Litinin 3 Agusta 2026 - 23:04
Ziyarar Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Hajji da Ziyara Maukibin Ofishin Jagora Sheikh Zakzaky a Hanyar Najaf zuwa Karbala

Hauza/ A yayin gudanar da tattakin Arba’in na Imam Husaini (A.S.), Sheikh Ridha’i, wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci mai kula da harkokin Hajji da ziyara, tare da Sheikh Muhammad Jawad Abu Qassem da Sheikh Haji Agah Amini, sun ziyarci maukibin Ofishin Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da ke Amudi na 1117, a kan hanyar Najaf zuwa Karbala.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga shafin Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), a yayin ziyarar, Sheikh Muhammad Jawad Abu Qassem ya gabatar da takaitaccen jawabi, inda ya bayyana alfaharinsa da samuwar babban malami kuma jagora irin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), tare da jaddada muhimmancin samun mataimaka da masu goyon bayan irin wannan shaksiyya.

Ya ce: “Muna alfahari da samuwar shaksiyya mai girma ta Sheikh Zakzaky, sai dai akwai buƙatar samun mataimaka ga wannan shaksiyya, wanda ku ne waɗannan mataimaka.”

Ya kuma jaddada cewa ya kamata mahalarta tattakin Arba’in su yawaita addu’a a wannan hanya, saboda muhimmancin abin da tattakin Arba’in yake ƙunshe da shi da kuma babban matsayinsa.
A ƙarshe, Sheikh Muhammad Jawad Abu Qassem ya gabatar da addu’a domin samun tabbatuwa da dawwama, tare da yin addu’a ta musamman ga manyan malaman addini (Maraji’ai). Haka kuma ya yi addu’a ta musamman ga Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).
An gudanar da ziyarar ne a ranar 19 ga Safar 1448H, yayin da miliyoyin masu ziyartar Imam Husaini (A.S.) ke ci gaba da tattaki daga Najaf zuwa Karbala domin gudanar da bukukuwan Arba’in.
Ziyarar Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Hajji da Ziyara Maukibin Ofishin Jagora Sheikh Zakzaky a Hanyar Najaf zuwa Karbala
Ziyarar Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Hajji da Ziyara Maukibin Ofishin Jagora Sheikh Zakzaky a Hanyar Najaf zuwa Karbala
Ziyarar Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Hajji da Ziyara Maukibin Ofishin Jagora Sheikh Zakzaky a Hanyar Najaf zuwa Karbala
Ziyarar Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Hajji da Ziyara Maukibin Ofishin Jagora Sheikh Zakzaky a Hanyar Najaf zuwa Karbala
Ziyarar Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Hajji da Ziyara Maukibin Ofishin Jagora Sheikh Zakzaky a Hanyar Najaf zuwa Karbala
Ziyarar Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Hajji da Ziyara Maukibin Ofishin Jagora Sheikh Zakzaky a Hanyar Najaf zuwa Karbala

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha