Talata 23 Yuni 2026 - 13:47
An Ɗaukaka Amon Sakon Neman Adalci Na Ashura A Jihohin Bauchi Da Yobe A Najeriya

Hauza/ Sakamakon shiga rana ta bakwai na watan Muharram 1448H, almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a garuruwa daban-daban na Najeriya sun gudanar da tarukan juyayi da raya makarantar Karbala cikin halartar dubban mutane.

A rahoton da sashen kasa da kasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, masoya da mabiya iyalan gidan Manzon Allah (AS) a fadin Najeriya, sun ci gaba da gudanar da tarukan bayani da na makoki domin tunawa da ranaku na shida da na bakwai na zaman juyayin watan Muharram. Wadannan taruka, wadanda Harkar Musulunci a Najeriya ta shirya, sun sami halartar masana, malamai na Mazhabobi daban-daban, da kuma daukacin musulmi masu neman gaskiya da adalci.

1. Bayyana Manufofin Juyayin Husaini a Garin Gashu'a

A garin Gashu'a, an gudanar da zaman juyayi na ranar bakwai ga Muharram inda malamin ɗarikar Tijjaniyya Khalifa Sheikh Muhammad Nura Adam Gashu'a ya gabatar da jawabi. Wannan babban malami ya bayyana falsafa da manyan manufofin yunkurin Shugaban Shahidai (AS) inda ya jaddada cewa: "Fitowar Imam Hussaini (AS) ba ta taba kasancewa domin neman mulkin duniya, iko, ko wata fa'ida ta abin duniya ba; Face dai fitowa ce ta tsarki domin raya gaskiya, kafa adalci, yaki da zalunci, da kuma kare koyarwa ta gaskiya ta Musulunci irin na Annabi Muhammadu (SAWW)."

Malamin ya kuma yi kira ga al'ummar Musulmi da su karfafa hadin kai, fahimtar juna da zaman tare, musamman a daidai wannan lokaci da duniyar Musulmi ke ciki.

2. Yaba wa Siffofin Sadaukarwar Karbala a Maiduguri

Zaman juyayin a garin Maiduguri ya gudana ne cikin halartar matasa kuma masoya iyalan gidan Manzon Allah (AS) masu dimbin yawa. A yayin wannan zama, Malam Lukman Abubakar Wakil daga cikin malaman Ɗarikar Qadiriyya ya gabatar da jawabi inda ya ce: "Shugaban Shahidai (AS) ta hanyar sadaukar da jininsa mai tsarki da na iyalansa, ya nuna mafi daukakar misali na sadaukarwa domin kare addinin Musulunci da tabbatar da adalci. Kuma a yau, wajibinmu ne mu tsaya kan tafarkin darajoji na addini da daukar darasi daga wannan makaranta."

3. Bayyana Rashin Ɗabi'a da na Dan Adam na Bala'in Hana Ruwa a Jaji-Maji

A garin Jaji-Maji, an ci gaba da gudanar da zaman makokin na Muharram tare da jawabi daga Malam Muhammad Sani wanda shi ma Malamin Ɗarika ne. Ya mayar da hankali kan batun kange kogin Furat ga sansanin iyalan gidan Annabi (AS), inda ya nuna rashin tausayawa na wannan musiba, yana mai cewa: "A Karbala, hana ruwa ga mata, tsofaffi, da yara kanana marasa laifi, ya fitar da batun ruwa daga matsayinsa na bukatar rayuwa kawai, ya mayar da shi ma'aunin gwada ɗabi'a da mutuntaka. Wannan lamari yana koya mana cewa zalunci ba koyaushe yake kasancewa da takobi ba, wani lokaci yana bayyana ne ta hanyar hana taimako ga wanda yake bukata a lokacin tsanani; Saboda haka, Karbala babban darasi ce ga daukacin tarihin dan Adam."

4. Jaddada Tsayuwa kan Gaskiya a Garin Nguru

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a garin Nguru su ma sun taru a wuraren zaman juyayi domin alhinin ranar bakwai ga watan Muharram. A wurin wannan taro, Malam Aminu Ɗan Limamin Baɓura ya yi amfani da abubuwan da suka faru a tarihin Karbala wajen jaddada muhimmancin tsayuwa kan gaskiya da adalci a cikin al'umma a yau, tare da kira ga muminai da su kasance masu juriya a kan imaninsu.

5. Yaba wa Marikin Tutar Karbala a Giade da Misau

A lokaci guda kuma, garuruwan Giade da Misau sun shaida gudanar da tarukan na juyayin Ashura cikin shauki da natsuwa.

 A Giade, Malam Salisu Tumfafi, Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a na Tumfafi ya yi bayani kan riwayoyi da labaran da Manzon Allah (SAWW) ya bayar tun kafin aukuwar abin da zai faru ga Imam Hussaini (AS) a Karbala.

 A Misau, Sheikh Ishaƙ Sabo ya gabatar da jawabi mai taken "Gudummawar Sahabban Imam Hussaini (AS)", inda ya tabo musibar da ta sami madaukin tutar Karbala, yana mai cewa: "Abul Fadl Abbas (AS) shi ne cikakken misali na cika alkawari, sadaukarwa, da jarumta a tarihi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa lokacin da yake kokarin debo ruwa ga masu kishirwa a sansanin Imam Hussaini (AS)."

Kammalawa da Sakon Karshe

Bisa ga rahotannin da aka samu, dukkan wadannan taruka sun gudana ne cikin kwanciyar hankali, tsaro, da yanayi na natsuwa da ruhi. Mahalarta taron a karshe sun karkare da addu'o'in samun mafita ga al'ummar Musulmi da nasarar masu gyara a duniya, tare da jaddada bukatar ci gaba da amfana da darussan Karbala madawwama, kamar neman gaskiya, sadaukarwa, hakuri, da tsayuwa da yaki da rashin adalci.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha