Bisa rahoton da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya samo daga sashin kasa da kasa, mabiya da masoyan Ahlul-Baiti (AS) sannan kai-tsaye almajiran Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sayyid Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky (H), a kwanakin farko na watan Muharramul-Haram 1448 (Yuni, 2026), sun gudanar da faretin juyayi tare da kafa tarukan makoki domin raya sadaukarwar Karbala a nahiyar Afirka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, jigon shirye-shiryen ranar 4 ga watan Muharram ya mayar da hankali ne kan bayyana irin zaluncin da aka yi wa jariri ɗan wata shida a Karbala, da kuma sabunta alƙawari da tsayin daka akan tafarkin fafutuka da shahada.
1. Da'irar Kano: Amon Kuka Da Juyayi Ya Cika Garin Kano
Bisa rahoton da wakilan Kamfanin Dillancin Labaran Hauza suka samu daga babban birnin Kano, an gudanar da gagarumin taron juyayin "Ranar Abdullahi Ar-Radhi (AS)". Bayan bude taro da addu'a daga Malam Sambo Sokoto da karatun Alkur'ani daga bakin Gwani Malam Aminu Dawanau, 'yan Ittihadu karkashin jagorancin Malam Abdurrahman Kazaure sun gabatar da bugun kirji. Hakanan an gudanar da tamsiliyya (wasan kwaikwayo na musamman na kwatanta Karbala) da display daga matasa da suka taba zukatan mutane har suka fashe da kuka. A dai cikin tsare-tsaren taron yau an yi bajekolin hotunan ɗaliban makarantar Minab dake jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka da Isra'ila suka yi wa ruwan bama-bamai domin kara fito da irin asalin Yazidawan da na wannan zamanin.
A cikin babban jawabin sa, Alhaji Mustapha Gadon Kaya (Mustapha Umar Baba) ya fadi cewa: “Ko a zamanin jahiliyya, Larabawa ba sa yanke kan jariri a yaki, amma a Karbala azzaluman Bani Umayya sun take kowane irin hakin bil'adama ta hanyar harbin wuyan jariri mai kishirwa da kibiyar Harmala mai guba.” Bayan haka, wakilin 'yan'uwa na Da'irar Kano, Shaikh Dakta Sunusi Abdulƙadir Ƙoƙi, ya jaddada cewa: “Za mu iya sadaukar da yaranmu gaba ɗaya saboda Abdullahi Ar-Radhi (AS).”
2. Birnin Zariya: Bayyana Gwagwarmayar Sayyida Rubaba (SA) A Makarantar Fudiyyah
Rahoton da muka samu daga birnin Zariya (wato cibiyar ilimi da addini ta mabiya Ahlul-Baiti a Najeriya) shi ma ya nuna an gudanar da babban taron iyaye mata na Ashura a makarantar ilimi ta "Fudiyyah" dake yankin Babban Dodo.
A taron, wanda ya sami gagarumar karbuwa daga iyalai, Sheikh Abdulhamid Bello, wakilin almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na shiyyar Zariya, ya gabatar da jawabi. Babban abin sha'awa a taron shi ne yadda iyaye mata suka taho da jariransu sanye da tufafi koraye da kalmomi masu rubutun "Ya Hussain", suna kuka tare da nuna juyayin irin halin da Sayyida Rubaba (SA) ta shiga. Iyayen na Najeriya sun daga jariransu sama a matsayin alamta cewa a shirye suke su sadaukar da mafi soyuwar abubuwan da suka mallaka domin kare Musulunci na gaskiya.
3. Birnin Gombe: Take Hakkin Dan Adam Da Dokokin Yaƙi Da Banu Umayya Suka Yi
A birnin Gombe kuwa, an gudanar da taron makoki na rana ta uku da taron jama'a na musamman. A yayin taron, Sheikh Muhammad Abbare, daya daga cikin manyan malamai a Najeriya, yayin da yake bayyana danyen aikin da aka yi wa Abdullahir-Radi (AS), ya kawo bayanai kan dokokin soja da ka'idojin yaki a Musulunci.
Yana mai jaddada cewa azzaluman gidan Bani Umayya sun rubuta babban shafi na rashin mutuntaka ta hanyar harbin jariri mai kishirwa da ba shi da kariya, Sheikh Abbare ya fada wa iyaye cewa: “Idan kuka ga yayanku sun fuskanci azzalumai da dakarun girman kai na zamani, ku sanya gagarumar sadaukarwar da Shugaban Shahidai (AS) ya yi ga jaririnsa a filin Karbala ta kasance abin koyi a gare ku.”
4. Garin Sara: Muryar Neman Adalci Da Yaki Da Zalunci
A lokaci guda, muminai da mabiya na garin Sara a rana ta hudu ta makokin Imam Hussaini sun taru domin sauraron abubuwan da suka faru da Ahlul Baiti masu daraja. Malam Imamu Zakariyya, mai jawabi a taron, ta hanyar sake karanto labarin danyen aikin da Harmala ya yi na harbin wuyan Abdullahir-Radi (AS) da kibiya mai kawuna uku, ya bayyana irin tsananin rashin tausayi na makiya Ahlul-Baiti (AS).
Mahalarta taron na addini, bayan sun yi makoki da bugun kirji, sun jaddada alkawarin tabbatuwa kan ka'idojin neman adalci, hakuri, juriya, da kuma yaki da kowane irin azzalumi a duniya karkashin jagorancin Sayyid Zakzaky.
Addu'ar Neman Nasarar Musulunci Da Lafiyar Jagora
Bisa rahoton na Hauza, wadannan taruka masu albarka wadanda aka gudanar cikin tsari da yanayi na musamman na mika wuya a sassa daban-daban na Najeriya, an kammala su da sallar jam'i da karanta addu'o'i, tare da rokon gaggauta bayyanar Shugaban Zamani (ATFS), samun nasara da daukakar Musulunci da Musulmi a fadin duniya, da kuma neman kariya da tsawon rai mai albarka ga babban mai gyara na Afirka, Sayyid Ibraheem El-Zakzaky da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei tare da fatan nasara ga ƙungiyoyin gwagwarmaya.










Ra'ayinka