Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, Ayatullah Jawadi Amuli — ɗaya daga cikin manyan maraji’i'an taƙlidi — ya jaddada cewa: “Yaƙi yana da hawa da sauka. Wani lokaci muminai sukan yi nasara, wani lokaci kuma kafirai; amma duk da haka sakamakon ƙarshe yana ga masu jihadi a tafarkin Allah.”
Ya kuma yi ishara da aya ta 140 a Suratul Ali‑Imran اِن یَمسَسکُم قَرحٌ فَقَد مَسَّ القَومَ قَرحٌ" مِثلُه ..." (“Idan wani rauni ya same ku, to lallai wani rauni makamancinsa ya riga ya sami waɗancan mutane ...”) , yana cewa: shan wahala ko asara wata jarrabawa ce daga Allah. A yaƙi dukkan ɓangarori suna iya rasa rai da dukiya, amma muminai suna amfana da rahamar Allah, alhali kafirai ba su da wannan falala.
﴿اِن تَکونوا تَألَمونَ فَاِنَّهُم یَألَمونَ کَما تَألَمونَ وتَرجونَ مِنَ اللهِ ما لایَرجون / آیه ۱۰۴ سوره نساء﴾.
(“Idan kuna jin zafi, to su ma suna jin zafi kamar yadda kuke ji; amma ku kuna fatan abin da ba su fata daga Allah.” — Suratun Nisa’i aya ta 104).
Wannan babban malami ya kuma jaddada muhimmancin ikhlasi da tsayin daka ga masu jihadi, yana cewa: "duk wanda ya yi iƙirarin yaƙi a tafarkin Allah ba lallai ba ne ya yi nasara da mu’ujiza a kowane lokaci ba. Wani lokaci sai ya dandani shan kashi na wucin gadi da kuma nasara, domin a gwada ainihin gaskiyarsa."
Ya ci gaba da cewa: "Amirul Muminin, Imam Ali (AS.) ya yi magana game da hawa da saukan yaƙi inda ya ce:
«ولقد کنّا مع رسول الله صلی الله علیه و آله و سلم نقتل آباءَنا و ابناءَنا و إخواننا و أعمامنا...»
“Mun kasance tare da Manzon Allah (SAWA) a fagen yaƙi, har muka yaƙi iyayenmu, ’ya’yanmu, ’yan’uwanmu da kawunanmu.”
Wato muna tare da Manzon Allah a filin fama, inda da umarnin Allah muka yaƙi har da danginmu. Wannan kuwa bai haifar da komai ba face ƙarfafa imani, tsayin daka, haƙuri a cikin wahala, da kuma ƙwazo wajen jihadi da abokan gaba."
Ya ƙara da cewa: "wani lokaci mutum daga gare mu da wani daga rundunar abokan gaba suna kai wa juna hari, kowanne yana ƙoƙarin kashe ɗayan. Wani lokaci nasara tana gefenmu, wani lokaci kuma gefen abokan gaba. Amma lokacin da Allah ya gwada mu ya ga gaskiyarmu, sai Ya wulakanta abokan gaba kuma Ya ɗaga tutar nasarar mu."
Madogara: Tasnim – Jildi na 19, shafi na 534
Ra'ayinka