Fushi yana daga cikin halittar mutum wadda idan ya zama ya kasa kula da ita ta kan kai shi ga matsaloli masu yawa. Kamfanin Dillancin Labaran Hauzah ya wallafa ruwayar da ke ƙasa daga Imam Sadiƙ (AS) a cikin wata ruwaya da take nuni kan illar rashin iya sarrafa fushi a cikin littafin "Usulul Kafi".
Imam Sadiƙ (AS) Yace:
مَن لَم یَملِکْ غَضَبَهُ لَم یَملِکْ عَقلَهُ
"Duk wanda bai iya mallakar fushinsa ba, ba zai iya mallakar hankalinsa ba".
Al-Kafi: Juzu’i na 2, shafi na 305, hadisi na 13.
Ra'ayinka