Alhamis 13 Agusta 2026 - 21:48
Wadannan Su Ne Bayin Allah na Musamman (Ibadur-Rahman)

Hauza/ Alƙur’ani Mai Girma ya bayyana siffofin “Bayin Mai Rahama” (Ibadur-Rahman), inda ya kawo tarin kyawawan halaye na akhlaƙ, ibada da zamantakewa; daga cikin su akwai tawali’u, haƙuri, tsayuwar dare, nisantar shirka, kisa, zina da shaidar ƙarya, lura da ayoyin Allah, da yin addu’a domin samun iyali nagari kuma salihai.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, siffofin “ibadur-Rahman” a cikin Alƙur’ani suna gabatar da cikakken hoto na muminai nagari; mutane waɗanda suke da tawali’u wajen mu’amala da jama’a, suke amsa wa jahilai cikin ladabi da taushi, suke tsayuwar dare, masu addu’a da sadaka, kuma suke nisantar zunubi da ayyukan banza. A cikin wannan rubutu, marigayi Allama Hasan Zadeh Amuli ya bayyana wasu siffofi 11 na musamman na bayin Allah daga Alƙur’ani Mai Girma, kamar haka:

Wadannan su ne Bayin Allah na musamman:

1. Suna tafiya a doron ƙasa cikin tawali’u da ƙasƙantar da kai.

2. Idan jahilai suka yi musu magana cikin tsawa ko zagi, suna amsa musu da lafiyar zuciya da magana mai kyau.

3. Suna shafe dararensu cikin sujjada da tsayuwa domin ƙaunar Allah da neman yardarsa.

4. A kodayaushe suna roƙo da kukan tawali’u suna cewa: “Ya Ubangijinmu! Ka nisantar da azabar Jahannama daga gare mu, domin lalle azabarta mummunar azaba ce, kuma Jahannama mummunar makoma ce.”

5. A wajen bayar da sadaka da taimako, ba sa yin almubazzaranci, sai dai sun riƙi tafarki matsakaici.

6. Ba sa haɗa Allah da wani abokin tarayya, kuma Allah kaɗai suke kira da roƙo.

7. Suna nisantar kisa da aikata laifuffuka waɗanda Allah Ya haramta.

8. Ba sa kusantar aikata mummunan fasikanci, wato zina. Duk wanda ya aikata wannan mummunan aiki zai ga azaba ta har abada, kuma a Ranar Alƙiyama za a ninka masa azaba, sai dai waɗanda suka tuba suka aikata ayyukan ƙwarai. A wannan hali, Allah zai mayar da zunubansu zuwa lada. Kuma duk wanda ya tuba, to lalle Allah Yana karɓar tubarsa.

9. Ba sa yin shaidar ƙarya ko shaidar da ba ta dace da gaskiya ba.

10. Idan suka wuce wajen wani aiki na banza ko mummuna da mutanen banza suke aikatawa, suna kauce masa cikin mutunci, ba tare da shiga cikinsa ba.

11. Idan aka tunasar da su da ayoyin Allah, ba sa wucewa ta kansu kamar makafi da kurame. A’a, suna kallonsu da zuciya mai fahimta da idon basira, suna yin tunani a kansu domin iliminsu da imaninsu su ƙaru.

A lokacin addu’a, suna cewa wa Allah: “Ya Ubangijinmu! Ka sanya mana daga cikin matanmu da ’ya’yanmu waɗanda za su zama sanyin idanu gare mu, kuma Ka sanya mu jagororin masu taƙawa.”

Sakamakon haƙurin irin waɗannan bayin Allah zai kasance gidajen aljanna, inda za su haɗu da juna cikin salama, aminci da farin ciki. Za su kasance a cikin kyakkyawar Aljanna har abada, ba tare da ƙarewa ba.

Ya kai Annabi! Ka gaya wa al’ummarka cewa: “Da ba don addu’arku da kukan neman Allah ba, da Ubangijinku bai damu da ku ba. Domin a baya kun kasance kuna ƙaryata ayoyin Allah da annabawanSa, kuma wannan ƙaryatawar za ta riske ku, ba za ta rabu da ku ba. Saboda haka, ku kawar da ita ta hanyar addu’a.”

Madogara:

Siraɗul-Suluk

Allama Hasan Zadeh Amuli 

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha