Lahadi 8 Nuwamba 2026 - 09:57
Ta Yaya Sayyida Zahra (S.A) Ta Tabbatar Da Wanzuwar Gaskiyar Wilayanci a Cikin Tarihi Ta Hanyar Wasiyyarta Ta a Binne Ta Da Dare?

Hauza/ Marigayi Ayatullahil Uzma Bahjat (R.A) ya bayyana wasiyyar tarihi ta Sayyida Zahra (S.A) na a binne ta da dare a matsayin wani babban shiri mai ban mamaki, wanda ya wuce tunanin ɗan Adam. Wannan mataki ne wanda duk da zaluncin da aka yi mata da kuma shahadarta, ya tabbatar da cewa gaskiyar cancantar Ahlul Baiti (A.S) tana nan daram a cikin tarihi.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, zaluncin da aka yi wa Ahlul Baiti (A.S) ya kasance tare da hikima da shiryarwa ta Ubangiji domin wayar da kan tarihi. Sayyida Siddiqatuɗɗahira (S.A), ta hanyar wasiyyarta ta tarihi, ta tabbatar da cewa gaskiyar cancantar Wilayanci za ta ci gaba da wanzuwa da kuma bayyana har abada. A nan gaba, za mu sake waiwayar wasu zurfafan bayanai da kuma sharhin babban malami kuma masani, Ayatullah Bahjat (R.A), dangane da wannan batu.

Ayatullah Bahjat (R.A) ya ce: “Abin da ya sa Sayyida Zahra (A.S), bayan duk irin zaluncin da aka yi mata, a lokacin da take dab da rasuwa ta yi wasiyyar cewa a binne ta da dare, wani lamari ne mai ban mamaki wanda babu irinsa sai a ayyukan Annabawa (A.S).

Domin aikin mutumin da ya yi saɓani da wasu, aka rinjaye shi, aka kashe shi, ya yi shahada, aka yanke hukunci a kansa, sannan ya fuskanci dukkan waɗannan masifu, amma duk da haka ya gano hanyar da zai sa kansa ya bayyana a matsayin wanda ya yi nasara, kuma ya nuna wa sauran mutane cewa shi ne mai nasara, wannan aiki ya yi kama da ayyukan Annabawa da mu'ujizozinsu.

Wannan wata hanya ce wadda tunanin ɗan Adam ya kasa fahimtarta, ita ce kuwa ta yi wasiyyar a binne ta da dare ba tare da an yi jana'izarta a fili ba.

Da a ce mahukuntan gwamnati da halifanci sun yi tunanin cewa Sayyida Zahra (A.S) za ta aikata irin wannan abu, da sun shiga gidanta domin hana ta aiwatar da hakan.

Bayan an binne ta kuma, babu wata hanyar da za su iya bi face tono kabarinta, amma Amirul Muminin (A.S) ya hana su hakan, don haka ba su iya aikata komai ba.”
 

Madogara: Fi Hadhirati Bahjat, juzu'i na 1, shafi na 131.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha