Litinin 3 Agusta 2026 - 23:40
An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

Hauza/ A safiyar Lahadi, 2 ga Agustan 2026, ’yan’uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na yankin Kano suka kammala tattakin Arba’in na tunawa da shahadar jikan Manzon Allah (S.A.W.A.), Imam Husaini (A.S.), bayan sun isa garin Kwanar Dangora.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, mahalarta tattakin sun ci gaba da tafiyarsu ne daga garin Gwarmai, inda suka kwana a rana ta uku ta tattakin. An fara tattakin ne ranar Alhamis, 30 ga Yulin 2026, kuma ya ƙare a yau Lahadi bayan mahalarta sun isa Kwanar Dangora, inda aka gudanar da zangon ƙarshe tare da kammala wannan ibada cikin nasara.

Kafin mahalarta su koma garuruwansu, an gudanar da taron rufe tattakin. Taron ya fara da waƙoƙin juyayi da mawakan Ittahadu suka gabatar, ciki har da Zaharaddeen Kode, Nasiru Fudiyya da sauran mawaka.

Waƙoƙin sun ƙara wa taron armashi tare da tunatar da mahalarta darussa da manufofin abubuwan da suka faru a Karbala.

Bayan haka, Dakta Salisu Gumel ya karanta saƙon da ’yan Tabligh suka rubuta zuwa ga al’umma.

Daga nan kuma, ƙungiyar ’yan Tamsiliya ta gabatar da wasan kwaikwayo da ya bayyana abubuwan da suka faru a fadar Yazidu ɗan Mu’awiya bayan an kai Imam Aliyu Zainul Abideen (A.S.) da Sayyida Zainab (S.A.) zuwa fadarsa.

Daga bisani, Shaikh Imamu Kurna ya gabatar da wakilin ’yan’uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Azare, Shaikh Malam Dawud Azare, wanda ya gabatar da muhimmin jawabin rufe tattakin.

An yi kira ga mahalarta da su tsarkake niyyarsu

A cikin jawabinsa, Shaikh Dawud Azare ya yi kira ga mahalarta da su fahimci manufar ibadar da suke gudanarwa, yana mai jaddada cewa wajibi ne Musulmi ya san dalilin duk wani aiki da yake yi.

Ya bayyana cewa ibada ba a gudanar da ita bisa ra’ayin mutum ba, sai dai bisa yadda Allah Maɗaukakin Sarki Ya shar’anta.

Ya ce idan mutum ya yi tattaki kawai saboda yana ganin wasu suna yi, ko domin ya burge mutane, ko kuma saboda wata manufa daban, to abin da zai samu shi ne sakamakon wannan niyya da ya yi.

Sai dai idan ya tsarkake niyyarsa saboda Allah, sannan ya gudanar da ibadar kamar yadda Allah Ya umurta, yana fatan Allah Ya riskar da shi ga Imam Husaini (A.S.), iyalansa da sahabbansa waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare addinin Musulunci.

Shaikh Dawud ya ƙara jaddada cewa duk wanda bai gyara niyyarsa ba, kuma bai fahimci hakikanin ibadar da yake yi ba, zai tashi da abin da ya zaɓa wa kansa.

Saboda haka, ya buƙaci mahalarta su riƙa gudanar da ibadunsu bisa ilimi, fahimta da ikhlasi.

Addinin Allah zai ci gaba da tabbata

A ƙarshen jawabinsa, Shaikh Dawud ya bayyana cewa addinin Allah zai ci gaba da tabbata duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Ya yi ishara da abubuwan da ke faruwa a duniyar Musulmi, daga batun Ɗufanul Aqsa zuwa sauran sauye-sauyen da ke gudana a wannan lokaci.

Daga bisani, Shaikh Yusuf Hamza As-Sudany ya rufe taron da addu’a, sannan aka sallami mahalarta domin komawa garuruwansu cikin aminci.

Mahalarta daga sassa daban-daban na yankin Kano

Tattakin Arba’in na yankin Kano ya haɗa mahalarta daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da Kano, Maiduguri, Azare, Jigawa, Nguru da sauran yankuna da dama na Da’irar Kano da kewaye.

An kammala tattakin Arba’in cikin nasara, inda mahalarta suka koma garuruwansu bayan kammala wannan tafiya ta tunawa da Imam Husaini (A.S.) da shahidan Karbala.

An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

An Kammala Tattakin Arba’in Na Yankin Kano A Kwanar Dangora Cikin Nasara 

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha