A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Sayyid Muhammad Sa'eedi, limamin Juma’ar birnin Qom, ya bayyana a hudubar Juma’a cewa Iran ba za ta bari Amurka ta ƙayyade lokacin ƙarshen yaƙin ba. Ya kuma ce mashigar Hormuz ba zai koma kamar yadda yake kafin yaƙin ba.
Ya bayyana cewa a cikin “yaƙin haɗaka”, akwai raba aiki tsakanin sojoji da al’umma, inda sojoji ke kare ƙasa a filin daga, yayin da kasancewar jama’a a cikin al’umma a tituna ke zama goyon baya ga wannan tsayin daka.
Ayatullah Sa'eedi ya kuma yi iƙirarin cewa manufofin farko na Amurka da Isra’ila a yaƙin ba su cimma nasara ba, kuma hakan ya nuna cewa ma’aunin ƙarfi ya sauya.
A wani ɓangare na hudubar, ya yi ishara da ayoyin Suratul Fath, yana mai jaddada darussan da suka shafi biyayya, tuba da jarabawoyin Ubangiji ga al’umma.
A ƙarshen hudubar, yayi addu'ar samun nasara ga rundunar gaskiya ta jamhuriyar Musulunci da ƙungiyoyin gwagwarmaya tare da gaggauta kawo karshen Amurka da Isra'ila.
Ra'ayinka