A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, jerin bahasin Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa” ana gabatar da su ne da nufin yada koyarwa da ma’arifar da suka shafi Imam Mahdi (A.F), ga ku masu daraja.
A cikin batun Wilayatul Faƙih, ɗaya daga cikin muhimman batutuwa shi ne hujjojin Wilayatul Faƙih. A koyaushe ana tambayar me ya sa a cikin al’umma ta Musulunci faƙihi yake gabata a kan sauran mutane kuma shi ne yake da ikon jagoranci?
Amsar wannan tambayar ita ce: hujjar Wilayatul Faƙih ana iya fahimtarta ta fuskar hankali da kuma ta fuskar nassosi; wato, hankali yana umartar musulmi ya yi biyayya ga faƙihi a lokacin ɓoyuwar (gaibar) Imam, haka kuma akwai ruwayoyin Musulunci da ke nuna hakan.
Nazari kan hujjar hankali game da Wilayatul Faƙih
Tun da mutum yana rayuwa cikin al’umma kuma yana son kaiwa ga cikakkiyar kamalar ruhaniya ta wannan rayuwa, yana bukatar abubuwa biyu masu muhimmanci:
1. Dokar Allah wadda saboda kasancewarta daga Allah ba ta da kuskure ko rauni. Wannan doka za ta tsara tsarin zamantakewar al’umma kuma bin ta zai tabbatar da jin daɗin kowa. Wannan dokar ita ce Alƙur’ani da Sunnah, waɗanda su ne cikakken shirin rayuwar ɗan Adam har zuwa ranar ƙiyama.
2. Mai aiwatar da doka kuma shugaba mai ilimi da adalci wanda zai kula da aiwatar da wannan doka yadda ya kamata.
A bayyane yake cewa idan babu waɗannan abubuwa biyu – ko ma ɗaya daga cikinsu – al’umma za ta fada cikin rikice‑rikice, lalacewa da fasadi.
Sakamakon wannan hujjar hankali shi ne tabbatar da wajabcin nubuwwar Annabawa, sannan bayan Annabi na ƙarshe, wajibcin Imamancin Imamai Ma’asumai (A.S). Ma’ana, mafi dacewa wajen aiwatar da dokokin Allah da tabbatar da su shi ne Imam Ma’asumi.
Ma’asumi shi ne wanda ba ya aikata kuskure ko zunubi, ba a tunani ba kuma ba a aiki ba. Yanzu idan muka tambayi hankali: idan ba mu da damar samun Ma’asumi fa, me ya kamata mu yi?
Hankali zai amsawa cewa tun da bukatar tsari a cikin al’umma da kuma ƙoƙarin kaiwa ga kamalar ɗan Adam da ta ruhaniya har yanzu suna nan, dole ne a sanya wanda ya fi kusanci da Ma’asumi a wannan matsayi.
Bayani a nan shi ne cewa dalilin dacewar Ma’asumi wajen jagorantar al’umma shi ne cikakken iliminsa ga addini da koyarwar Musulunci, da kuma taƙawarsa, tsoron Allah da kuma tsarkinsa daga kuskure, wanda ba zai bari maslahar al’umma ta salwanta saboda son zuciya ko anfani na kashin kai ba.
Haka kuma wani dalilin dacewarsa shi ne fahimtarsa da saninsa ga al’amuran zamantakewa da kuma iya tafiyar da su.
Saboda haka, idan a wani lokaci kamar lokacin ɓoyuwa (gaiba) ba a iya samun Ma’asumi ba, ya kamata a koma ga wanda ya fi sauran mutane wadannan siffofi. Wannan mutum kuwa shi ne faƙihi mai taƙawa wanda yake da ƙwarewa wajen tafiyar da al’amuran al’umma da jama’a.
Domin wanda ba faƙihi ba ba zai iya sanin addinin Musulunci da dokokinsa da ma’arifarsa yadda ya kamata ba, don ya aiwatar da dokar Allah. Haka kuma mutum mai ilimi amma ba shi da takawa da adalci yana cikin haɗarin bin son zuciyarsa ko tasirin wasu mutane, kuma ba za a iya amincewa da irin wannan mutum ya jagoranci Musulmi ba. Idan kuma ba shi da kwarewar shugabanci, ba zai iya tafiyar da al’amuran jama’a yadda ya kamata ba, kuma a lokutan bukata ba zai iya yanke shawara masu anfani ga al’ummar Musulmi ba.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An samo daga littafin “Negine Afarinish”, tare da ɗan gyara kaɗan
Ra'ayinka