Laraba 28 Oktoba 2026 - 21:18
Sayyida Fatima Zahra (AS) A Cikin Alƙur’ani: Daga Matsayinta Mai Girma Zuwa Nauyin Da Ke Kan Ɗan Adam

Hauza/ Ayoyin Mubahala, Tsarkakewa (Taɗhir), Ƙaunar Ahlul Baiti (Mawadda) da kuma ayoyin Suratul Insan suna daga cikin ayoyin Alƙur’ani da ke taimakawa wajen fahimtar matsayin Ahlul Baiti (AS) da kyawawan ɗabi’u da halayensu na ruhaniya. Tarihin rayuwar Sayyida Fatima Zahra (AS) abin koyi ne wajen imani, ikhlasi, sadaukarwa da sauke nauyin zamantakewa.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito wani rubutu na Hujjatul Islam Ghulamreza Raza’i Turbaƙan, wanda ya gabatar da shi a yayin kwanakin tunawa da shahadar Sayyida Fatima Zahra (SA).

A cikin rubutunsa mai taken “Sayyida Fatima Zahra (SA) A Cikin Alƙur’ani: Daga Matsayinta Mai Girma Zuwa Nauyin Da Ke Kan Ɗan Adam,” ya yi nazari kan matsayin Sayyida Fatima Zahra (SA) ta fuskar ayoyin Alƙur’ani mai girma, tare da bayyana ma’anoni da darussan da ake samu daga ayoyin Mubahala, Tsarkakewa, Ƙauna da kuma Suratul Insan.

Ya jaddada cewa fahimtar halayen Sayyida Fatima Zahra (SA) ba ta tsaya ga bayyana falalolinta da sake waiwayar abubuwan da suka faru a tarihi kawai ba. A maimakon haka, ɗaya daga cikin manyan darussan tarihinta ga ɗan Adam a yau shi ne alaƙar da ke tsakanin son Ahlul Baiti (AS), kyautata ɗabi’u da kuma sauke nauyin zamantakewa.

Kwanakin tunawa da shahadar Sayyida Fatima Zahra (SA) wata dama ce mai muhimmanci ta sake nazarin rayuwar wannan baiwar Allah da aka san ta a tarihin Musulunci a matsayin abin koyi wajen imani, tsarki, sadaukarwa da kare ƙa’idojin Allah.

Sanin matsayinta bai takaita ga bayyana falalolinta da waiwayar abubuwan da suka faru a tarihi kawai ba. Haka kuma, wata dama ce ta yin tunani a kan koyarwar Alƙur’ani da kyawawan ɗabi’un da suka bayyana a rayuwarta, waɗanda za su iya zama jagora ga rayuwar Musulmi ta kashin kai da kuma ta zamantakewa.

Sayyida Fatima Zahra (SA), ’yar Manzon Allah (S), matar Amirul Muminin Ali (AS), kuma mahaifiyar Imam Hasan (AS) da Imam Husaini (AS), tana da matsayi na musamman a Musulunci.

A tafsirin malaman Shi’a, ana danganta wasu ayoyin Alƙur’ani mai girma da matsayin Sayyida Fatima (SA) da sauran Ahlul Baiti (AS). Daga cikin waɗannan ayoyi akwai Ayar Mubahala, Ayar Taɗhir, Ayar Mawadda da kuma ayoyin Suratul Insan. Kowace daga cikinsu tana taimakawa wajen fahimtar matsayin Ahlul Baiti (AS) da kyawawan ɗabi’unsu na ruhaniya.

Ayar Mubahala: Wata Shaida Ta Matsayin Sayyida Fatima (SA)

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce a cikin aya ta 61 ta Suratu Ali Imran:

«فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَكُمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَكُمْ وَأَنْفُسَنَا وَأَنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَتَ اللَّهِ عَلَی الْکَاذِبِینَ»

Ma’ana: “Ka ce: Ku zo mu kira ’ya’yanmu da ’ya’yanku, matanmu da matanku, mu kanmu da ku kanku, sannan mu roƙi Allah Ya sanya la’anarsa a kan maƙaryata.”

An saukar da wannan aya ne dangane da abin da ya faru na Mubahala tsakanin Manzon Allah (S) da wasu Kiristocin Najran. Mubahala tana nufin roƙon hukuncin Allah da neman Ya la’anci wanda yake ƙarya a cikin wata takaddama ta aƙida. Wannan mataki yana nuna muhimmancin da girman batun da ake saɓani a kansa.

Bisa sanannen rahoton wannan lamari, Manzon Allah (S) ya tafi Mubahala tare da Imam Ali (AS), Sayyida Fatima (SA), Imam Hasan (AS) da Imam Husaini (AS).

Kasancewar Sayyida Fatima (SA) a cikin wannan tawaga, a tafsirin Shi’a, alama ce ta matsayinta na musamman tare da Manzon Allah (SAWA). Ta kasance ɗaya daga cikin mafi kusancin mutanen gidan Annabi da suka halarci wani muhimmin lamari na aƙida a farkon tarihin Musulunci.

Muhimmancin Ayar Mubahala wajen fahimtar matsayin Sayyida Fatima (SA) bai taƙaita ga kasancewarta a wannan lamari na tarihi kawai ba. A maimakon haka, yana nuna cewa fahimtar matsayin Ahlul Baiti (AS) tana buƙatar yin la’akari da Alƙur’ani, hadisai da kuma abubuwan da suka faru a tarihin Musulunci.

Daga wannan mahanga, Sayyida Fatima (SA) ba kawai fitacciyar mace ce a gidan Manzon Allah (SAWA) ba, har ma da mace mai matsayi na musamman a tarihin Musulunci da al’adunsa na addini.

Ayar Tsarkakewa (Taɗhir): Tsarkin Ruhaniya Da Matsayin Ahlul Baiti (AS)

Wata aya mai muhimmanci wajen bayyana matsayin Ahlul Baiti (AS) ita ce aya ta 33 ta Suratul Ahzab, inda Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

«إِنَّمَا یُرِیدُ اللَّهُ لِیُذْهِبَ عَنْکُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَیْتِ وَیُطَهِّرَکُمْ تَطْهِیرًا»

Ma’ana: “Allah Yana nufin Ya kawar da ƙazanta daga gare ku, ya ku Ahlul Baiti, kuma Ya tsarkake ku tsarkakewa ta musamman.”

Bisa hadisai, ana danganta wannan aya da Manzon Allah (SAWA), Imam Ali (AS), Sayyida Fatima (SA), Imam Hasan (AS) da Imam Husaini (AS). Haka kuma, a cikin sanannen Hadisin Kisa, an jaddada matsayin wannan iyali na musamman.

Ayar Taɗhir tana daga cikin muhimman hujjojin Alƙur’ani da malaman Shi’a suke dogaro da su wajen bayanin matsayin Ahlul Baiti (AS). Malamai sun yi tattaunawa mai yawa a fannin tafsiri da aƙida dangane da ma’anar ayar da kuma abin da take nunawa game da tsarki da rashin aikata zunubi na wannan iyali.

Sai dai, yin tunani a kan wannan aya ba ya taƙaita ga batun aƙida kawai. Haka kuma, tana iya ƙarfafa mu wajen yin nazari a kan ma’anar tsarkin ruhaniya da yadda yake shafar rayuwar ɗan Adam.

A koyarwar addini, tsarki da taƙawa ba kalmomi ba ne da ake amfani da su wajen yabo kawai. Suna da alaƙa da halayen mutum, niyyarsa, ɗaukar nauyi da kuma yadda yake mu’amala da gaskiya.

Ƙaunar Sayyida Fatima (SA) za ta ƙara samun zurfi a rayuwarmu idan ta kasance tare da ƙoƙarin gyara halaye, kiyaye haƙƙin wasu, faɗin gaskiya da kuma riƙo da ƙa’idojin Allah.

Saboda haka, sanin matsayin wannan baiwar Allah ya kamata ya haɗu da fahimtar darussan tarbiyya da kyawawan ɗabi’un da rayuwarta ta ƙunsa.

Ayar Ƙauna (Mawadda): Son Ahlul Baiti (AS) Ya Fi Jin Ƙauna A Zuciya Kawai

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce a cikin aya ta 23 ta Suratus Shura:

«قُلْ لَا أَسْأَلُکُمْ عَلَیْهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِی الْقُرْبَی»

Ma’ana: “Ka ce: Ba na neman wani sakamako daga gare ku a kan wannan saƙo, sai dai ƙauna ga makusanta na.”

Akwai ra’ayoyin tafsiri daban-daban dangane da waɗanda ake nufi da kalmar Al-Qurba a cikin ayar. A tafsirin Shi’a, bisa dogaro da hadisai, ana danganta ayar da ƙauna da soyayya ga Ahlul Baitin Manzon Allah (S), kuma Sayyida Fatima Zahra (SA) tana daga cikin fitattun mutanen wannan gida.

Muhimmin abin lura a cikin wannan aya shi ne ma’anar ƙauna ta gaskiya. Idan ƙauna ta haɗu da sani da fahimta, tana iya yin tasiri a kan halayen mutum.

Saboda haka, girmama Ahlul Baiti (AS) bai kamata ya tsaya ga bayyana ƙauna da baki kawai ba. Ya kamata wannan ƙauna ta zama hanyar kusantar kyawawan ɗabi’u da halayen da suka yi fice a rayuwarsu.

Idan muna magana a kan ƙauna da biyayya ga Sayyida Fatima (SA), ya kamata mu yi la’akari da irin tasirin wannan ƙauna a kan mu’amalarmu da iyalai, maƙwabta, mabuƙata da sauran al’umma.

Shin ƙaunarmu gare ta tana sa mu ƙara yin adalci, faɗin gaskiya, kiyaye haƙƙin mutane da kuma kula da waɗanda suke cikin buƙata?

Tabbas, bai kamata a yi wa mutane hukunci game da imaninsu bisa wasu ƙalilan daga cikin halayensu kawai ba. Abin da ake nufi shi ne, ƙaunar addini tana da babban tasiri wajen tarbiyyantar da ɗan Adam da kyautata ɗabi’unsa.

Daga wannan mahanga, Ayar Ƙauna tana tunatar da mu cewa alaƙa da Ahlul Baiti (AS), ban da matsayinta na aƙida, tana ɗora wa masu ƙaunarsu wani nauyi na kyautata ɗabi’u.

Suratul Insan: Bayyanar Sadaukarwa Da Ikhlasi A Rayuwar Sayyida Fatima (SA)

Ɗaya daga cikin fitattun kyawawan ɗabi’un Ahlul Baiti (AS) shi ne kula da mabuƙata da fifita yardar Allah a kan son zuciya.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce a cikin ayoyi na 7 zuwa na 9 na Suratul Insan:

«وَیُطْعِمُونَ الطَّعَامَ عَلَیٰ حُبِّهِ مِسْکِینًا وَیَتِیمًا وَأَسِیرًا ۞ إِنَّمَا نُطْعِمُکُمْ لِوَجْهِ اللَّهِ لَا نُرِیدُ مِنْکُمْ جَزَاءً وَلَا شُکُورًا»

Ma’ana: “Kuma suna ciyar da abinci, duk da suna son sa, ga miskini da maraya da fursuna (bawa). Suna cewa: Muna ciyar da ku ne domin neman yardar Allah kawai; ba ma neman wani sakamako ko godiya daga gare ku.”

A cikin wasu littattafan tafsirin Shi’a, ana danganta waɗannan ayoyi da labarin bakancen azumi da Imam Ali (AS), Sayyida Fatima (SA) da iyalinsu suka yi, da kuma ciyar da masu buƙata.

Bisa sanannen riwayar da ake bayarwa, bayan Imam Hasan (AS) da Imam Husaini (AS) sun yi rashin lafiya, iyayensu suka yi bakancen cewa idan sun warke za su yi azumi. A ci gaban wannan labari, a lokacin buɗa baki, iyalin sun ba miskini, maraya da fursuna (bawa) abincinsu, duk da cewa su ma suna buƙatarsa, suka fifita wasu a kansu.

A al’adar Shi’a, wannan labari yana zama misali na sadaukarwa da ikhlasin Ahlul Baiti (AS). Sai dai, akwai rahotannin tafsiri daban-daban dangane da cikakkun bayanai game da dalilin saukar waɗannan ayoyi. Saboda haka, ya dace a bambanta tsakanin abin da ayoyin Alƙur’ani suka faɗa kai tsaye da kuma bayanan riwayoyin da aka bayar dangane da dalilin saukarsu.

Darasin akhlaƙ da waɗannan ayoyi suke koyarwa a bayyane yake: darajar bayarwa ba ta dogara da yawan abin da mutum ya bayar kawai ba. Niyya, ikhlasi da kuma irin sadaukarwar da ya yi su ma suna da muhimmanci.

Ciyar da mabuƙata idan aka yi ta ba tare da neman wani sakamako ba, domin neman yardar Allah, tana wuce matakin wani aiki na yau da kullum, ta zama wata alama ta bautar Allah da ɗaukar nauyin al’umma.

Tarihin rayuwar Sayyida Fatima (SA), kamar yadda aka bayyana a cikin waɗannan riwayoyi, yana tunatar da mu cewa kula da mabuƙata bai kamata ya tsaya ga jin tausayinsu kawai ba.

Mutum mai buƙata yana da mutunci da daraja, kuma taimaka masa yana daga cikin nauyin ɗabi’a da zamantakewa da ke kan al’umma.

A yau ma, bin wannan kyakkyawan misali yana iya bayyana ta hanyar taimaka wa iyalai mabukata, tallafa wa yaran da ba su da isassun abubuwan rayuwa, taimakon mutanen da suka shiga matsala da kuma shiga ayyukan rage wahalhalun ɗan Adam.

Al’ummar da take magana a kan sadaukarwar Sayyida Fatima (SA), ya dace ta nuna hakan a aikace, ta hanyar kin rashin yin ko-oho da wahala da talaucin sauran mutane.

Sayyida Fatima (SA): Abin Koyi Ga Rayuwar Yau

Sake nazarin waɗannan ayoyi yana nuna cewa fahimtar matsayin Sayyida Fatima (SA) ba ta taƙaita ga bayyana falalolinta da matsayinta a tarihi kawai ba.

A tafsirin Shi’a, Ayar Mubahala tana nuna matsayinta na musamman tare da Manzon Allah (S). Ayar Tsarkakewa tana da alaƙa da matsayin ruhaniya na Ahlul Baiti (AS). Ayar Ƙauna tana jaddada muhimmancin ƙaunar iyalan Annabi (S), yayin da ayoyin Suratul Insan suke bayyana sadaukarwa, ciyar da mabukata da ikhlasi, waɗanda aka danganta da tarihin rayuwar Ahlul Baiti (AS) a wasu littattafan tafsiri.

Baya ga muhimmancinsu a fannin aƙida da tafsiri, waɗannan ayoyi suna ba mu damar sake nazarin halayenmu na kashin kai da na zamantakewa.

Ƙaunar Sayyida Fatima (SA) za ta fi samun tasirin tarbiyya idan ta bayyana a cikin faɗin gaskiya, neman adalci, cika alƙawura da nauyin da ke kanmu, da kuma kula da masu buƙata.

Girmama wannan baiwar Allah dama ce ta tunani a kan nauyin da ke kanmu ga al’umma, baya ga gudanar da bukukuwa da bayyana falalolinta.

Shin muna kiyaye haƙƙin wasu a cikin mu’amalarmu ta yau da kullum? Shin muna jin nauyin taimaka wa mabuƙata? Shin muna ƙoƙarin tabbatar da kyawawan ɗabi’u irin su ikhlasi, adalci da riƙo da gaskiya a rayuwarmu?

Babu shakka, amsa waɗannan tambayoyi ta hanyar ayyuka za ta taimaka wajen raya tunawa da Sayyida Fatima (SA) a cikin rayuwarmu.

Abubuwan koyarwa na addini suna samun tasiri mai ɗorewa a cikin al’umma ne idan suka wuce matakin magana da motsin zuciya, suka bayyana a cikin halaye da zaɓin da mutum yake yi a rayuwarsa.

Kwanakin tunawa da shahadar Sayyida Fatima Zahra (SA) wata dama ce ta sabunta alƙawarinmu da wannan baiwar Allah, wadda tunawa da ita ga masu ƙaunar Ahlul Baiti (AS) take zama alamar ƙauna da girmamawa, tare da kira zuwa ga imani, ikhlasi, sadaukarwa da ɗaukar nauyi a gaban Allah da bayinsa.

Marubuci: Ghulamreza Raza’i Turbaƙan 

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha