Talata 27 Oktoba 2026 - 20:29
Miƙa Wuya Ga Amurka Fita Ne Daga Da’irar Imani da Tauye ’Yancin Kai

Hauza/ Ayatullah Muhsin Araki, a cikin saƙon da ya aika wa shugabannin siyasar Iraƙi, ya jaddada cewa miƙa wuya ga manufofin Amurka yana nufin fita daga da’irar imani da kuma tauye ’yancin kai. Ya bayyana cewa babu shakka, miƙa wuya ga manufofin Amurka da yi mata biyayya yana daga cikin bijirewa Allah da kuma jingina kai ga azzalumi.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Muhsin Araki, mamba a Majalisar Ƙoli ta Makarantun Hauza kuma mamba a shugabancin Majalisar Kwararru ta Jagoranci, ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya aika wa shugabannin siyasar Iraƙi.

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai

Zuwa ga shugabannin siyasar Iraƙi, Allah Maɗaukakin Sarki Ya shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.

Ƙasar Iraƙi mai daraja da kuma dukkan yankin Gabas ta Tsakiya suna fuskantar wani muhimmin lokaci mai haɗari a tarihin yankin. A wannan lokaci, babu damar yin sakaci, yin biris da al’amura, sassauci marar gurbi ko kuma yin ko-oho, domin wannan lokaci ne da zai tsara makomar Iraƙi da dukkan yankin.

Akwai wasu ƙa’idoji bayyanannu na Shari’a da hankali waɗanda bai halatta a yi watsi da su ko a ƙetare iyakokinsu ba. Ga wasu daga cikinsu:

Ƙa’idojin Shari’a

Ƙa’ida ta farko: Haramcin zalunci da jingina kai ga azzalumai

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

وَلَا تَطْغَوْا إِنَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ ۝ وَلَا تَرْكَنُوا إِلَى الَّذِينَ ظَلَمُوا فَتَمَسَّكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ مِنْ أَوْلِيَاءَ ثُمَّ لَا تُنْصَرُونَ

“Kada ku ƙetare iyaka, domin lallai Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatawa. Kuma kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zalunci, har wuta ta shafe ku. Ba ku da wasu majibinta da za su taimake ku baicin Allah, sannan ba za a taimake ku ba.” (Suratul Hud: 112–113).

Babu shakka, miƙa wuya ga manufofin Amurka da yi mata biyayya yana daga cikin bijirewa Allah da jingina kai ga azzalumi. Sakamakon hakan ba zai wuce faɗawa cikin wutar Jahannama, rasa taimakon Allah da kuma shiga cikin halin baƙin ciki a duniya kafin azabar Lahira ba.

Ƙa’ida ta biyu: Haramcin bai wa kafirai damar mamaye muminai

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

وَلَنْ يَجْعَلَ اللَّهُ لِلْكَافِرِينَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ سَبِيلًا

Ma’ana: “Kuma Allah ba zai sanya wa kafirai wata hanya ta samun rinjaye a kan muminai ba.” (Suratun Nisa’i: 141).

Wannan wulaƙantaccen miƙa wuya da muke gani a yau daga wasu ’yan siyasar Iraƙi yana daga cikin manyan misalan buɗe ƙofa domin kafirai su samu iko a kan muminai. Wannan yana nufin cewa amincewa da wannan mamaya da miƙa wuya gare ta, babu shakka, fita ne daga da’irar imani.

Ƙa’ida ta uku: Haramcin ɗaukar maƙiya a matsayin majiɓinta

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَىٰ أَوْلِيَاءَ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ وَمَنْ يَتَوَلَّهُمْ مِنْكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ ۝ فَتَرَى الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ مَرَضٌ يُسَارِعُونَ فِيهِمْ يَقُولُونَ نَخْشَىٰ أَنْ تُصِيبَنَا دَائِرَةٌ فَعَسَى اللَّهُ أَنْ يَأْتِيَ بِالْفَتْحِ أَوْ أَمْرٍ مِنْ عِنْدِهِ فَيُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا أَسَرُّوا فِي أَنْفُسِهِمْ نَادِمِينَ

Ma’ana: “Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi Yahudawa da Nasara a matsayin majiɓinta. Su dai majiɓintan juna ne. Kuma wanda ya riƙe su a cikinku, to, lallai shi yana daga cikinsu. Haƙiƙa, Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai. Saboda haka, za ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta suna gaggawar shiga cikinsu, suna cewa: ‘Muna tsoron kada wata musiba ta same mu.’ To, akwai fatan Allah Ya kawo nasara ko wani al’amari daga gare Shi, sai su wayi gari suna nadamar abin da suka ɓoye a cikin zukatansu.” (Suratul Ma’ida: 51–52).

Waɗannan ƙa’idoji ne bayyanannu na Shari’a waɗanda suke bambance tsakanin zaɓi biyu: zaɓin imani da tsayawa tare da masu gaskiya, da kuma zaɓin kafirci da munafunci, wanda yake nufin tsayawa tare da kafirai da masu girman kai.

A yau, ku shugabannin siyasar Iraƙi kuna a kan mararrabar waɗannan zaɓuɓɓuka biyu, kuma babu wani zaɓi na uku da za a iya tunani a kansa.

Ƙa’idojin Hankali

Akwai kuma wasu ƙa’idoji bayyanannu na hankali waɗanda suke da muhimmanci. Ga wasu daga cikinsu:

Ƙa’ida ta farko: ’Yantar da kai daga mamayar azzalumi ya fi miƙa wuya gare shi

’Yantar da kai daga mamayar azzalumi mai girman kai ya fi miƙa wuya da ƙasƙantar da kai a gabansa, kuma farashin da ake biya wajen samun ’yanci sun fi sauƙi sosai idan aka kwatanta da sakamakon miƙa wuya.

Akwai misalai da dama daga tarihi waɗanda suke tabbatar da wannan magana. Mafi bayyana daga cikinsu shi ne abin da ya faru da Hukumar Mulkin Kai ta Falasɗinu, wanda kuke gani da idanunku. Haka kuma, tarihin gwamnatin Saddam ba ya da nisa da ku.

Ƙa’ida ta biyu: Biyayya ga maƙiyi tana ƙara masa zalunci

Biyayya ga maƙiyi ba ta haifar da komai sai ƙara masa ƙarfin zalunci da wuce gona da iri.

Babban kuskure ne mutum ya yi tunanin cewa sassautawa ga maƙiyi zai kawar da sharrinsa. A’a, kamar yadda ɗaruruwan abubuwan da suka faru a tarihin ɗan Adam, na baya da na yanzu, suka tabbatar, irin wannan hali yana ƙara wa maƙiyi ƙarfin gwiwa da tsananin zalunci ne kawai.

Ƙa’ida ta uku: ’Yancin yanke shawara shi ne maslahar kowace al’umma

Maslahar kowace al’umma tana cikin kasancewarta ita ce take yanke shawara kan manufofinta, tafiyar da ƙasarta, tattalin arzikinta, al’adunta da kuma dangantakar siyasarta da sauran al’umma.

Amma matsayar da muke gani daga wasu ’yan siyasar Iraƙi tana bayyana babban kuskure a fahimtarsu game da maslahar al’ummar Iraƙi. Mun ji wasu daga cikinsu suna iƙirarin cewa maslahar Iraƙi tana cikin miƙa wuya ga shawarwarin Amurka!

Shin yana cikin maslahar al’ummar Iraƙi ta yadda ba za ta sami ’yancin yanke shawara ko da wajen zaɓen firaminista, ministoci da manyan jami’an gudanarwarta ba?

Shin yana cikin maslahar al’ummar Iraƙi cewa kuɗaɗen shigar da take samu daga man fetur su riƙa kwarara zuwa Amurka, alhali ita ba ta da ’yancin yanke shawara kan arzikinta da tattalin arzikinta?

Shin yana cikin maslahar wannan al’umma ta rasa ’yancin tsara dangantakarta da ƙasashen maƙwabta, har a riƙa tilasta mata yanke hulɗa da su, alhali tana da manyan muradu na bai ɗaya da waɗannan ƙasashe?

Musamman ma ƙasar maƙwabciyar da ta tsaya tare da Iraƙi da kyakkyawar niyya a lokacin da wannan ƙasa take fuskantar babban rikici, wato a lokacin da ’yan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na Takfiri, waɗanda maƙiyiya Amurka take tallafawa, suka kai mata hari.

To, ta yaya wasu ’yan siyasar Iraƙi za su yi tunanin cewa miƙa wuya ga maƙiyi Amurka da kuma ƙiyayya ga maƙwabciyarsu mafi taimako da gaskiya zai dace da hankali da maslahar ƙasa?

Wane irin hankali ne zai sa a sadaukar da ’yancin siyasa, gudanarwa da tattalin arzikin al’ummar Iraƙi domin neman yardar maƙiyanta, har a sadaukar da abokai da masu taimaka wa al’ummar Iraƙi, waɗanda suka tsaya mata a lokutan wahala da kaɗaici?

Shin Amurka ba ita ce babbar maƙiyiyar al’ummar Iraƙi ba, wadda ta rusa wannan ƙasa, ta kuma zubar da jinin dubban matasa, maza, mata da yara?

Shin ba Amurka ce wadda, bisa ikirarin shugaban ƙasarta na yanzu, ta samar wa ƙungiyar ISIS makamai kuma ta kafa ta ba? Ita ce ƙungiyar da ta yanka ’ya’yan Iraƙi, ta mayar da yara marayu, ta kori mata daga gidajensu, ta halatta zubar da jinin al’ummar Iraƙi da ƙwace dukiyoyinsu, tare da mamaye ikon ƙasa, sararin samaniya, teku da ƙasa busasshiya ta wannan ƙasa?

Ya ku ’yan siyasar Iraƙi! Ku sani cewa al’ummar Iraƙi al’umma ce mai mutunci da ɗaukaka, wadda ba za ta taɓa amincewa da wulaƙanci da ƙasƙanci ba, kuma ba za ta taɓa barin imaninta da addininta ba.

Shin ba ita ce al’ummar da ta amsa kiran babban Marja’inta na addini ba, ta tashi da miliyoyin jama’a domin taimakon addini da ceton ƙasarta, har ta ba maƙiyanta mamaki da ruɗani ba?

Shin ba ita ce al’ummar (Imam) Husaini da Ali ba, wadda ta bi tafarkin Sayyidush Shuhada (A.S.), ta kuma gudanar da gagarumin taron Arba’in na Imam Husaini, taron da ya zama mafi girma a duniya wajen nuna goyon baya ga waɗanda ake zalunta da tsayawa tsayin daka a gaban azzalumai masu girman kai?

Shin ba ita ce wannan babbar al’umma da ta shafe ƙarni goma sha huɗu tana tsayawa kan Wilayar Amirul Muminin Ali (A.S.) ba, duk da irin sadaukarwar rayuka, shahidai da asarar dukiyoyin da ta yi a wannan tafarki, ba tare da ta daina yaƙi da zalunci da wuce gona da iri ba?

Ya ku ’yan siyasar Iraƙi! Ku sani cewa nan ba da daɗewa ba, al’ummar Iraƙi za ta tashi tsaye domin fuskantar zaluncin Amurka, ta kuma murƙushe shi. Wannan al’umma za ta ƙi waɗanda suka amince da wulaƙanci da ƙasƙantar da ita a lokacin da Amurka take iko da makomar wannan al’umma da aka zalunta.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

وَلَيَنْصُرَنَّ اللَّهُ مَنْ يَنْصُرُهُ إِنَّ اللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ

Ma’ana: “Kuma lallai Allah zai taimaki wanda yake taimakon addininsa. Haƙiƙa, Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwayi.” (Suratul Hajj: 40).

Haka nan, Amirul Muminin Ali (A.S.) ya ce:

وَاللَّهِ إِنَّ امْرَأً يُمَكِّنُ عَدُوَّهُ مِنْ نَفْسِهِ يَعْرُقُ لَحْمَهُ، وَيَهْشِمُ عَظْمَهُ، وَيَفْرِي جِلْدَهُ لَعَظِيمٌ عَجْزُهُ، ضَعِيفٌ مَا ضُمَّتْ عَلَيْهِ جَوَانِحُ صَدْرِهِ. أَنْتَ فَكُنْ ذَاكَ إِنْ شِئْتَ، فَأَمَّا أَنَا فَوَاللَّهِ دُونَ أَنْ أُعْطِيَ ذَلِكَ ضَرْبٌ بِالْمَشْرَفِيَّةِ تَطِيرُ مِنْهُ فَرَاشُ الْهَامِ، وَتَطِيحُ السَّوَاعِدُ وَالْأَقْدَامُ.

Ma’ana: “Na rantse da Allah, mutumin da ya bai wa maƙiyinsa damar iko da kansa har maƙiyin ya cinye namansa, ya farfasa ƙasusuwansa, ya kuma yaga fatarsa, to, lallai gazawarsa babba ce, zuciyar da ke cikin ƙirjinsa kuma mai rauni ce ƙwarai. Kai, idan kana so, ka zama haka. Amma ni, na rantse da Allah, kafin in ba maƙiyina irin wannan dama, sai na kai masa sara da takobin Mashrafiyya, har ƙasusuwan kai su tashi sama, hannaye da ƙafafu su yanke su faɗi.” (Nahjul Balagha, Huɗuba ta 34).

Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ayatullah Muhsin Araki 

14 ga Jimada al-Ula, 1448H

Daidai da 3 ga Aban, 1405 Shamsiyya / 26 ga Oktoba, 2026 Miladiyya

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha