A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, cikin wani babban bayani da ya fitar, Nwaeze ya bayyana cewa tafiyarsa ta canza rayuwarsa baki ɗaya, inda ya bayyana yadda ya fita daga tsarin addinin Kiristanci zuwa Musulunci, sannan daga rudun jita-jita zuwa yakinin gaskiya.
Nwaeze, wanda ya taso a cikin babban gidan Kiristoci na al'ummar Igbo, ya bayyana cewa tun yana ƙarami, ya kasance yana jin kalamai marasa inganci game da Musulunci, inda aka koya masa cewa Musulunci addini ne na tashin hankali da ta'addanci. Ya ƙara da cewa waɗannan ra'ayoyi sun yi ƙarfi a cikin al'ummarsa ba tare da an taba yin bincike na gaskiya ba.
Ya bayyana cewa, sha'awar neman gaskiya ta sa ya fara yin tambayoyi masu zurfi game da manufar rayuwa da kuma tafarkin gaskiya zuwa ga Allah. Wannan bincike ya kai shi ga karanta littattafan addinai daban-daban, wanda hakan ya sa hankalinsa ya karkata zuwa ga Musulunci bayan ya gano cewa Musulunci addini ne na adalci, rahama, da bautar Allah Shi kaɗai.
Nwaeze ya yi bayanin cewa, bayan ya musulunta, ya fara koyon addini daga malamai daban-daban, inda ya amfana da karatun malamai na Ahlus-Sunnah. Sai dai, ya bayyana cewa ya fuskanci gargadi da jita-jita da yawa game da mazhabar Shi'a, inda aka ce masa cewa Shi'a ba Musulmai ba ne, kuma suna bautar mutane maimakon Allah.
A maimakon ya amince da waɗannan zarge-zarge, Nwaeze ya yanke shawarar gudanar da bincike na kashin kansa. Ya shafe sama da shekaru biyu yana nazarin koyarwar Shi'a, yana karanta littattafansu, da kuma kwatanta hujjojin malaman Ahlus-Sunnah da na Shi'a.
Babban mataki a tafiyarsa ya kasance ziyarar da ya yi zuwa birnin Zariya, inda ya haɗu da mambobin Harkar Musulunci da kuma jagoran Harkar, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H). Nwaeze ya bayyana cewa, binciken da ya yi a can ya nuna masa cewa yawancin zarge-zargen da yake ji ba gaskiya ba ne. Ya tabbatar da cewa Shi'a suna bautar Allah Shi kaɗai, suna girmama Manzon Allah (S.A.W.A) da Ahlul Baitinsa, kuma suna yin rukunnan Musulunci kamar sallah, azumi, zakka, da Hajji.
A ƙarshe, Nwaeze ya bayyana cewa ya zaɓi mazhabar Shi'a ne bisa yakini da gamsuwa bayan ya ga gaskiyar koyarwarsu da idonsa. Ya ƙara da cewa, ba ya yi wannan bayani don haifar da rarraba kai tsakanin Musulmai ba ne, sai dai don ƙarfafa mutane su nemi ilimi da gaskiya maimakon dogaro da jita-jita.
Nwaeze, wanda yake wakiltar al'ummar Igbo a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya kammala da roƙon Allah da Ya shiryar da dukkan masu neman gaskiya zuwa ga tafarkin adalci da fahimta.
Ra'ayinka