Talata 16 Yuni 2026 - 12:26
Manhajin Rayuwa | Idan Mun Kawar da Batun Hukunci (Azaba), Me Ya Sa Bai Kamata Mu Aikata Zunubi Ba?

Hauza/ Domin mai zunubi ya aikata saɓo, ba shi da wata mafita face yin amfani da ni'imomin da Allah ya ba shi domin yin biyayya gare Shi; wannan kuma yana nufin butulci a fili.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Amirul Muminin Imam Ali (A.S) a cikin Hikima ta 290 na littafin Nahjul Balagha, ya yi ishara da wani mabuɗin tunani game da zunubi da azaba, wanda ake gabatar muku da shi ya ku masana:

Hikima ta 290:

«لَوْ لَمْ یَتَوَعَّدِ اللَّهُ عَلَی مَعْصِیَتِهِ، لَکَانَ یَجِبُ أَلَّا یُعْصَی شُکْراً لِنِعَمِهِ.»

"Ko da a ce Allah bai tsoratar da bayinsa da hukunci a kan saɓa masa ba, to dole ne (wajibi ne) mutum kada ya aikata kowane irin zunubi, domin hakan ya zama hanyar nuna godiya ga ni'imomin Sa."

Ƙarin Bayani:

Wanda yake yin zunubi kuma ba ya cika umurnin Allah, a haƙiƙa yana lalatar da ni'imomin da Allah ya ba shi ne; domin irin wannan mutumin, don ya sami damar aikata zunubi, dole ne ya yi amfani da dukkan ƙarfin da yake cikin jikinsa. Alhalin Allah Maɗaukakin Sarki bai ba shi waɗannan madafun ikon ba domin yin zunubi da saɓo.

Yi tunanin mutumin da yake son ya saɓa wa umurnin Allah ta hanyar aikata zunubi, misali kamar yin sata. Domin ya aiwatar da wannan zunubin, dole ne dukkan gaɓoɓin jikinsa su gudanar da ayyukansu da dukkan ƙarfin da suke da shi don ya sami ikon yin wannan satar.

 *Hancinsa: Dole ne su riƙa shakar iska mai kyau akai-akai domin ya shaki numfashi kuma ya rayu.

 * Zuciyarsa: Dole ne ta riƙa bugawa a kai-akai don jini ya kai ga dukkan jikinsa, hakan ya kiyaye rayuwarsa.

 * Idanunsa: Dole ne su kasance suna da ikon gani domin ya ga hanyarsa.

 * Ƙafafunsa: Dole ne su kasance suna da ikon tafiya da ɗaukar mataki domin ya ci gaba da tafiya a hanyar da yake gani da idonsa.

 * Kunnuwansa: Dole ne su kasance suna da ikon ji domin ya fahimci sautin kusantowar mutane kuma ya gudu daga hatsari.

 * Hannayensa: Dole ne su kasance suna da ikon aiki da motsi domin ya buɗe kofofi kuma ya ɗauki abubuwa.

 * Ƙwaƙwalwarsa: Dole ne ta yi aikinta domin sauran gaɓoɓin jikinsa su karɓi umurni daga gare ta kuma su aiwatar da ayyukansu...

Idan ɗaya daga cikin waɗannan gaɓoɓin, wato ɗaya daga cikin waɗannan ni'imomin da Allah ya ba mutum ba ta yi aikinta daidai ba, mai zunubin ba zai iya aikata zunubin ba. Saboda haka, kana iya gani cewa mai zunubi don ya yi zunubi da saɓo ga Allah, yana amfani ne da su kansu damammaki da ƙarfin da Allah ya ba shi don yin ayyuka na ƙwarai kuma kyawawa.

Bisa wannan tsarin, ashe mai zunubi ta hanyar aikata kowane zunubi ba shi da kansa yake lalatar da ni'imomi da ikon da Allah ya ba shi ba?

Tabbas, Allah ya yi gargaɗi ga bayinsa kuma ya tsoratar da su da zunubi da saɓo. Sai dai idan da a ce Allah bai yi irin wannan gargaɗi da tsoratarwa ba, kuma mutum ya kasance yana da kwanciyar hankali cewa ba za a yi masa horo ko hukunci ba saboda zunubansa, to har yanzu ba shi da damar lalatar da ni'imomin Allah. Wato, domin nuna godiya ga ni'imar gani, ji, shakar ƙamshi, motsi, bugun zuciya, numfashin huhu, tunani, ikon yin ayyuka daban-daban da kuma dubun-dubatar sauran ni'imomi, dole ne mutum ya kasance mai daraja da nuna godiya. Kuma don yin godiya ga waɗannan manya da darajar ni'imomin, bai kamata ya taɓa aikata zunubi da saɓo ga Allah ba.

An ɗakato ne daga littafin "Fand'haye Kuta Az Nahjul Balagha (Gajerun Gargaɗi daga Nahjul Balagha)"

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha