Litinin 16 Maris 2026 - 07:27
Muhimmancin Amfani da Ragowar Lokutan Watan Ramadan

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Afrazide ya yi nuni da ƙarancin lokacin da ya rage na cin moriyar watan liyafar Allah, yana cewa: "Domin fahimtar wannan dama mai daraja da kyau, dole ne mutum ya kula da tsarkin zuciya da lafiyar ruhinsa."

A wata hira da ya yi da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza a Sari, Hujjatul Islam wal Muslimin Akbar Afrazide ya ce: "Wata mai alfarma na Ramadan, wato watan liyafar Allah, yana dab da ƙarewa, kuma mutum mai basira yana amfani da kowane lokaci na wannan lokaci mai daraja."

Ya ƙara da cewa Sayyid Ibn Tawus ya kawo a cikin littafinsa Iqbal al‑A‘mal cewa: 

«عن جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اَللَّهِ اَلْأَنْصَارِیِّ، قَالَ: دَخَلْتُ عَلَی رَسُولِ اَللَّهِ (ص) فِی آخِرِ جُمُعَةٍ مِنْ شَهْرِ رَمَضَانَ، فَلَمَّا أَبْصَرَنِی [بَصُرَ بِی] قَالَ لِی: یَا جَابِرُ، هَذَا آخِرُ جُمُعَةٍ مِنْ شَهْرِ رَمَضَانَ، فَوَدِّعْهُ وَ قُلْ: (اَللَّهُمَّ لاَ تَجْعَلْهُ آخِرَ اَلْعَهْدِ مِنْ صِیَامِنَا إِیَّاهُ، فَإِنْ جَعَلْتَهُ فَاجْعَلْنِی مَرْحُوماً وَ لاَ تَجْعَلْنِی مَحْرُوماً)؛ فَإِنَّهُ مَنْ قَالَ ذَلِکَ ظَفِرَ بِإِحْدَی اَلْحُسْنَیَیْنِ: إِمَّا بِبُلُوغِ شَهْرِ رَمَضَانَ مِنْ قَابِلٍ، وَ إِمَّا بِغُفْرَانِ اَللَّهِ وَ رَحْمَتِهِ "Daga Jabir bn Abdullah al‑Ansari ya ce: na shiga wajen Manzon Allah (SAW) a Juma’ar ƙarshe ta watan Ramadan. Da ya gan ni sai ya ce:  “Ya Jabir! Wannan ita ce Jumma’ar ƙarshe ta watan Ramadan. Ka yi masa bankwana ka ce: Ya Allah! Kada Ka sanya wannan watan Ramadan ya zama na ƙarshe da zan  azumce sa. Idan kuwa Ka ƙaddara shi ya zama na ƙarshe a rayuwata, to Ka sa ni cikin rahamarKa, kada Ka bar ni cikin waɗanda aka hana.”  

Manzon Allah (SAWA) ya ƙara da cewa: "Duk wanda ya faɗi wannan zikiri, zai samu ɗaya daga cikin alherai biyu: ko dai zai sake kaiwa watan Ramadan na shekara mai zuwa, ko kuma zai samu gafarar Allah da rahamarsa.  

(Iqbal al‑A‘mal na Sayyid Ibn Tawus, juzu’i na 1, shafi na 243)

Masanin addinin ya kuma ce: "Daya daga cikin hanyoyin fahimtar maganganun Ma’asumai (AS) shi ne tsarkin zuciyar mutum. Akwai abubuwa da ke taimakawa wajen samun hakan, daga cikinsu mafi muhimmanci akwai yaƙi da son zuciya, yin sallar dare da tashi sahur, yin azumi, sai kuma wataƙila mafi muhimmanci shi ne zubar da hawaye saboda Imam Husain (AS). Wadannan abubuwa suna taimaka wa mutum ya tsarkake ruhinsa domin ya fi fahimtar kalaman Ma’asumai (AS)."

Ya kuma jaddada muhimmancin addu’a, yana cewa: "Addu’a wata hanya ce da mutum ke kaiwa ga kamala. Yin addu’a ba wai don samun lada ba ne kawai; domin abubuwan ma’ana masu zurfi da ke cikin addu’o’in da aka ruwaito suna koyar da ilimi, hikima da darussan ɗabi’a. Watan Ramadan dama ce ta kusanci da addu’o’i masu daraja kamar Addu’ar Abu Hamza al‑Thumali da Addu’ar Kumail, ta yadda mutum zai karanta su tare da fahimtar ma’anoninsu domin ya koyi darussan rayuwa."

Hujjatul Islam wal Muslimin Afrazide ya kara da cewa: "Daya daga cikin manyan darussa a cikin Addu’ar Abu Hamza al‑Thumali shi ne tuna mutuwa da shirya mata. Imam Sajjad (AS) a cikin wannan addu’a mai daraja yana yawan tunatar da mutane game da lokutan tsoro na mutuwa da binne mutum, yana kuma gargadin kada mutum ya zama mai gafala da wannan hakika."

A ƙarshe ya ce: Ayatullah al‑Uzma Khonsari (R) wani babban malami ne wanda Imam Khumaini (R) ya bayyana a matsayin mai ruhi mai tsarki. Har ma lokacin da aka tambayi Imam Khumaini game da adalcin Ayatullah Khonsari, sai ya ce:  “Mu muna shakkar ismar sa (anya ba ma'asumi ba ne?), ku kuma kuna tambayar adalcinsa?”

Haka nan Ayatullah Mujtahidi Tehrani ya ce bai taɓa ganin wani marja’i a rayuwarsa ba wanda bai da son zuciya ba kamar shi. Duk da irin wannan matsayi na ruhaniya da kamala, wannan babban malami ya ce: “Zan bar wannan duniya ina jin kamar hannuna babu komai; abu ɗaya kawai nake fata zai zama sanadin tsirata, shi ne hawayen da nake zubarwa a majalisun makokin Ahlul Baiti (AS).”

Irin wannan magana daga babban malami ya kamata ta tayar da wadanda suka gafala daga mutuwa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha