A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, saƙon Ayatullah Makarim Shirazi bayan hare‑haren ta’addancin hukumar Sahyoniyawa a Lebanon ya kasance kamar haka:
Bismillahir Rahmanir Rahim
Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un
Labarin hare‑haren ta’addanci da ban‑takaici da gwamnatin Sahyoniyawa ta kai wasu yankunan ƙasar Lebanon, da kuma shahadar da raunatar da daruruwan mutane marasa galihu — musamman mata da yara — ya jawo mana bakin ciki da baƙin rai sosai.
Ba shakka wannan gwamnati, wadda ba ta da koda ɗan ƙaramin girmama ka’idojin ɗabi’a na ɗan adam, ta hanyar kai hari kan asibitoci, muhimman kayayyakin more rayuwa da cibiyoyin fararen hula, ta aikata manyan laifuka da ke tayar da hankalin kowanne mutum mai hankali da ‘yanci.
Ya kamata al’ummomin Musulmi, masu kare ‘yanci a duniya da gwamnatocin Musulmai su tallafa wa mutanen wannan ƙasa marasa kariya da kuma Hizbullah masu jarumta, su kuma lura cewa gogewar baya ta nuna cewa sakaci ko sassauci a gaban zalunci yana haifar da ƙara tsananta shi.
Ana sa ran jami’ai da hukumomin da suka dace na Jamhuriyar Musulmi ta Iran, kamar yadda suka saba, su ci gaba da aiwatar da nauyin ɗan adam da na addininsu wajen rage radadin wannan bala’i da kuma tallafa wa mutanen Lebanon da ake zalunta.
Ina mika ta’aziyyata ga Sahibuz Zaman (AF), ina roƙon Allah Madaukaki ya ɗaga darajar shahidai, ya ba wa waɗanda suka ji rauni lafiya cikin gaggawa, kuma ya ba wa iyalan da suka yi rashi haƙuri da lada.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu
Qom – Nasir Makarim Sirazi
Ra'ayinka