A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a ranar Juma'a, 30 ga Oktoba, 2026, an gudanar da taron tunawa da shahadar Sayyida Fatima Zahra (SA) a birnin Qum na ƙasar Iran, wanda Harisawan Harkar Musulunci a Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), na Iran suka shirya.
An gudanar da taron ne a unguwar ɗalibai ta Shahrak Mahdiye, tare da halartar wasu daga cikin almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) da ke karatu a ƙasar Iran.
A cikin jawabinsa a matsayin babban bako, Hujjatul Islam wal Muslimin Sulaimani ya jaddada cewa addinin Musulunci ba addinin ƙabila ko wata al'umma ta musamman ba ne, a'a addini ne da ya ginu bisa imani da aiki, ba bisa nasaba ko dangantakar jini ba.
Ya yi misali da Salmanul Farisi, inda ya bayyana cewa duk da kasancewarsa ɗan ƙasar Iran, amma saboda imaninsa da kyawawan ayyukansa ya kai wani matsayi mai girma, har Manzon Allah (SAWA) ya bayyana cewa: "Salman yana daga cikinmu, Ahlul Baiti".
Nau'o'in mutanen da Sayyida Zahra (SA) ta fuskanta bayan rasuwar Manzon Allah (SAWA)
Da yake magana kan abubuwan da suka faru bayan wafatin Manzon Allah (SAWA) da kuma batun Saƙifa, Hujjatul Islam wal Muslimin Sulaimani ya bayyana cewa akwai nau'o'in mutane guda uku waɗanda Sayyida Zahra (SA) ta fuskanta a wancan lokaci.
Ya ce: "Nau'i na farko su ne mutanen da suka shiga addinin Musulunci da wasu ɓoyayyun manufofi na raunana shi. Nau'i na biyu kuwa su ne waɗanda suka karɓi Musulunci saboda ƙaunar Manzon Allah (SAWA), amma imani bai riga ya kafu sosai a cikin zukatansu ba. Saboda haka, kwanaki kaɗan bayan rasuwar Manzon Allah (SAWA), sun kasa taimaka wa tsokar jikinsa, tare da karya alkawarin da suka ɗauka a Gadir Khum. Nau'i na uku kuma su ne waɗanda suka karɓi Musulunci domin samun matsayi da moriyar duniya."
Malamin ya ƙara da cewa waɗannan nau'o'in mutane suna wanzuwa a kowane zamani, inda ya ce: "Ko a ƙasar Iran akwai mutanen da suka bi Imam Khumaini (RA), amma bayan wafatinsa sai suka koma suna adawa da Imam Shahid."
Ya jaddada muhimmancin fahimtar haƙiƙanin Wilaya da kuma tsayawa daram a kanta, yana mai cewa wajibi ne mutum ya fahimci matsayin Wilaya yadda ya kamata tare da kasancewa mai tsayin daka a tafarkinta.
Hanyoyi uku da Sayyida Zahra (SA) ta bi wajen kare Wilaya
A wani ɓangare na jawabinsa, Hujjatul Islam Sulaimani ya yi bayani kan hanyoyi uku da Sayyida Fatima Zahra (SA) ta yi amfani da su wajen gwagwarmayarta ta kare Wilaya.
Ya bayyana cewa hanya ta farko ita ce yin bayani da wa'azi domin bayyana gaskiya. Ya ce Sayyida Zahra (SA) ta kasance tana zuwa gidajen mutanen Madina ɗaya bayan ɗaya, tana kiransu zuwa ga taimakon Wilaya.
A wannan ɓangaren, ya yi ishara da aya ta 46 a cikin Suratul Saba'i, inda Allah Maɗaukakin Sarki yake cewa:
«قُلْ إِنَّمَا أَعِظُكُمْ بِوَاحِدَةٍ أَنْ تَقُومُوا لِلَّهِ مَثْنَى وَفُرَادَى ثُمَّ تَتَفَكَّرُوا مَا بِصَاحِبِكُمْ مِنْ جِنَّةٍ إِنْ هُوَ إِلَّا نَذِيرٌ لَكُمْ بَيْنَ يَدَيْ عَذَابٍ شَدِيدٍ».
Malamin ya bayyana cewa Sayyida Zahra (SA) ba ta zauna tana cewa mace ce ko kuma ba ta da mataimaka ba, ta miƙe ta gudanar da nauyin da ke kanta cikin sani da fahimta, a lokacin da ya dace.
Ya ce hanya ta biyu ita ce bayyana rashin yardarta a fili ga khalifa. Ya bayyana cewa yardar Sayyida Zahra (SA) tana da alaƙa da yardar Allah Maɗaukakin Sarki, kamar yadda Manzon Allah (SAWA) ya bayyana a cikin hadisinsa game da matsayinta.
Hanya ta uku kuwa ita ce bayyana rashin halaccin khalifancin da aka kafa bayan Saƙifa ta fuskar shari'a, tare da nuna cewa wannan khalifanci ba shi da ingantacciyar madogara ta halaccin Allah.
A ƙarshen taron, Hujjatul Islam Ibrahim Tudunwada ya gabatar da taƙaitaccen bayani, sannan mawaka suka gabatar da waƙoƙin juyayi domin tunawa da shahadar Sayyida Fatima Zahra (SA).
Daga bisani, wakilin Harisawan Harkar Musulunci a Iran, Malam Salisu Aƙil, ya gabatar da jawabin godiya ga mahalarta taron. A ƙarshe kuma, Malam Bature ya rufe taron da addu'a.







Ra'ayinka