada goyon bayan Harkar Musulunci ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Falasɗinu, Hizbullah ta Lebanon, Ansarullah ta Yemen da kuma gwagwarmayar ƙasar Iraki.
Mulki da jagorancin Annabawa da Imamai
A nasa jawabin, Hujjatul Islam Wal Muslimin Abdullahi Ahmad Fudiyya ya yi magana kan ƙoƙarin da wasu ke yi na raba mulki da Annabawa, Imamai (A.S.) da malamai.
Ya bayyana cewa asalin mulki ma na Annabawa ne, yana mai kafa hujja da abin da Allah (T) Ya faɗa game da Annabi Ibrahim (A.S.) cewa Ya ba shi mulki mai girma.
Ya ce: “Saboda haka, duk waɗanda suke ƙoƙarin kore wannan magana, hassada ce take cin su.”
Da yake bayani kan siffofin bayin Allah, wato ‘Ibadur Rahman, Mallam Abdullahi Fudiyya ya yi kira da a koma a duba ayoyi daga 63 zuwa 74 na Suratush-Shu’ara.
Muhimmancin jagorancin Imami wajen gudanar da addini
Hujjatul Islam Abdullahi Fudiyya ya bayyana cewa kuskure ne a takaita addini da yawan yin sallah, azumi, zakka da sauran ibadu kawai, ba tare da kula da ginshikin jagoranci ba.
Ya bayyana cewa ginshikin addini shi ne gudanar da rayuwar addini ƙarƙashin jagorancin Imami daga Allah da wakilansa. Ya ce idan mutum ya gudanar da addininsa ƙarƙashin jagorancin wanda Allah bai yardar masa da jagoranci ba, to, kamar yadda Imam Sadiƙ (A.S.) ya bayyana a wani hadisi, ba zai kasance yana da cikakken addini ba.
Ya ƙara da cewa wannan yana wajabta samar da gwamnatin Musulunci da kuma rayuwa a ƙarƙashinta.
Kira ga ‘yan’uwa da su kasance masu tsayin daka
A ƙarshen jawabinsa, Mallam Abdullahi Fudiyya ya tabbatar wa ‘yan’uwa cewa su kwantar da hankalinsu, domin kiran da Jagoransu yake yi yana kan gaskiya, kuma babu shakka zai kai ga nasara.
Ya kuma yi kira gare su da kada su ruɗu da masu kawo shubuha waɗanda suke ƙoƙarin kautar da ‘yan’uwa daga tafarkin gwagwarmaya.
Musamman ma, ya shawarci ɗalibai da su riƙa ware lokaci a gefen karatunsu na Hauza domin ƙara ƙarfafa tunani da fahimta.
Bayani kan haƙƙin jagora a kan mabiya
Shi kuwa Alhaji Ali Babba, ya yi jawabinsa ne kan haƙƙin jagora a kan mabiya, inda ya ja hankalin ‘yan’uwa kan muhimmancin nisantar mutanen da suke ƙoƙarin bata shaksiyyar jagora ta hanyar shigar da ƙananan maganganu da shubuhohi a hankali har su fara yin tasiri a zukatan mutane.
Ya ce: “Idan aka ce jagora, ana nufin masanin hanya. Duk wanda yake bin jagora, yana nufin shi bai san hanyar ba. Saboda haka, zai rufe ido ya bi duk inda jagoran ya nuna masa.”
Ƙoƙarin samar da abin hawa domin sauƙaƙawa maziyarta
A wani ɓangare na taron, ‘yan’uwa sun tattauna kan ƙoƙarin samar da mota da za ta riƙa ɗaukar kayan maziyarta domin sauƙaƙa musu, maimakon dogaro da motocin haya.
‘Yan’uwa maziyartan da suka zo daga Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen wannan ƙoƙari, tare da yin alkawarin samar da motar da za ta riƙa gudanar da wannan hidima.
A ƙarshen taron, Sheikh Alhassan Sufi ya gabatar da nasiha ga ‘yan’uwa, musamman ɗalibai.
Daga nan ne Mallam Junaidu Kudan ya rufe taron da addu’a.
Taron ya kasance wani ɓangare na shirye-shiryen kammala tattakin Arba’in na Imam Husaini (A.S.) da almajiran Sheikh Ibraheem Yaƙub Zakzaky (H) suka gudanar daga Najaf zuwa Karbala, tare da halartar maziyartan daga Najeriya, Iran da Iraki.








Ra'ayinka