Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya bayyana cewa, ana gabatar muku da wannan jerin tattaunawa kan bahasin Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimi mai alaka da Imamin Zamani (AF) ga ku masana masu daraja.
Karsashi da kuzarin dan Adam a tsawon rayuwarsa ta daidaiku da ta zamantakewa, ya ginu ne akan ni'imar "Fata" da "Jira" (Intizar). Idan har dan Adam ba shi da wani fata game da gaba, rayuwa ba za ta kasance da wata ma'ana mai zurfi a gare shi ba. Abin da yake sanya dan Adam ya kasance da fatan rayuwa kuma yake sanya ta kasance da sha'awa, sannan yake sanya damuwa da bacin rai su zama masu sauki a gare shi, shi ne jira da fatan samun kyakkyawar gaba mai haske da ci gaba, wadda a cikinta za a ba da amsa cikakka ga dukkan bukatunsa na ruhi da na jiki baki daya. Dan Adam a karkashin inuwar wannan jira da fata ne yake jure wa radadi da wahahalun rayuwa kuma yake ci gaba da tafiyarsa.
Mabiya Shi'a, ta hanyar amfani da koyarwar Ahlul Baiti (A.S), sun sanya wannan fata da jira na samun kyakkyawar gaba a matsayin fitilar haskaka hanyarsu ta rayuwa.
Ma'anar "Intizarul Faraj" A Harshe Da Kuma Isdilahance
"Intizar" (Jira), a harshe (Lugga) yana nufin sanya ido da jiran zuwan wani abu ko wani mutum; amma a Isdilahance, yana nufin sanya ido ga bayyanar ajiyar Ubangiji ta karshe (Imam Mahdi) da kuma shirya kai domin taimaka masa wajen kafa gwamnatin adalci a daukacin fadin duniya.
A wani fadin kuma: "(Jira) wani yanayi ne na ruhi wanda ke haifar da samar da yanayin shirya kai (na mutane) domin abin da suke jira, kuma akasinsa shi ne yanke kauna da rashin fata. Duk lokacin da jiran ya kasance mai yawa, kuma duk lokacin da wutar jiran ta kasance mai ruruwa da haske, motsi da kuzarin mutum — kuma a sakamakon haka, shirya kansa — za su kasance mafi girma."
"Faraj" yana nufin "Samun Sauki" (Yaye damuwa ko bude kofa). Jiran samun faraj, abu ne da ya samo asali daga dabi'ar dan Adam (Fitrah) ta neman kamala; koda yake akwai wasu abubuwan daban da su ma za su iya zama tushen wannan jira.
Sabanin zaton wasu da ke tunanin cewa ra'ayin Mahdawiyya abu ne da mabiya Shi'a suka ƙirƙire shi da kansu, imani da Mahdawiyya bai takaitu ga mabiya Ahlul Baiti (A.S) kadai ba, a'a, yana da babban bangare na akidojin Musulunci kuma yana daya daga cikin muhimman lamura masu tushe a cikin shika-shikan Musulunci (Usul) wanda ya kafu a tsakanin daukacin kungiyoyi da mazhabobin Musulunci baki daya bisa bisharorin Alkur'ani mai girma da koyarwar Annabi Mai Daraja (S.A.W.A). Riwayoyin da ke da alaka da Imam Mahdi (A.F) — kamar yadda suka zo a cikin majiyoyin Shi'a — sun kuma zo a cikin litattafai da dama sanannu na mabiya Ahlus Sunnah.
Saboda haka, imani da samun nasarar karshe ta dakarun gaskiya, da tabbatar da dabi'u na gari na dan Adam baki daya ta hannun wani babban mutum mai daraja wanda a cikin riwayoyin Musulunci aka bayyana shi da "Mahdi", abu ne da ya samo asali daga wahayin Ubangiji; a saboda haka, jiran wancan zamani, baya ga cewa ana ganin sa a cikin tarin akidojin daukacin mabiya addinai na sama, yana da wani babban muhimmanci na musamman a tsakanin Musulmi baki daya.
Matsayin Jira (Intizar) A Cikin Al'adun Shi'a
A cikin wani takaitaccen bincike, riwayoyin da aka yi maganar Intizar a cikinsu an raba su zuwa gida biyu: "Jiran samun faraj a ma'anarsa ta gama-gari (Aam)" da kuma "Jiran samun faraj a ma'anarsa ta musamman (Khas)"...
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An ɗauko daga littafin "Darsnameh-ye Mahdawiyyat; na Khodamorad Salimiyan", tare da dan canji kadan.
Ra'ayinka