A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, harba waɗannan makamai ya biyo bayan ci gaba da taurin kan da Isra'ila ke yi na ƙin amincewa da sulhu da kuma ci gaba da lalata birnin Beirut. Cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a wannan samame, akwai wasu kalmomi da aka rubuta a jikin ɗaya daga cikin makaman linzamin na Iran, waɗanda suka karɓi babban gurbi a shafukan sada zumunta da kafafen yaɗa labarai na duniya.
Rahotanni sun nuna cewa Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa a Beirut da sauran yankunan Lebanon, yayin da ta sha yin watsi da ƙoƙarin diflomasiyya na tsagaita wuta. Iran ta bayyana cewa wannan mataki nata ya zama dole sakamakon ƙara ruruta wutar rikici da ta'addancin da Isra'ila ke yi a yankin.
Sakon da aka rubuta a jikin makamin linzamin ya zo kamar haka:
"Da sunan Allah, Shi ne wanda ikonsa ya fi ƙarfin kowace rundunar jiragen ruwa na yaƙi, jiragen sama, da kowace dakarun soja. Da sunan Ubangijin Annabi Isa (AS), Ubangijin Annabi Musa (AS), kuma Ubangijin dukkan 'yan adam masu 'yanci na duniya."
Sakon ya ci gaba da jawabi ga al'ummar duniya cewa:
"Mu fa muna yaƙi ne da ƙungiyar masu laifi. Muna yaƙi ne da gurbatattun abubuwa na tsibirin Epstein (Epstein Island). Ba za mu taɓa yin sanyir jiki ko sulhu ba wajen kare al'ummarmu."
A ƙarshen rubutun an ƙara da cewa:
"Yakinmu zai ci gaba domin tsarkake duniya daga fasadi da tsarin ruwa (interest), kuma wannan tafarki yana tafiya ne daidai da koyarwar Annabi Isa (AS) da Annabi Musa (AS)."
A halin yanzu, hotunan wannan makami na linzami da rubutun dake jikinsa suna ta yaɗuwa cikin sauri a shafukan sada zumunta, yayin da ƙasar Iran ke kallon wannan saƙo a matsayin wata alama dake bayyana matsayarta ta siyasa da ta akida a fagen fama.
Ra'ayinka