A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Dandalin Matasan Harkar Musulunci a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), sun gabatar da Ijtima na kwana ɗaya da wuni ɗaya a garin Birnin Kudu da ke ƙarƙashin yankin Rasulul Akram.
Rahoton da aka samu ya nuna cewa, lokacin da yake gabatar da jawabin rufe taron, wakilin ƴan uwa almajiran Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) na Birnin Kudu, Sheikh Sa'eed Ibrahim, ya yaba da yadda aka gudanar da taron cikin tsari, sannan ya buƙaci matasa su yi aiki da ilimin da suka samu a aikace cikin rayuwarsu ta yau da kullum.
A cikin bayanin nasa, ya jaddada cewa: "Tun farko Harkar Musulunci ta ginu ne a kan ilimi da aiki, kuma ba za a iya raba su ba. Ilimi da aiki tamkar ƙafafu biyu ne na mutum; domin tafiya ba za ta yiwu yadda ya kamata ba idan mutum ya dogara da ƙafa guda ɗaya kawai."
Haka zalika, ya yi addu'ar samun damar ci gaba da gudanar da irin wadannan taruka domin ƙara bunƙasa ilimi da tarbiyyar matasa.
Fahimtar Koyarwar Ahlul Baiti (AS) da Mas'alolin Shari'a
A cikin darussan da aka gabatar a taron sun haɗa da Mas'alolin Fikihu inda Malama A'isha Yunusa ta gabatar da darasi daga littafin Muntakhabul Ahkam, inda ta jaddada cewa wajibi ne ga kowane mukallafi ya san mas'alolin addini da suka shafi ibadarsa. Ta kuma kirayi matasa da su ba da himma wajen neman ilimin addini domin tsara rayuwarsu bisa koyarwar Musulunci.
Bayanin Aƙida: Malam Nasiru Ibrahim ya gabatar da darasi daga littafin Aƙa'iduna, inda ya yi bayani kan imani da Allah da fahimtar Ahlul Baiti (AS) game da alamomin Allah. Ya kuma yi karin haske kan bambancin fahimta tsakanin Mazhabar Ahlul Baiti (AS) da sauran mazhabobi game da ayar “Yadullahi fawqa aydihim”, inda ya bayyana cewa "Hannun Allah" a ayar yana nufin ikonsa da ƙarfinsa ne, ba wai hannu irin na halitta ba.
Ayyukan Ibada da Ilimin Wilaya
Baya ga darussan ilimi, mahalarta taron sun raya daren da Sallar Tahajjud, addu'o'i da azkar har zuwa sallar Asuba.
Bayan sallar Asuba kuma, Sheikh Sa'eed Ibrahim ya gabatar da darasi daga littafin 'Durus fi Hukumatil Islamiyya' (Ilimin Wilayatul Faƙih) na Imam Khumaini (QS).
Kafin a rufe taron, mahalarta sun gudanar da addu'o'i na samun kariya da tsawon rai ga Jagoran Harkar Musulunci Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), ɗaukakar Shahidai, nasarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma kariya ga daukacin al'ummar Musulmi.








Ra'ayinka