A cewar rahoton sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an shirya tattakin ne domin tunawa da shahadar Imam Husaini (A.S), jikan Manzon Allah (S.A.W.A), da sahabbansa masu tsarki, waɗanda aka kashe a filin Karbala a shekara ta 61 bayan Hijira.
Tattakin ya fara ne da sanyin safiya daga filin wasa da ke kusa da sakatariyar ƙaramar hukumar Suleja. Dubban mahalarta taron, maza da mata, sun yi tattaki cikin tsari da natsuwa, sanye da baƙaƙen tufafi a matsayin alamar jimami da alhini kan zaluncin da aka yi wa Imam Husaini (A.S) da iyalansa da sahabbansa.
Mahartan tattakin sun bi ta manyan titunan garin Suleja, inda suka ratsa unguwar Rafin Sanyi, suka wuce ta Tsohuwar Kwata zuwa garin Kwankwashe, kafin daga bisani su kammala tattakin a filin kasuwar Madallah da ke kusa da garin Zuba a yankin Abuja.
Tattakin ya samu halartar almajirai da masoya Ahlul Baiti (A.S) daga sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da Minna, Suleja, Kaduna, Kontagora, Kano, Sakkwato, Gusau, Katsina, Legas da sauran garuruwa.
An gudanar da tattakin cikin lumana da tsari, kuma an kammala shi cikin nasara ba tare da an samu wata matsala ba.
Ya kamata a lura cewa tattakin Arba'in na Imam Husaini (A.S) ya zama ɗaya daga cikin manyan tarukan addini da ke nuna ƙauna da biyayya ga Ahlul Baiti (A.S), tare da sabunta alƙawarin ci gaba da tafiya a kan tafarkin Ashura a tsakanin al'ummar Musulmi a Najeriya.







Ra'ayinka