Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa a cikin Alƙur’ani Mai Girma:
«مَنْ جَاءَ بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ عَشْرُ أَمْثَالِهَا وَمَنْ جَاءَ بِالسَّيِّئَةِ فَلَا يُجْزَى إِلَّا مِثْلَهَا وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ»
“Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, yana da lada ninki goma na shi. Wanda kuma ya zo da mummunan aiki, ba za a saka masa ba face da misalinsa, kuma ba za a zalunce su ba.” (Suratul An’am: 160)
Bayani
A rayuwar duniya, ana iya gane mutum ta hanyar abokansa da waɗanda yake zama da su. Har ma a cikin ruwayoyi da dama, an bayyana cewa abokan zama suna daga cikin ma’aunan da ake amfani da su wajen tantance halin mutum da ƙimarsa.
A cikin wani hadisi, Annabi Sulaiman (AS) ya ce:
«لاَ تَحْكُمُوا عَلَى رَجُلٍ بِشَيْءٍ حَتَّى تَنْظُرُوا إِلَى مَنْ يُصَاحِبُ فَإِنَّمَا يُعْرَفُ الرَّجُلُ بِأَشْكَالِهِ وَأَقْرَانِهِ وَيُنْسَبُ إِلَى أَصْحَابِهِ وَأَخْدَانِهِ»
“Kada ku yanke hukunci a kan wani mutum har sai kun duba waɗanda yake abota da su. Domin ana gane mutum ta hanyar waɗanda suke kama da shi, abokan zamansa da abokansa.” (Biharul Anwar, juzu’i na 71, shafi na 188)
Haka nan a Lahira, abin da mutum ya zo da shi na ayyuka shi ne zai zama ma’aunin tantance shi. Za a yi masa hukunci bisa ga abin da ya aikata kuma ya zo da shi. Kamar yadda Allah Maɗaukakin Sarki ya faɗa.
Saboda haka, Imam Ali (AS), ta hanyar wani kyakkyawan misali, ya ce:
«لاَ يُعْرَفُ الرَّجُلُ إِلَّا بِعَمَلِهِ كَمَا لاَ يُعْرَفُ الْغَرِيبُ مِنَ الشَّجَرِ إِلَّا عِنْدَ حُضُورِ الثَّمَرِ»
“Ba a san mutum da hakika ba sai ta hanyar ayyukansa, kamar yadda ba a iya gane irin bishiya sai lokacin da ta ba da ’ya’yanta.” (Gurarul Hikam, juzu’i na 1, shafi na 700)
Wani muhimmin abin lura shi ne, mutum na iya rabuwa da abokinsa ko wanda yake zama da shi a duniya, amma a Lahira ba haka lamarin yake ba. Kamar yadda Imam Ali (AS) ya ce:
«أَعْمَالُ الْعِبَادِ فِي الدُّنْيَا نُصْبُ أَعْيُنِهِمْ فِي الْآخِرَةِ»
“Ayyukan bayin Allah da suka aikata a duniya za su kasance a gaban idanunsu a Lahira.” (Gurarul Hikam, juzu’i na 1, shafi na 103)
Saboda haka, tun daga yanzu ya kamata mutum ya yi tunanin abokin tafiyarsa a Lahira. Wannan abokin shi ne zai zama kamar madubi da ke bayyana hakikanin ayyukansa, kuma zai kasance tare da shi a dukkan mawuyatan matakai na Ranar Alƙiyama.
A saboda haka ne Amirul Muminin Ali (AS) ya yi mana gargaɗi da cewa:
«عِبَادَ اللَّهِ، الْآنَ فَاعْلَمُوا [فَاعْمَلُوا]، وَالْأَلْسُنُ مُطْلَقَةٌ وَالْأَبْدَانُ صَحِيحَةٌ وَالْأَعْضَاءُ لَدْنَةٌ وَالْمُنْقَلَبُ فَسِيحٌ وَالْمَجَالُ عَرِيضٌ، قَبْلَ إِرْهَاقِ الْفَوْتِ وَحُلُولِ الْمَوْتِ»
“Ya bayin Allah! Ku yi hankali tun yanzu, kuma ku aikata ayyukan alheri, alhali harsunanku suna da ’yancin magana, jikinku yana cikin ƙoshin lafiya, gaɓoɓinku suna da ƙarfi da shirin aiki, filin aiki yana da faɗi, kuma dama tana nan. Ku yi haka kafin lokaci ya kuɓuce muku, kuma mutuwa ta zo.” (Nahjul Balaga, Huɗuba ta 196)
An shirya wannan rubutu ne a Sashen Ilimi da Al’adu na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza.
Ra'ayinka