Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Jalal Bani Hashimi, malamin Hauzar ilimi a Tehran, a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza a Tehran, ya yi bayani kan alamomin bayyanar da kuma nauyin da ke kan mabiya Shi’a a zamanin jira (intizar). Ya ce: "Shubuhohin da ake yi kan Mahdawiyya su ne abubuwan da ke jefa asalin lamarin cikin tambaya, kamar cewa wai babu Imam, ko ta yaya yaro mai shekaru biyar zai zama Imam? Dole ne mu fahimci cewa alamomi da shubuhohi abubuwa biyu ne mabambanta, kuma a yau matasa da dama suna da tambayoyi a kansu."
Limamin Masallacin Ashtiyaniha ya ci gaba da cewa a tattaunawar alamomin bayyana (zuhur), an ruwaito cewa a lokacin bayyanar Imam (A.J) zalunci da fasadi za su yawaita a duniya kuma duniya za ta kusanci halaka. To me ya sa a yau duk da wannan yawan zalunci, bayyanar ba ta faru ba? A bahasin Mahdawiyya muna da batun imamancin Imam da kuma batun mulkinsa. Daga cikin batun Imamanci, kafa gwamnati da jagoranci na addini shi ne a gaba. Matsayin Imam yana da alaƙa da gwamnati ta yadda al’umma za su mara masa baya, su yi masa mubaya’a, su bi tafarkinsa domin a samar da yanayin bayyanar Waliyyul Asr (A.J).
Wazifarmu shi ne mu bi Imam kuma mu fifita bukatarsa kan tamu
Masanin addinin ya ƙara da cewa: "Idan har har zuwa yau bayyanar ba ta faru ba, hakan na nufin ba a shirya yanayin mulkin Imam ba. A cikin Imamai, Amirul Muminin Ali (A.S) da Imam Hasan Mujtaba (A.S) ne kaɗai suka yi mulki na ɗan wani lokaci. Hazrat Hujja (A.F) a matsayinsa na Imami na zamani yana da imamancinsa, kuma a ranar 9 ga Rabi’ul Awwal da sauran kwanaki muna sabunta mubaya’a gare shi. Wajibi ne a kanmu mu bi Imam, mu fifita bukatarsa (A.J) kan namu, mu ɗauki matakai mu taimake shi wajen kafa gwamnatin Musulunci.
Ya jaddada cewa ɓoyuwa (gaiba) ba yana nufin rashin gani ba ne. Idan Imam Mahdi (A.J) bai bayyana kansa gare mu ba har zuwa yau, saboda yanayin mulkinsa bai cika ba ne. Wani lokaci maimakon mu shagaltu da taimakon Imam da samar da gwamnatin Mahdawiyya ta duniya, sai mu shagaltu da alamomin bayyanar. Alhali taimakon Imam da samar da yanayin bayyanar yana farawa ne da gyaran kai, domin mai jira na gaskiya yana gyara kansa kuma yana da damuwa da al’umma."
Hujjatul Islam wal Muslimin Bani Hashimi ya ce: "Wani lokaci maimakon mu yi aiki domin bayyanar, sai mu shagaltu da ƙayyade lokacin bayyanar, mu bar asali mu kama reshe. Abin takaici, al’umma wani lokaci suna mayar da hankali kan abubuwan da ba sa taimakawa wajen samar da yanayin bayyanar."
Da yake magana kan illolin da suka shafi Mahdawiyya, ya ce: "Daga cikin manyan illoli akwai karkatar da mutane daga aikin shimfiɗa hanyoyin bayyanar. Akwai matsaloli masu tsanani da dama, ciki har da shagaltuwa da labaran haɗuwa da Imam, aurensa da wasu bayanan rayuwarsa. Mafi muni daga cikin wadannan shi ne ɗaukar jira a matsayin abu mara amfani ko kuma nuna halin ko-in-kula da jira, wato wasu suna tunanin mai jira ya zama marar tasiri."
Juyin Juya Halin Musulunci ya sauya fahimtar Mahdawiyya
Masanin ya nuna cewa Juyin Juya Halin Musulunci a ƙasarmu ya sauya fahimtar Mahdawiyya, kuma ya kamata mu gode wa Imam Khumaini (R). A cewarsa: “Jiran samun sauƙi (faraj) shi ne jiran samun ƙarfin Musulunci.” Wannan ra’ayi yana kallon mai jira a matsayin mutum mai ƙoƙari."
Ya ƙara da cewa Imam Khumaini (Q) ya yi magana kan aiwatar da tsarin Musulunci a duniya domin a kawar da zalunci da danniya, a kuma samar da gabatarwar Zuhur. Amma a yau wasu suna kuskure suna cewa duk lokacin da zalunci ya ƙaru, to bayyanar ta fi kusa. Ya kamata a fayyace wa al’umma cewa mai jira na gaskiya yana tsayawa gaban zalunci. Jira yana nufin mantawa da kai da kuma mayar da hankali gaba ɗaya wajen ƙarfafa Musulunci.
A ƙarshe, Hujjatul Islam wal Muslimin Bani Hashimi ya ce: "Bisa ga ruwayoyi da bayanai, bayyanar Imam Mahdi (A.J) al’amari ne da Allah Ya ɓoye lokacinsa daga mutane, kuma duk lokacin da nufin Allah ya tabbata, yanayin bayyanar zai cika. Idan da za a bayyana lokacin bayyanar tun da wuri, azzalumai za su tattara dukkan ƙarfinsu domin kashe wannan hasken Allah da hana adalci yaduwa a duniya."
Ra'ayinka