Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, an shirya wannan silsilar bahasin a kan Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa" da nufin yaɗa koyarwa da ilimomin da suka shafi Imam Mahdi (AF), domin amfanin masu bincike da masana.
Daga cikin mafi muhimmancin hujjoji na nassoshi (ruwayoyi) kan Wilayatul Faƙih, akwai wadannan da za mu kawo:
Wasika (Tauqi'i) Daga Imamin Zamani (AS)
Babban malamin Shi'a, Sheikh Sadouƙ (RA), a cikin littafinsa Kamaluddin wa Tamamun Ni'imah, ya ruwaito wasikar Ishaƙ bin Yaqoub zuwa ga Imam Mahdi (AS). A cikin wannan wasika, an yi tambayoyi da dama ga Imam.
Imamuz Zaman (AS) ya ba da amsa kamar haka:
«وَ أَمَّا الْحَوَادِثُ الْوَاقِعَةُ فَارْجِعُوا فِیهَا إِلَی رُوَاةِ حَدِیثِنَا فَإِنَّهُمْ حُجَّتِی عَلَیْکُمْ وَ أَنَا حُجَّةُ اللَّهِ عَلَیْهِمْ.»
"Amma game da lamuran da suke faruwa (sababbin abubuwa da suka taso), to ku koma ga masu ruwaito hadisanmu a cikin ku; domin su ne hujja ta a kanku, ni kuma hujjar Allah ne a kansu." (Kamaluddin wa Tamamun Ni'imah, Juzu'i na 2, Shafi na 484)
A kashi na farko na wannan wasika, Imam (AS) ya ba da umarni cewa mabiya a lokacin Gaiba su koma ga masu ruwaito hadisan Ahlul Baiti (AS), kuma su tambaye su don sanin ayyukan da suka rataya a wuyansu a kan abubuwan da suka faru.
Anan, ya kamata mu yi tunani a kan su wanene ne ake nufi da "Ruwatu Hadisina" (masu ruwaito hadisanmu)? Kuma menene ma'anar "Al-Hawadithul Waqi'ah" (lamuran da ke faruwa)?
Kalmar 'Hawadith' jam'i ce ta 'Hadisah' (abu mai faruwa). Tunda Imam ya ce a koma ga masu ruwaito hadisai a kan abubuwan da ke faruwa, hakan yana nuna cewa abubuwan da ake nufi da Hawadith su ne lamuran da suka shafi addini da rayuwar musulmi, wadanda ya kamata masu ruwaito hadisai su fayyace wa muminai matsayar addini a kai.
Tambayar anan ita ce: Shin ana nufin matsaloli na ƙashin kai ne (kamar yaddda suke a cikin risaloli na aiki) ko kuwa lamuran al'umma ne baki daya (kamar jihadi da kafirai, tsaron kasa gaban harin maƙiya, alakar siyasa, tattalin arziki, da al'adu da kasashen waje)?
Yana da wahala a ce abin da Imam (AS) yake nufi da Hawadithul Waqi'ah ya taƙaitu ga lamuran kashin kai kawai kamar sallah, azumi, da zakka; domin komawa ga malamai da tambayarsu kan wadannan abubuwa abu ne da ya saba faruwa tun a zamanin sauran Imamai (AS). Mabiya suna komawa ga wakilai da jakadun Imamai saboda nisan gari ko matsalolin tsaro da suka sanya ba a samun ganawa kai tsaye da Imaman.
Asali ma, wannan al'amari ne a bayyane cewa idan ba za a iya samun damar shiga ga Imam ma'asumi ba — ko yana raye a bayyane ko kuma yana cikin gaiba — to dole ne a koma ga malaman addini wadanda suka san Alkur'ani da Sunnah.
Sabanin haka, abin da ake nufi da "Hawadithul Waqi'ah" shi ne lamuran da suka shafi al'ummar musulmi baki daya, kuma wannan ma'ana ta dace sosai da zahirin kalmar "Hawadith".
Su Wanene Masu Ruwaito Hadisan Imamai?
Bisa ga wasikar Imam (AS), mabiya a lokacin Gaiba dole ne su koma ga masu ruwaito hadisai. Kamar yadda aka fada, fahimtar kalaman Ma'asumai (AS) a kan lamuran ɗaiɗaikun mutane ko na al'umma yana bukatar kwarewa ta musamman, domin ciro hukunce-hukunce daga hadisai aiki ne mai rikitarwa. Shi ya sa tun can baya, mabiya suke komawa ga malamai da masana addini na gaskiya.
Sakamakon haka, abin da ake nufi da "mai ruwaito hadisi" ba wai kawai mutumin da yake karanta hadisi ba ne; a'a, ana nufin mutumin da:
1. Ya san tushen hadisai da littattafansu daki-daki, kuma yana iya rabe hadisi ingantacce (Sahih) da wanda ba ingantacce ba.
2. Ya san kowane fanni na kalaman Ma'asumai da yadda ake ciro hukunci daga gare su, kuma ya koyi dukkan matakai da kayan aikin da ake bukata don fahimtar kalaman nasu daidai.
A wurin dukkan musulmi da masu hankali, irin wadannan mutane ba kowa ba ne face Faƙihai (Malaman Fikhu) da Mujtahidai na addini, wadanda ke ciro hukunce-hukuncen Ubangiji daga Alkur'ani da kalaman Ma'asumai a kan dukkan lamuran rayuwa na ƙashin kai da na al'umma baki daya.
Wannan fahimta ta yi daidai da karshen hadisin inda aka ce "Fa'innahum Hujjati Alaikum" (Domin su ne hujja ta a kanku); domin kasancewar mai ruwaito hadisi ya zama "hujja", hakan yana nuna cewa ra'ayinsa da fahimtarsa su ne ma'auni. Idan da a ce komawa kawai za a yi ga kalaman Ma'asumi ba tare da ijtihadi ba, da Imam bai ce "su da kansu" hujjoji ba ne a kanku.
A kan wannan gaɓar, kalaman babban malamin fikihun Shi'a, Sheikh Ansari (RA), suna da bayani sosai inda yake cewa: "Abin da yake a zahiri ga kalaman Imam shi ne cewa, abin da ake nufi da 'Hawadith' shi ne dukkan lamuran da a bisa al'ada, hankali, da shari'a ya kamata a koma ga shugaba ko babba a cikinsu, kuma yana da wahala a ce 'Hawadith' ta takaitu ga hukunce-hukuncen shari'a kawai." (Makasib Muharramah, Juzu'i na 3, Shafi na 554)
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An dauko ne daga littafin "Negine Afarinsh", tare da ɗan gyara kaɗan
(1) Tauqi'i: Kalma ce ta musamman da ake amfani da ita mafi yawa ga wasiku ko rubuce-rubucen Imamin Zamani (AS). A cikin wadannan wasiku, ana rubuta amsoshin tambayoyin mabiya ne, sannan jakadu hudu (Nuwwab al-Arba'ah) su mika su ga mutane.
Ra'ayinka