Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammad Haj Abulqasim Dolabi ya bayyana hakan a cikin taron karatun juzu’i na 25 na Alƙur’ani. Yayin da yake ishara da aya ta 23 ta Suratul Shura, ya ce: "Al’ummar da ke son tsayawa da kafafunta, kada ta rusuna wa zaluncin makiya, kuma ta iya tunkarar danniya, tana bukatar wani ginshiki mai ƙarfi da za ta jingina da shi domin ta iya jure matsin lamba."
Ya ƙara da cewa: "Daya daga cikin mafi kyawun hanyoyin samun wannan ginshiki shi ne soyayya ga waliyyan Allah domin wannan soyayya tana ƙarfafa mutum a yayin wahalhalu.
Mai jawabin ya jaddada cewa Allah Madaukaki a cikin aya ta 23 ya ce: “Ladan sakona shi ne kauna ga dangin tsarki (Ahlul‑Baiti)”, wanda hakan ke nuna girman matsayinsu.
Ya bayyana cewa waɗanda ake nufi da “Dhil‑Qurba” su ne Imam Ali (AS), Sayyida Zahra (SA) da ‘ya’yansu ma’asumai, kuma mawadda (soyayya) tana nufin matsayi mai girma na kauna. Wannan kauna ba wai so a zuciya kawai ba ne, sai dai ta kai ga soyayya mai zurfi wadda za ta haifar da bin su a aikace.
Malamin Hauzar ya ce: "Tambaya mai muhimmanci ita ce me ya sa Manzon Allah (SAWA) bai sanya ladan sakonsa a cikin abubuwa kamar sallah, hajji ko azumi ba, sai ya sanya soyayya ga Ahlul‑Baiti?'
Ya ce amsar ita ce: "Idan ibada ta kasance ba tare da wilaya (jagorancin Ahlul‑Baiti) ba, to ibadar za ta zama marar ruhi kuma marar ma’ana. Saboda haka duk ibadu dole su kasance tare da soyayya ga waliyyan Allah; domin ibada ba tare da wilaya ba tana iya zama kamar ibadar masu tsattsauran ra’ayi irin na Daesh ko wahabiyawa."
Hujjatul Islam Haj Abulqasim ya kuma jaddada cewa wilaya da soyayya suna sa mutum ya ƙaunaci sauran mutane musamman masu rauni da waɗanda ake zalunta, ya kuma zama mai kare su.
Ya tunatar cewa a cikin Ziyarar Jami‘a Kabira an bayyana cewa wilayar Ahlul‑Baiti (AS) ce ke sa ni’imomi su cika, sabani ya ragu, kuma zukata su kusanci juna.
Ya ce: "Sabanin ra’ayi na siyasa, tunani ko ma na cikin iyali yana iya raba zukata; amma idan soyayyar Imam Husain (AS) ta shiga tsakani, kowa yana taruwa a ƙarƙashin tutarsa." Ya ce tattakin Arba’in ma yana da asali daga wannan tafarkin soyayya, kuma yana haɗa al’ummar Musulmi.
Malamin Hauzar ya jaddada cewa dole ne a girmama majalisun Ahlul‑Baiti (AS), domin idan a yau ƙasarmu tana tsaye a gaban makiya kamar dutse, to da albarkacin waɗannan majalisu ne. Ya ce: "Da ba a samu majalisun makokin Imam Husain (AS) ba, da da yawa daga cikinmu sun zama masu ra’ayin wahabiyanci."
A ƙarshe ya ce: "Sirrin juriyar al’ummar Iran a gaban masu girman kai na duniya shi ne irin sirrin juriya na Sahabbai 72 na Imam Husain (AS) a Karbala a gaban rundunar Yazid."
Ra'ayinka