Alhamis 4 Yuni 2026 - 01:35
Bin Fikirar Imam Khumaini Shi Ne Hanyar Samun Mafita Ga Al'umma / Duniya Tana Buƙatar Komawa Ga Tunanin Imam

Hauza/ Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, yayin da yake jaddada cewa tunani da makarantar koyarwa ta wanda ya assasa Juyin Juya Halin Musulunci tana nan raye kuma tana aiki, ya bayyana cewa bin fikirar Imam Khumaini (R.A) shi ne kaɗai tafarkin ceto da tsallake duniya daga rikice-rikice da ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Jagoran Harkar Musulunci Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), a yayin taron Makon Imam Khumaini karo na 37 da Dandalin Ɗalibai na Harkar Musulunci suka shirya a gidansa da ke Abuja, ya bayyana sassan fuskoki na hanyar rayuwa da tunani na wanda ya assasa Juyin Juya Halin Musulunci.

Bisa rahoton da aka samu daga shafin Facebook na ofishin jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a wannan taro ya siffanta Imam Khumaini (R.A) a matsayin wata baiwa ce ta Ubangiji ga zamanin yanzu, wanda ya canza tunanin al'ummar Musulmi tare da samar da sauye-sauye masu zurfi da tushe a matakin ƙasa da ƙasa.

Yayin da yake nuni da sauye-sauyen da aka samu a kan ma'anar Intizar (jiran bayyanar Imam Mahdi) a makarantar koyarwa ta Imam Khumaini (R.A), ya bayyana cewa: "Imam ya canza wa al'umma tsohuwar fahimta ta zama ba tare da tabuka uffan ba game da wannan batu; domin Intizar a makarantar Imam ba wai kawai zama ne, yin shiru da sauraro ba, aiki ne mai cike da karsashi, madaidanci kuma tare da aiwatarwa wanda yake wajaba a wuyan daukacin al'umma, kafin bayyanar Hazrat Baqiyyatullahil A'azam (A.F) da kuma bayan bayyanarsa."

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya ya ƙara da cewa: "Imam Khumaini (R.A) ya canza yadda duniya ke kallon addini; ta yadda aka fahimci addini a matsayin hanyar samun ƴanci, ɗaukaka da zaman kansa, ba wai hanyar danne mutane da sa su gunguma ba kamar yadda makiya masu girman kai suke yaɗawa kafin nasarar Juyin Juya Halin Musulunci."

Ya ci gaba da cewa, tare da jaddada cewa ainihin iko na zahiri yana hannun mutane ne, Imam ya koyar da duniya cewa nasarar ƙarshe a kan masu girman kai tana samuwa ne kawai ta hanyar yaƙar zalunci, tsayin daka a cikin fitintinu da dogaro na gaskiya ga Allah Maɗaukaki; "Maƙiya na tsoron tasirin fikirarsa a cikin al'umma, wanda hakan ya sa suke ci gaba da yaƙi tare da ƙoƙarin dakile yaɗuwar wannan tunani." 

Sheikh Zakzaky, yayin da yake bayyana cewa Imam Khumaini (R.A) yana nan raye domin fikirarsa, tafarkinsa da makarantar koyarwarsa suna nan raye kuma suna aiki, ya bayyana cewa: "A halin da ake ciki yanzu babu buƙatar ƙirƙirar sabbin hanyoyi, a'a, abin da ya rage wa al'ummar Musulmi kawai shi ne su bi hanyarsa."

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya a ƙarshe ya tunatar da cewa: "Wannan ita ce ainihin fikirar da Shaheed Sayyid Khamenei ya tsaya ƙyam a kanta kuma yake kiyayewa; don haka ne ma duniya a yau don ta tsallake rikice-rikice, tana buƙatar komawa ga fikirar Imam Khumaini (R.A), domin wannan tunani shi ne kaɗai hanyar ceto da rabon al'ummomi."

Bin Fikirar Imam Khumaini Shi Ne Hanyar Samun Mafita Ga Al'umma / Duniya Tana Buƙatar Komawa Ga Tunanin Imam

Bin Fikirar Imam Khumaini Shi Ne Hanyar Samun Mafita Ga Al'umma / Duniya Tana Buƙatar Komawa Ga Tunanin Imam

Bin Fikirar Imam Khumaini Shi Ne Hanyar Samun Mafita Ga Al'umma / Duniya Tana Buƙatar Komawa Ga Tunanin Imam

Bin Fikirar Imam Khumaini Shi Ne Hanyar Samun Mafita Ga Al'umma / Duniya Tana Buƙatar Komawa Ga Tunanin Imam

Bin Fikirar Imam Khumaini Shi Ne Hanyar Samun Mafita Ga Al'umma / Duniya Tana Buƙatar Komawa Ga Tunanin Imam

Bin Fikirar Imam Khumaini Shi Ne Hanyar Samun Mafita Ga Al'umma / Duniya Tana Buƙatar Komawa Ga Tunanin Imam

Bin Fikirar Imam Khumaini Shi Ne Hanyar Samun Mafita Ga Al'umma / Duniya Tana Buƙatar Komawa Ga Tunanin Imam

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha