Laraba 29 Yuli 2026 - 21:37
Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Sun Fara Tattakin Arba'in Daga Najaf zuwa Karbala

Hauza | Almajiran Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) sun fara tattakin Arba'in na bana daga yankin Thawratul Ishrin da ke birnin Najaf Ashraf zuwa Karbala Mai Tsarki, a safiyar yau Laraba, 14 ga Safar 1448H (29 ga Yuli, 2026).

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Almajiran Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) sun fara tattakin Arba'in na bana daga yankin Thawratul Ishrin da ke birnin Najaf Ashraf zuwa Karbala Mai Tsarki, a safiyar yau Laraba, 14 ga Safar 1448H (29 ga Yuli, 2026).

An fara tattakin ne da misalin ƙarfe 6:30 na safe, inda kafin fara tafiyar aka saurari taƙaitaccen jawabi daga shugaban tawagar tattakin na bana, Sheikh Aliyu Tirmizi Kaduna, wanda ya jaddada muhimmancin raya saƙon Ashura da manufofin juyin Imam Husain (A.S.).

Masu tattakin sun fara tafiyar cikin tsari, natsuwa da yanayin jimami, suna nuna alhini da tausayawa ga irin wahalhalun da Iyalan Manzon Allah (S.A.W.A) suka fuskanta bayan aukuwar masifar Ashura, lokacin da aka tilasta musu tafiya daga Karbala zuwa Dimashƙ a matsayin fursunoni.

A cewar masu shirya tattakin, wannan tafiya ba wai tunawa da Arba'in kaɗai ba ce, har ila yau wata hanya ce ta ƙoƙarin fahimtar wani ɓangare na wahalhalu da ƙuncin da Ahlul Baiti (A.S.) suka sha a wannan tafiya mai cike da baƙin ciki.

Yayin da suke ci gaba da nufar Karbala Mai Tsarki, mahalarta tattakin suna rera waƙoƙin alhini da marsiyoyin Ashura tare da ɗaukaka taken Imam Husain (A.S.), cikin shirye-shiryen halartar gagarumin taron Arba'in na Sayyidina Aba Abdillahi al-Husain (A.S.).

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Sun Fara Tattakin Arba'in Daga Najaf zuwa Karbala

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Sun Fara Tattakin Arba'in Daga Najaf zuwa Karbala

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Sun Fara Tattakin Arba'in Daga Najaf zuwa Karbala

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Sun Fara Tattakin Arba'in Daga Najaf zuwa Karbala

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Sun Fara Tattakin Arba'in Daga Najaf zuwa Karbala

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Sun Fara Tattakin Arba'in Daga Najaf zuwa Karbala

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Sun Fara Tattakin Arba'in Daga Najaf zuwa Karbala

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha