A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daidai lokacin da ake gudanar da tarukan Arba’in din Imam Husaini (A.S.), dubban Musulmai almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) a jihar Kaduna sun gudanar da tattakin Arba’in daga Kaduna zuwa Zariya, a safiyar Lahadi, 18 ga Safar 1448H, daidai da 2 ga Agustan 2026.
An gudanar da tattakin ne domin tunawa da shahadar Sayyidush Shuhada Imam Husaini (A.S.) da sahabbansa a Karbala, da kuma tunawa da wahalhalun da iyalan Manzon Allah (S.A.W.A.) suka fuskanta bayan aukuwar Ashura, musamman yadda aka tilasta musu tafiya daga Karbala zuwa Sham da kuma fadar Yazidu, cikin yanayi mai tsananin wahala da zafin rana.
An raba tattakin zuwa rukuni huɗu
Domin sauƙaƙa halartar Musulmi daga sassa daban-daban na Kaduna da garuruwan da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, an raba tattakin zuwa rukuni huɗu, inda dukkan rukunonin suka fara tafiyarsu kusan lokaci guda.
Rukuni na farko ya fara tattaki daga Barakallahu zuwa Ɗankande, inda mahalarta suka tsaya domin hutawa. Daga nan suka ci gaba da tafiya har zuwa Maraban Jos, inda aka gudanar da taron rufe wannan rukuni a Babban Masallacin Juma’a na garin. Malam Auwal Hayi ne ya gabatar da jawabin rufewa.
Rukuni na biyu ya fara tafiya daga Babban Masallacin Juma’a na Maraban Jos, inda suka bi hanyar Jos zuwa Kaduna kafin su koma babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya. Sun ci gaba da tafiya har zuwa Unguwar Pate da ke Jaji, inda aka kammala wannan ɓangare na tattakin a Makarantar Fudiyya. Malam Abdullahi Umar, wakilin ’yan’uwa Musulmi na Maraban Jos, ne ya gabatar da jawabin rufewa.
Rukuni na uku ya fara tattaki daga Kan-Kwana da ke Unguwar Pate, Jaji. Mahalarta sun ci gaba da tafiya cikin yanayin makoki, suna rera waƙoƙin juyayi tare da tunawa da irin zaluncin da aka yi wa iyalan Manzon Allah (S.A.W.A.).
Sun isa Kwanar Faraƙwai, inda suka tsaya domin hutawa na ɗan lokaci, sannan suka ci gaba da tafiya har zuwa Lambar Zango, inda aka kammala wannan zangon. Alaramma Malam Abubakar Sa’id ne ya gabatar da jawabin rufewa, sannan aka gudanar da addu’a tare da sallamar mahalarta.
Rukuni na huɗu ya fara tafiya daga Lambar Zango, inda mahalarta suka ci gaba da tattaki cikin yanayin juyayi da alhini har suka isa Taryan Sarki, wani gari da ke kusa da Zariya. Bayan ɗan hutawa, mahalarta suka ci gaba da tafiya har suka shiga birnin Zazzau. Daga nan aka karkatar da hanyar tattakin ta Ƙofar Kuyanbana zuwa kasuwar Zariya, inda aka gudanar da babban taron rufe tattakin.
Malam Aliyu Bakin Ruwa ne ya gabatar da jawabin rufewa, inda ya ƙarfafa mahalarta da su ci gaba da jajircewa da tsayawa kan wannan tafiya, tare da bayyana fatan cewa a nan gaba za a koma gudanar da tattakin cikin yanayin da aka saba yi kafin waƙi’ar shekarar 2015. Bayan kammala jawabin, an gudanar da addu’a tare da sallamar mahalarta.
An kammala tattakin lafiya
Rahotanni sun nuna cewa an kammala tattakin a dukkan rukunoni huɗu cikin lafiya da aminci, ba tare da wata barazana, matsala ko tangarda ba.
A wurare daban-daban da tattakin ya ratsa, an ga mazauna garuruwan suna tsayawa domin kallon mahalarta. Wasu daga cikinsu sun nuna farin ciki da yadda aka gudanar da tattakin, tare da yaba wa mahalarta da yi musu addu’ar fatan alheri.
Hanyar Kaduna zuwa Zariya na daga cikin muhimman hanyoyin da ake gudanar da tattakin Arba’in a baya. Kafin waƙi’ar shekarar 2015, mahalarta kan fara tattakin ne daga cikin birnin Kaduna har zuwa Zazzau, inda ake shafe kwanaki ana gudanar da wannan tafiya ta tunawa da Imam Husaini (A.S.) da shahidan Karbala.
Ra'ayinka