A cewar wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Isa Zadeh, mamba a kwamitin ilimi na Cibiyar Bincike kan Kimiyya da Al’adun Musulunci, a yayin taron makokin shahadar Imam Hasan Mujtaba (A.S) da aka gudanar a masallacin ofishin yada addinin Musulunci na Hauzar Ilimi ta Qum, ya yi bayani dalla-dalla kan siffofin “aboki na gaskiya” daga mahangar Mai daraja na Ahlul Baiti (A.S), bisa koyarwar Alƙur’ani Mai Girma da tafarkin Ahlul Baiti (A.S).
A farkon wannan taro, ya ambaci wata hadisi daga Manzon Allah (S.A.W) inda ya ce:
«اَلْحَسَنُ وَ اَلْحُسَیْنُ سَیِّدَا شَبَابِ أَهْلِ اَلْجَنَّةِ»
"Hasan da Husain su ne shugabannin samarin mutanen Aljanna."
Sannan ya fara bayaninsa yana jaddada muhimmiyar rawar da abokan zama suke takawa wajen gina halayen mutum.
Malamin Hauza da Jami’a ya bayyana cewa: “Babu shakka abin da ke gina halayen mutum — bayan nufi, buri da kuma shawarar kansa — abubuwa ne daban-daban, daga cikin mafi muhimmancinsu akwai abokin zama, aboki da kuma wanda yake mu’amala da shi. Domin mutum ko yana so ko baya so yana tasirantuwa, kuma wani babban ɓangare na tunaninsa da halayensa na ɗabi’a yana samuwa ne ta hanyar abokansa. Wannan gaskiya ta tabbata ta fuskar ilimi da kuma ta hanyar gogewa da abubuwan da ake gani a rayuwa.”
Mamba a kwamitin ilimi na Cibiyar Bincike kan Kimiyya da Al’adun Musulunci ya ƙara da cewa: “Wannan tasiri daga mahangar tsarin tunanin Musulunci ya kai wani matsayi da Amirul Muminina Ali (A.S) ya yi magana game da rawar aboki wajen sanin halin mutum, inda yake cewa: ‘Idan ya kasance yana da wahala gare ku ku tantance halayen mutum da ɗabi’unsa, kuma ba ku san irin riƙonsa da addini ba, to ku duba abokansa. Idan abokansa masu riƙo da addini ne, shi ma mai bin addinin Allah ne; amma idan abokansa ba su damu da addini ba kuma ba su da tsari, to shi ma ba shi da wani rabo daga tafarkin gaskiya.’” (Biharul Anwar, juzu’i na 74, shafi na 197)
Kamar yadda aka ce: “Ka fara gaya mini waɗanda kake zama tare da su, sannan zan gaya maka ko kai wanene.”
Hujjatul Islam wal Muslimin Isa Zadeh ya yi nuni da mahangar Alƙur’ani game da batun abota, inda ya ce: “Alƙur’ani Mai Girma ya yi gargaɗi a wasu ayoyi game da yin abota da maƙiyan Allah, masu aikata zunubi da masu gurɓatattun halaye, kuma ya hana mu kusantar su, ko da kuwa waɗannan mutane ‘yan uwa ne ko makusantanmu. Musulunci duk da cewa ya jaddada muhimmancin kyautata zumunci, amma ya bayyana cewa idan waɗannan mutane ba sa kan tafarkin gaskiya da hanyar Allah, bai kamata a yi abota da su ba.”
Ya yi nuni da aya ta 22 a cikin Suratul Mujadala: “Ba za ka sami mutanen da suka yi imani da Allah da ranar lahira suna son waɗanda suke adawa da Allah da Manzonsa ba, ko da kuwa sun kasance ubanninsu, ko ‘ya’yansu, ko ‘yan’uwansu, ko danginsu.”
Siffofin aboki nagari daga mahangar Imam Hasan Mujtaba (A.S)
Malamin na Hauzar Ilimi ya bayyana a babban ɓangaren jawabinsa mai taken “Siffofin aboki nagari daga mahangar Imam Hasan Mujtaba (A.S)”, yana naƙaltowa daga Junaada bn Abi Umayya cewa a lokacin shahadar Imam Hasan (A.S), lokacin da aka nemi ya yi nasiha, Imam ɗin ya bayyana ma’aunin aboki nagari kamar haka:
Idan kana buƙatar samun aboki, ka yi abota da wanda yake da waɗannan siffofi:
1. Ya kasance abin ado gare ka:
Kasancewarsa tare da kai ya ƙara maka daraja; wato halayensa da ayyukansa yayin kasancewarsa tare da kai su zama abin da zai sa ka samu mutunci a gaban mutane, kamar ado gare ka.
2. Ya kiyaye mutuncinka:
Idan ka yi masa hidima ko alheri, ya kiyaye mutuncinka da darajarka.
3. Mai taimako:
Idan ka nemi taimakonsa, ya taimake ka.
4. Mai tabbatar da maganarka:
Idan ka yi magana, ya tabbatar da maganarka.
5. Mai goyon bayanka a gaban maƙiyi:
Idan ka fuskanci maƙiyi, ya ƙarfafa ka.
6. Mai magance matsaloli:
Idan matsala ta faru a cikin aikinka ko rayuwarka, ya taimaka wajen kawar da ita.
7. Ba ya manta alheri:
Idan ya ga alheri daga gare ka, ba ya mantawa da shi.
8. Mai amsa buƙata da gaggawar bayarwa:
Idan ka miƙa masa hannun neman taimako, kada ya hana ka abin da zai iya bayarwa; kuma idan ba ka faɗa masa bukatarka ba, shi ya riga ka wajen bayarwa.
9. Ba ya jawo maka wahala:
Idan matsaloli da bala’o’i suka same shi, kada ya jawo maka baƙin ciki ko wahala; ka yi abota da wanda ba za ka samu cutuwa ko bala’i daga gare shi ba.
10. Ba ya karkatar da kai:
Ta dalilinsa kada ka samu karkacewa a hanyoyinka da tafiyarka.
11. Ya fifita ka a kansa:
Idan wani lokaci aka samu sabani tsakaninku wajen raba wani abu (kamar dukiya ko wani abu daban), ya fifita ka a kansa.
Madogara: Biharul Anwar, juzu’i na 44, shafi na 139.
Ra'ayinka