A cewar rahoton sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga shafin Dandalin Matasa na Facebook, a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, 2026 ne, Dandalin Matasan Harkar Musulunci na yankin Funtua (Sayyid Zakzaky Zone), suka kawo zangon ƙarshe na gaggarumin Mu’utamar din da suka shirya na yankin, wanda aka gabatar a garin Tudun Iya.
Da ya ke jawabin rufe taron, Sheikh Ashiru Abdullahi Funtua, ya taɓo kusan dukkan maudu'an da aka tattauna a yayin gudanar da taro, inda ya yi ƙarin jan hankali ga mahalartan dama sauran al'umma baki ɗaya.
Game da lalacewar al'umma a yanzu da kuma yadda su Sayyid Zakzaky (H) su ke ta faɗi tashi wajan ganin wannan al'umma ta gyaru, Sheikh Ashiru ya ce: "Allah maɗaukakin Sarki Ya kimsawa Malam jin cewa wannan ɓarnar ya wajaba a gyara ta, to kuma tunda nufin shi gyara ɓarnar dake da akwai ne, to dole asa mutane su hau kan hanya irin wadda Ma'aiki (S) ya koyar da Sahabbai, domin ba mai yin gyara sai gyararre."
Da ya ke shajja'a mahalarta taron bangaren dogaro da kai. Malamin ya ce: "Zama a cikin tafiyar gwagwarmaya kana da bukatar hanya ta dogaro da kai, domin a wannan rayuwar, mabuɗin fitintinu da rigingimu shi ne tsananin bukata ta lullube mutum bai da yadda zai yi ya yi wannan bukata ɗin, zai koma rokon mutane ne wanda wannan wulakanci ne ga namiji ko mace."
A wani ɓangaren jawabinsa kan kula da shigar mutunci da kyautata hijabi yadda shari'a ta tanada, ya na cewa "Lallai kiyaye dokar Allah ta sanya cikakken hijabi da shiga ta mutunci tana kange al'umma daga faɗawa musifun alfasha da ta ke yawaita a cikin wannan al'umma. Shigar banza da tauye hijabi yadda Allah ya ce mata su sa shi ke sabbaba mafiyawan alfasha a doron ƙasa."
Daga karshe ya ƙare jawabinsa da kiran al'umma zuwa haɗin kai da nisantar rarrabuwa a tsakanin mu inda ya ce: "Yana daga cikin makircin makiya, ba randa za su iya barin suga cewa kan al'ummar Musulmi ya hadu, kullum burinsu shi ne su ga kan al'ummar Musulmi ya rabu, domin idan mun hadu mun dunkule waje daya za mu yi ƙarfi, idan Kuma mukai ƙarfi to su za su yi rauni."
A ɗaya gefen, kafin jawabin rufewa, Malam Nura Isah Bakori ya gabatar da jawabi a kan maudu'i mai taken 'Akhlaƙ, babbar hanya ga matasa wajen isar da sakon Harka Musulunci', Malamin ya fara magana a kan kyawawan ɗabi'u a cikin al'umma yake cewa: "Babu wani wanda yake kusantar da bawa zuwa ga Allah (S), sannan yake sa mishi soyayya da kaunar mutane irin kyakkyawar ɗabi'a."
Ya ci gaba da cewa: "'Jihadun nafs' shi ne ke yaƙi da zuciyarka, ka gyara kanka, to wannan jihadin ya fi jihadin takobi girma, ya fi jihadin takobi wahala, kamar yadda jiki ba ranar da zai zauna ba ya buƙatar abinci, haka shi ma ruhin mumini ne ko da yaushe ya na bukatar kalar nashi abincin, wanda da shi ne yake ginuwa ya yi kyau, to idan ruhinka ya tsarkaka ya yi kyau, shi ne zaka siffantu da dabi'o'i irin na Annabawa masu kira, in ka iya canza kanka to za ka iya canza waninka, amma idan kai baka gyaru ba to 'mustahil' ne ka iya gyara wani."
Kafin gabatar da jawabin, tun da sanyin safiya aka fara gabatar da wasan sada zumunta na kwallon kafa wanda kwamitin wasanni ya shirya tsakanin mahalarta taron, wanda ya gudana tsakanin baƙi da masu masaukin baƙin na taron Mu'utamar din, Inda aka tashi wasan kunnen doki 1-1.
Daga karshe an rarraba shaidar girmamawa ga Matasan da suka samu halartar karatun daura da aka rika shiryawa a 'online' na tsawon sati Huɗu a zauran wakilan matasa na yankin, bayan nan sai jawabin godiya da addu'a aka sallami kowa.










Ra'ayinka