Kamar yadda wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, Sheikh Ibraheem Zakzaky ya yi ishara da faɗin girman hali da gwagwarmayar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yana mai cewa: "yin magana a kan jajircewarsa na nufin shiga fage mai faɗi wanda ba zai yiwu a tattara shi cikin ɗan lokaci kaɗan ba." Ya ƙara da cewa tun farkon rayuwarsa ya kasance cikin tafarkin gwagwarmaya a hanyar Allah, kuma ya tashi ne a cikin iyali mai ilimi da falala.
Da yake magana kan tarihin ilimi da gwagwarmayarsa, Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa Ayatullah Khamenei (Q) ya tashi a cikin gida mai addini, kuma ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ɗaliban Imam Khumaini (Q). A zamanin mulkin Pahlavi, saboda rawar da yake takawa a fafutukar Musulunci, an kama shi kuma an tsare shi sau da dama.
Jagoran Harkar Musulunci ta Nijeriya ya bayyana cewa bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Khamenei ya zama ɗaya daga cikin manyan ginshiƙai masu tasiri a tsarin Musulunci. Ya jaddada cewa maƙiyan juyin juya hali sun yi ƙoƙarin dakatar da tafiyar juyin juya hali ta hanyar kawar da manyan jagorori, kuma saboda haka ne aka kai masa hari na ta’addanci.
Ya ci gaba da cewa: "a ɗaya daga cikin waɗannan hare-haren ta’addanci, sakamakon fashewar bam, Ayatollah Khamenei ya ji mummunan rauni, inda hannunsa na dama ya sami lahani. Sai dai, da ikon Allah, an ƙaddara ya rayu domin ya ci gaba da taka rawar tarihi a jagorancin al’umma."
Sheikh Zakzaky ya kuma yi ishara da zaɓen Ayatullah Khamenei (R) bayan wafatin Imam Khumaini (RA) a matsayin magajinsa, yana mai cewa: "duk da tawali’unsa da rashin sha’awarsa a farko ga wannan matsayi, Majalisar Kwararru ta jagoranci ta yanke hukunci cewa shi ne mafi cancanta don ɗaukar wannan nauyi mai girma, kuma jagorancin Juyin Juya Halin Musulunci ya ci gaba a ƙarƙashin shugabancinsa."
Ya kuma yi magana kan rawar da Ayatullah Khamenei ya taka a lokacin Yaƙin Kare Ƙasa, yana cewa: "ko da yake ba ƙwararren soja ba ne, amma da ruhin jihadi da jarumtaka a fagen fama, ya nuna cikakken alhaki da jajircewa ga al’ummar Musulunci."
A ɓangaren ƙarshe na jawabinsa, Sheikh Zakzaky ya yabawa halayen ilimi, ruhi da gwagwarmayar Ayatullah Khamenei, tare da jaddada cewa zai ci gaba da kasancewa a kan wannan tafarkin, kuma zai ci gaba da wannan hanya.
Haka nan ya bayyana fatan cewa hanyar da Imam Khumaini (R) da Ayatullah Khamenei suka shimfiɗa za ta ci gaba, kuma al’ummar Musulunci za ta samu ɗaukaka da cigaba a ƙarƙashin wannan tafarki.
Ra'ayinka