Asabar 13 Yuni 2026 - 15:36
Cikakken Bayani kan Jana'iza da Taron Bankwana da Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali

Hauza/ Kwamitin taron tunawa da shahadar sadauki kuma shugaba, Ayatullah al-Uzma Khamenei, a cikin sanarwa ta uku, ya bayyana cikakken bayani game da taron bankwana da jana'izar Shahidin jagoran juyin juya hali.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, an buga sanarwa ta uku ta kwamitin taron tunawa da shahadar sadauki kuma shugaba, Ayatullah al-Uzma Khamenei (Kaddasallahu Nafsahu al-Zakiyya).

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

"Daga cikin muminai akwai maza wadanda suka cika alkawarin da suka yi wa Allah, a cikinsu wasu sun riga sun rasu, wasu kuma suna jira, kuma ba su canza alkawarinsu ba."

Sakamakon shahadar babban malami kuma marja'i na duniyar Shi'a, hazikin jagoran juyin juya halin Musulunci, kuma mai rike da tutar gaskiya da gwagwarmaya, sadauki kuma shugaba Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Hussaini Khamenei (Kaddasallahu Nafsahu al-Zakiyya), duniyar Musulunci tana cikin jimami da alhinin rashin wannan babban mutum wanda ya shafe dukkan rayuwarsa mai albarka wajen daukaka kalmar gaskiya, kare Musulunci, hidimtawa mutane, da kuma shiryar da al'umar Musulmi. Wannan shugaba da ya yi shahada, tare da cikakken imani, da gwagwarmaya ta gaskiya, da juriya, da kuma basira ta Ubangiji, ya kasance ko da yaushe yana ɗaukaka tutar 'yancin kasar Iran mai daraja da kuma shiryarwa da ɗaukakar al'umar Musulmi. Sunansa da ambatonsa za su kasance madawwama a tarihin kasar Iran mai daraja, duniyar Musulunci, da kuma cikin zukatan duk mutanen da ke son 'yanci a duniya.

Kwamitin taron tunawa da shahadar sadauki kuma shugaba, Ayatullah al-Uzma Khamenei (A'lallahu Maqamahu al-Sharif), yayin da yake mika ta'aziyya ga Hazrat Waliyyul Asr (ATFS), da kuma sabon Jagoran Juyin Juya Hali Hazrat Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei (Mudda Zilluhul Ali), da kuma dukkan al'ummar da ke son 'yanci da gaskiya, yana mika godiya ta musamman da kuma ban girma ga dumbin al'ummar Iran da dukkan masoyan Musulunci da juyin juya hali saboda halartar taron da suka yi.

Biyo bayan sanarwar da wannan kwamiti ya fitar a baya, da kuma duba da tsare-tsaren da aka yi, ana sanar da daukacin al'umma masu daraja da masu makoki cewa, za a gudanar da taron bankwana, jana'iza, da kuma bizne gawar wannan sadaukin shahidi da tare da sauran iyalansa, wadanda suka hada da shahidai: Dr. Misbahul Huda Baƙiri Kani, Sayyida Bushra Hussaini Khamenei, Zahra Haddad-Adel, da Zahra Muhammadi Golpayegani (Radhiyallahu Anhum Ajma'in) kamar haka:

 - Ranakun Asabar 13 da Lahadi 14 ga watan Tir, shekara ta 1405 (wanda ya yi daidai da 19 da 20 ga watan Muharram): Taron bankwana da gawarwakin shahidai a Masallacin Musalla na Imam Khumaini (Q) da ke Tehran.

 - Ranar Litinin 15 ga watan Tir, shekara ta 1405 (wanda ya yi daidai da 21 ga watan Muharram): Taron jana'iza da jerin gwano a birnin Tehran.

 - Ranar Talata 16 ga watan Tir, shekara ta 1405 (wanda ya yi daidai da 22 ga watan Muharram): Taron jana'iza a birni mai tsarki na Qom.

 - Ranar Alhamis 18 ga watan Tir, shekara ta 1405 (wanda ya yi daidai da 24 ga watan Muharram, daren shahadar Imam Sajjad AS): Taron jana'iza a birni mai tsarki na Mashhad da kuma bizne shi a cikin Haramin Imam Rida (A.S).

Ana gayyatar daukacin mutane masu daraja da masoya, masu son 'yanci na duniya, masoyan makarantar Musulunci, da masu ƙaunar Iran da su halarci wannan babban taro mai kyan gani domin yi wa wannan jagora shahidi rakiya ta ƙarshe.

A ƙarshe, muna godiya ga dukkan hukumomin da abin ya shafa da kuma kungiyoyin farar hula kan shirye-shirye da dabarun da suka samar na gudanar da wannan taro. Muna jaddada cewa babban jigo wajen gudanar da wannan taro shi ne al'umma mai daraja da ke kan gaba ko da yaushe a matsayinsu na ainihin masu makoki, kuma za a samar da wani taro mai kayatarwa da ba shi da tsara na taron al'umma, insha Allah.

Za a sanar da cikakkun bayanai na taron nan gaba ga daukacin al'umma.

Ofishin Kiyayewa da Buga Ayyukan Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

23 ga Khordad, 1405 (13 ga Yuni, 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha