A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Cibiyar Albasira karkashin Harkar Musulunci a Nijeriya bisa jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta fitar da sanarwar taya murnar zaben Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei (DZ) a matsayin sabon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kuma babban mataimakin Imam Mahdi (A.F), sannan kuma ta sanar da mubaya'arta gare shi.
Cikakken rubutun saƙon shi ne kamar haka:
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيم
ٱللَّهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِسَالَتَهُۥۗ
“Allah ne Mafi sani inda Ya fi dacewa Ya sanya sakonSa.” (Al‑An’am: 124)
A daren Lailatul Qadr, Allah Madaukaki ya yi wa al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wata babbar ni’ima, inda ya sake shimfiɗa hannun wilayar Allah na Waliyyullahi al‑A‘azam a kan al’umma kamar yadda ya saba a baya.
Yanzu kuma, da yardar Allah, sunan babban mutum 'Khamenei' (R) ya sake rayuwa, bayan zabin hikima da hangen nesa da Majalisar Kwararru ta wakilan jama’a ta yi na Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei (DZ). Wannan zabin ya zuba sabon jini a jikin juyin juya halin Musulunci, rundunonin gwagwarmayar muqawama, da kuma gwagwarmayar raunana a duniya.
Muna sake mika ta’aziyyarmu da zuciya mai cike da bakin ciki kan shahadar Maulanmu, tare da sabunta mubaya’armu ga magajinsa na gari Imam Sayyid Mujtaba Khamenei, kuma muna bayyana cewa za mu yi cikakkiyar biyayya ga umarninsa.
Cibiyar Albasira, Karkashin Harkar Musulunci ta Najeriya bisa jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Zakzaky – Qom, Iran
19 Ramadan 1447
18 Isfand 1404
09 Maris 2026
Ra'ayinka