Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Ayatullah al-Uzma Shahid Imam Khamenei (Q) a farkon darussansa na fikihu, ya yi bayanin wani hadisi na akhlaƙ. Taken wannan hadisi shi ne: “Mafi nauyi a cikin mutane da kuma mafi ƙwazo a cikinsu”, daga bakin Manzon Allah, Annabi Muhammad (S.A.W.W).
Ga bayanin kamar haka:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.
An karɓo daga Annabi (S.A.W.A), a ci gaban hadisin da ya gabata:
و امقت الناس المتکبر.
“Mafi abin ƙi a cikin mutane shi ne mai girman kai.” Kalmar “maƙt” na nufin zunubi da kuma nauyin kaya da ake ɗora wa mutum.
Ma’ana, Annabi yana cewa mai girman kai shi ne wanda yake ɗauke da mafi girman nauyin zunubi a kansa.
Wannan saboda irin tasirin da halin girman kai da ganin kai fiye da kowa yake yi a cikin ayyukan mutum, ko a mu’amalarsa da bayin Allah, ko ma da Allah Maɗaukaki. Saboda haka ne girman kai yake sa mutum ya gangara cikin wani rami mai ban tsoro na halaka ta ruhi.
و اشدّ الناس اجتهاداً من ترک الذنوب.
“Kuma mafi tsananin ƙoƙari (ijtihadi) a cikin mutane shi ne wanda ya bar zunubai.”
Wato, mutum mafi ƙwazo a tafarkin Allah shi ne wanda yake guje wa aikata zunubi. Wannan yana nuna muhimmancin barin zunubi wajen ci gaban mutum da kamalarsa.
Mai yiwuwa wani ya ɗauka cewa mafi girman ƙoƙari shi ne yawaita ibadu da mustahabbai. Amma hadisin yana nuna cewa abin da ya fi haka daraja shi ne barin zunubi.
Dalili kuwa shi ne, zunubai suna da tushen da ke cikin zuciyar mutum, sha’awoyi da son zuciya su ne abubuwan da kullum suke jan mutum zuwa ga aikata laifi. Saboda haka, mutum yana buƙatar gwagwarmaya ta dindindin domin ya nisanci zunubi. Kuma asalin al’amarin kenan.
Mutanen da suka kasance masu ma’anawiyyah da sanin Allah, idan suna yi wa matasa da sauran jama’a nasiha game da tafiya a tafarkin kusanci ga Allah, suna ɗaukar mataki na farko a matsayin barin aikata zunubi. Idan babu barin zunubi, to ayyukan alheri, ibadu, sadaka da ƙoƙari a tafarkin Allah ba sa yin babban tasiri.
Misalinsa kamar mutum ne da yake zuba ruwa cikin wani tafki ta manyan bututu masu ƙarfi, amma duk da haka tafkin bai cika ba. Me ya sa? Domin akwai wasu ramuka ko ɓuloli a jikinsa da suke ta fitar da ruwan. Zunubi haka yake.
Duk ibadu da ayyukan alheri da nagarta da mutum yake yi, zuciyarsa ba za ta cika da alheri da tsarkaka ba matuƙar akwai zunubi. Domin zunubi kamar wannan tsaga ko rami ne da ke jikin tafkin, yana ta zubar da abin da ake zubawa.
Saboda haka, abu na farko shi ne a toshe hanyar wannan asara, wato a bar zunubi. Da zarar an yi haka ne, sannan ayyukan alheri za su fara bayar da cikakken tasirinsu.
Ra'ayinka