Litinin 3 Agusta 2026 - 22:06
Arba’in Ya Samo Asali ne Daga Saƙon da Sayyida Zainab (S.A.) Ta Bar Wa Duniya / Ƙarfafa Ilimi Ita Ce Hanya Daya Tilo ta Amsa Shubuhohi

Hauza/ Ayatullah mai girma Jawadi Amuli ya bayyana cewa: “Tattakin Arba’in ya samo asali ne daga wannan saƙo mai ɗorewa da Sayyida Zainab Kubra (S.A.) ta isar, inda ta bayyana cewa: ‘Ba za mu taɓa yin shiru ko gushewa ba.’”

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Jawadi Amuli ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Hujjatul Islam wal Muslimin Ghulam-Hussain Muhsini-Eje'i, shugaban Hukumar Shari’a ta Iran, a garin Damavand, yayin da yake magana kan gabatowar kwanakin Arba’in na Imam Husaini (A.S.).

Ya bayyana wannan gagarumin motsi na Arba’in a matsayin sakamakon al’adar “Ya Husaini” da kuma dawwamammen saƙon  Sayyida Zainab Kubra (S.A.), inda ya ce: “Tattakin Arba’in ya samo asali ne daga wannan saƙo mai ɗorewa da Sayyida Zainab Kubra ta bayyana cewa: ‘Ba za mu taɓa yin shiru ko gushewa ba.’”

Jawabin Sayyida Zainab (S.A.) ya karya tunanin Jabr na Banu Umayya

Wannan babban malamin addini ya ci gaba da cewa kalaman Sayyida Zainab (S.A.) a Kufa ba magana ce kawai game da kuka da musiba ba, a’a, magana ce mai zurfi da ta tsaya kai tsaye wajen ƙalubalantar tunanin karkataccen Jabr.

Ya ce lokacin da Ubaidullah bn Ziyad ya tambayi Sayyida Zainab Kubra (S.A.) cewa: “Kin ga abin da Allah Ya aikata da ɗan’uwanki?” ko kuma lokacin da ya ce: “Allah ne Ya kashe Ali bn Husaini a Karbala!”, wannan ba magana ce kawai game da “ni” ko “mu” ko Banu Umayya ba, a’a, magana ce da ake danganta abin da ya faru ga Allah, wato magana ce daga mahangar tunanin Jabr.

Sai Sayyida Zainab (S.A.) ta amsa masa da cewa: “Ma ra’aytu illa jamilan”, wato: “Ban ga komai ba face kyakkyawa.”

Ayatullah Jawadi Amuli ya bayyana cewa ma’anar hakan ita ce: Aikin Allah kyakkyawa ne, amma ku ne masu kisan kai; ku ne kuka kashe Ali bn Husaini. Ta haka ne Sayyida Zainab (S.A.) ta karya tunanin Jabr na Banu Umayya tare da bayyana gaskiyar ’yancin zaɓin mutum da alhakin da yake ɗauka kan ayyukansa.

Ƙoƙarin shekaru 40 wajen tafsirin Alƙur’ani

Ayatullah Jawadi Amuli, yayin da yake ishara zuwa shekaru arba’in na ƙoƙarin ilimi wajen tafsirin Alƙur’ani Mai Girma, ya bayyana cewa wannan babbar makarantar ilimi mai tushe ta shafe shekaru arba’in tana gudanar da aikin tafsirin Alƙur’ani, ta hanyar ƙoƙarin tsararraki huɗu na ɗalibai da malamai, inda kowace tsara ta yi ƙoƙari na tsawon shekaru goma ba tare da gajiyawa ba.

Ya ce idan rubuta tafsirin “Tafsirul-Tasnim” ya ɗauki lokaci mai tsawo, hakan ya faru ne saboda an samu sababbin batutuwan ilimi da kuma sabbin tambayoyi da matsaloli da suka taso a cikin waɗannan shekaru.

Wannan marja’in ya ƙara da cewa a gaban kowace matsala da tambaya, waɗannan tsararraki sun yi ƙoƙari, kuma an samu amsoshin matsalolin da aka gabatar.

Saboda haka, wannan aikin tafsiri ba aikin mutum guda ba ne. Ya ce: “Wannan ba magana ce ta ladabi ko yabo kawai ba, gaskiya ce bayyananniya; wannan aiki sakamakon ƙoƙarin gama-garin Hauzar Ilimi ne.”

Ƙarfafa ilimi ita ce hanyar amsa shubuhohi

Ayatullah Jawadi Amuli ya jaddada cewa Hauzar Ilimi dole ne ta kasance a shirye a kowane lokaci wajen amsa shubuhohi, suka da sabbin tambayoyi.

Ya bayyana cewa Hauza za ta iya bayar da amsa ne kawai idan ta kiyaye cikakken iliminta da kuma ci gabanta na ilimi. Saboda haka, ya zama dole a koyar da bayyana muhimman ƙa’idoji da tushe na ilimi, kamar “Asalatul Hurriyya” wato ƙa’idar ’yanci, da sauran ginshiƙai masu alaƙa da wannan a Hauzozin Ilimi ta hanyar ilimi mai zurfi.

Ilimin gaibu ba hujjar yanke hukuncin shari’a ba ne

Ayatullah Jawadi Amuli ya kuma yi ishara da matsayin ilimin gaibu a fikihun Musulunci, inda ya bayyana cewa ilimin gaibu ba hujjar da ake dogaro da ita wajen yanke hukuncin shari’a ba ce.

Ya ce saboda haka, Ma’asumai (A.S.), duk da cewa suna da ilimin Allah, a lokacin yanke hukunci suna yin hukunci ne bisa hujjoji da rantsuwa, kamar yadda aka ruwaito cewa sun ce: “Ni dai ina yin hukunci a tsakaninku ne bisa hujjoji da rantsuwa.”

Ya ƙara da cewa idan wani mutum ya mallaki haƙƙin wani ta hanyar shaidar ƙarya, to a zahiri ya tanadar wa kansa wuta ne. Amma hukunci a tsakanin mutane zai kasance bisa hujjojin da ake iya gani da kuma ma’aunin Shari’a.

Halartar al’umma wajen kare juyin juya halin Musulunci wata alama ce ta taimakon Allah

A wani ɓangare na jawabinsa, Ayatullah Jawadi Amuli ya bayyana irin gagarumar halartar al’umma da kuma sadaukarwar da suke yi wajen kare Juyin Juya Halin Musulunci da ƙasar a matsayin wata alama ta taimakon Allah.

Ya kafa hujja da wannan aya ta Alƙur’ani:

﴿هُوَ الَّذِي أَيَّدَكَ بِنَصْرِهِ وَبِالْمُؤْمِنِينَ﴾

“Shi ne Wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa da kuma ta hannun muminai.”

Ya bayyana cewa Allah Maɗaukakin Sarki yana fitar da muminai zuwa fagen yaƙi domin taimakon addininSa, kuma wannan halartar da maza, mata, matasa da sauran sassan al’umma suke yi cikin sani, misali ne na taimakon Allah.

Ya ƙara da cewa Allah ɗaya da Ya ba Musulmi manyan nasarori a farkon Musulunci, a yau ma yana da ikon taimakon al’ummar da suka yi imani. Ya ce a Yaƙin Badar, ba Musulmi suka yi tsammanin za su yi nasara ba, haka kuma maƙiyansu ba su yi tsammanin za su sha kashi ba, amma nufin Allah ya kasance kan cika alkawarinSa.

Addu’a ga shahidai da neman nasarar masu hidima ga tsarin Musulunci

A ƙarshen jawabinsa, Ayatullah Jawadi Amuli ya girmama tunawa da dukkan shahidan Musulunci da Juyin Juya Halin Musulunci, musamman Shahidin jagora, yana roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya tashe su tare da shahidan Karbala.

Haka kuma ya roƙi Allah Ya ba masu hidima ga tsarin Musulunci nasara wajen kiyaye wannan amana ta Ubangiji, domin su isar da wannan tuta zuwa ga mai ita na asali, wato Hazrat Waliyyul Asr (A.F.).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha