A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a cikin bayanan Jagoran Juyin Juya Hali Shahid Hazrat Ayatullah Khamenei (R), an yi bayanin matsayin mace a gurin Alkur'ani mai girma. Yayin da yake nuni da ayoyin Alkur'ani, ya gabatar da ainihin abubuwan koyi na mace a fagen imani da kafirci, kuma ya bayyana bambancin mahangar Musulunci da na wayewar yamma.
"Lokacin da namiji ya kasance shi ne jinsi mafi daukaka a cikin wayewar yamma, kuma wayewar ta kasance mai fifita maza, sakamakonsa shi ne mace za ta yi kokarin mayar da namiji ya zama abin koyi gare ta, sai namiji ya zama abin koyi ga mace; mace kuma sai ta bi sawun ayyukan maza; wannan ne sakamakon."
Ku duba, a nan akwai wata aya ta Alkur'ani da take cewa:
ضَرَبَ اللهُ مَثَلًا لِلَّذینَ کَفَرُوا امرَأَتَ نُوحٍ وَ امرَأَتَ لوط؛
"Allah ya buga misali ga wadanda suka kafirce da matar Nuhu da matar Lud; mata biyu kafirai, sune misali da abin koyi ga mata kafirai: matar Nuhu da matar Lud wadanda suka ci amanar mazajensu; mazajensu duk da cewa Annabawa ne, ba su amfane su da komai ba a gurin Allah." Wannan na kafirai ke nan.
Bayan haka [Yake cewa]:
وَ ضَرَبَ اللهُ مَثَلًا لِلَّذینَ آمَنُوا امرَأَتَ فِرعَون.
Allah ya sanya mata biyu su zama abin koyi ga dukkan mutane kafirai, kuma ya sanya mata biyu su zama abin koyi ga dukkan mutane muminai; ba tare da bambancin namiji ko mace ba.
Wato idan dukkan mazan duniya suna son su kasance muminai, abubuwan koyi gare su mata biyu ne: daya ita ce matar Firauna, daya kuma ita ce Hazrat Maryam.
Matar Firauna ta kasance a kololuwar mutunci da kamun kai; ita ce dai matar da ta yi sanadin cewa lokacin da aka tsamo Annabi Musa daga ruwa, kada a kashe shi; ta ce la taqtuluhu (kada ku kashe shi); daga baya kuma ta yi imani da Hazrat Musa, kuma aka kashe ta a cikin azaba. Wannan ita ce abin koyi.
[Kuma ɗayan abin koyi ita ce] «وَ مَریَمَ ابنَتَ عِمرَان» wanda a game da Hazrat Maryam (S.A) aka ce «الَّتی اَحصَنَت فَرجَهَا» wadda ta tsare mutuncinta da kamun kanta. Abin takaici ba mu da bayanai masu yawa game da yadda lamarin ya kasance; akwai abubuwan da suka faru a kusa da Hazrat Maryam wadanda wannan babbar mace ta yi tsayin daka da dukkan iyawa kuma ta kiyaye tufafinta mai tsarki, har zuwa karshen al'amuran da kuka sani.
Wato dai-dai akasin wayewar yamma wadda take mayar da namiji ya zama abin koyi, a cikin Alkur'ani mace ce aka mayar da ita abin koyi; ba wai kawai ga mata ba, a'a ga dukkan dan adam; ko a fagen kafirci, ko a fagen imani.
Ra'ayinka