Talata 23 Yuni 2026 - 15:02
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (43) | Matsayin Intizar A Al'adun Shi'a (Kashi na Biyu)

Hauza/ A cikin wannan ma'ana, koyarwar addini tana nufin, ban da bayyana falalar "samun sauki na bai-daya" da sanya tsammani da fata ga rayuwa ta gaba da kuma karkatar da mutane zuwa ga wannan fage, hakanan an yi tir da yanke kauna da cire tsammani.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da jerin bahasin Mahdawiya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimin da suka shafi Imamin  Zamaninmu (Allah ya gaggauta bayyanarsa), zuwa gare ku masu daraja.

A cikin bincike takaitacce, riwayoyin da suka yi magana game da Intizar an raba su gida biyu:

Jiran Samun Sauki (Intizarul Faraj) a Ma'anarsa ta Kulli

A cikin wannan ma'ana, koyarwar addini tana kokari ne, baya ga bayyana falalar "sauki na baki-daya" da sanya fatan alheri ga gobe da kuma tura dan adam zuwa ga wannan fage, har ila yau ta yi tir da yanke kauna.

Kula da koyarwar Musulunci wajen bayyana ma'anar jiran Intizar da sanya fata ya kai ga matsayin da aka ambace shi da mafi daukakar lakabi, kuma aka ambaci darajoji masu ban mamaki game da shi. Wasu daga cikin wadannan lakabobi su ne kamar haka:

Ibada da Bauta

Alkur'ani mai girma yana koya mana cewa manufar halitta ita ce bauta wa Allah Madaukakin Sarki.

«وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِیَعْبُدُونِ.»

"Ban halicci aljanu da mutane ba face domin su bauta mini." (Suratuz-Zariyat: Aya ta 56) 

Manzon Allah (SAWA) ya dauki Intizarul Faraj a matsayin daya daga cikin alamun wannan bauta, inda yake cewa:

«اِنتِظارُ الفَرَجِ عِبَادَةٌ.»

"Jiran samun sauki (Intizarul Faraj) ibada ne."(Sheikh Tusi, Al-Amali, Shafi na 405)

Tunda yake mafi yawancin ibadu suna cikin ayyukan dan adam ne, za mu iya fahimtar cewa a nan ma abin da ake nufi da Intizarul Faraj shi ne jerin wasu ayyuka na musamman na dabi'a.

Mafi Girman Ibada

Wasu ibadun suna da fifiko akan wasu; saboda haka yin su, baya ga kasancewa abin jaddadawa a koyarwar addini, yana kuma sanya samun lada mai yawa kuma rawar da yake takawa wajen gina dan adam tana da girma.

Manzon Allah (SAWW) bayan ya lissafta jiran samun sauki a matsayin daya daga cikin ibadu ga Allah, ya bayyana shi a matsayin daya daga cikin mafi girman ibadu, inda yake cewa:

«اَفضَلُ العِبادَةِ اِنتظارُ الفَرَجِ.»

"Mafi falalar ibada ita ce jiran samun sauki (Intizarul Faraj)." (Kamaluddin wa Tamamun-Ni'imah, Juzu'i na 1, Shafi na 287)

Mafi Kyawun Ayyuka

Wani lokaci kuma ana gabatar da shi a matsayin mafi kyawun ayyukan al'ummar Annabin karshe (SAWW).

Manzon Allah (SAWW) yana cewa game da wannan:

«اَفْضَلُ اَعْمالِ اُمَّتِی اِntظارُ الفَرَجِ مِنَ اللَّهِ عَزَّوَجَلَّ.»

"Mafi girman ayyukan al'ummata shi ne jiran samun sauki daga Allah Mai Girma da Daukaka." (Kamaluddin wa Tamamun-Ni'imah, Juzu'i na 2, Shafi na 644)

Kasancewar Jiran Sauki (Intizarul Faraj) Shi Kansa Sauki Ne

A yau, ta fuskar ilimin sanin halayyar dan adam (Psychology), an tabbatar da cewa kasancewa da fata da tsammani yana taka rawar gani sosai a dabi'un al'umma. Ma'ana, jiran kyakkyawar makoma mai haske yana sanya rayuwar yanzu ta dan adam ta kasance mai haske da kuzari.

A cikin wasu riwayoyi da suka shafi jiran Faraj, an yi ishara da wannan gaskiya mai kima, cewa shi kansa jiran samun sauki wani nau'i ne na sauki da yalwa.

A kan wannan, Imam Sajjad (A) ya ce:

«انتظارُ الفَرَجِ مِنْ اَعظَمِ الفَرَجِ.»

"Jiran samun sauki, yana daya daga cikin mafi girman sauki." (Kamaluddin wa Tamamun-Ni'imah, Juzu'i na 1, Shafi na 319)

Jihadi Mafi Girma

A cikin koyarwar addini, jihadi da kokari a tafarkin Allah an gabatar da shi a matsayin daya daga cikin mafi mahimmancin dabi'un mutum a ɗaiɗaiku ko a kungiyance ga musulmi. Ayoyi da dama na Alkur'ani da riwayoyi masu yawa na Ma'asumai (AS) sun yi ishara da gaskiyar wannan dabi'a mai kima.

Game da muhimmancin jiran samun sauki – baya ga abubuwan da aka ambata – mun ci karo da riwayoyin da suka dauki Intizar a matsayin "mafi daukakar jihadi". Daga wannan nau'i na riwayoyi ma za a fahimci cewa Intizar aiki ne na zahiri.

Manzon Allah (SAWW) ya bayyana kasancewar jiran samun sauki mafi daukakar jihadi kamar haka:

«اَفْضَلُ جِهادِ اُمَّتی اِنْتِظارُ الفَرَجِ.»

"Mafi girman jihadi ga al'ummata shi ne jiran samun sauki." (Tuhaful-Uqul, Shafi na 37)

A daya bangaren kuma, yanke kauna da cire tsammani da fata daga rahamar Ubangiji an yi tir da shi sosai kuma yana cikin manyan zunubai. (Suratu Yusuf (12): Aya ta 87)

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An tsakuro ne daga littafin "Darsname  Mahdaviyyat" na Khodamurad Salimiyan, tare da ɗan gyara kadan

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha