Alhamis 9 Yuli 2026 - 21:16
Ayatullah A'arafi Ya Yaba da Gagarumar Jana'izar Imam Shahidi a Iraki

Hauza/ Ayatullah Alireza A'arafi ya bayyana cewa abin da ya faru a Iraki, musamman a biranen Najaf da Karbala, a jana'izar tsarkakkar gangar jikin Shahidin Jagora kuma Jagoran Al'umma, Imam Khamene'i (QS), ya nuna zurfin imani, ikhlasi, sadaukarwa da jajircewar al'ummar Iraki.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, cikakken saƙon Ayatullah A'arafi na yabawa da wannan gagarumar jana'iza mai cike da tarihi a Iraki mai ɗaukaka ya zo kamar haka:

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

{مِّنَ ٱلمُؤمِنِینَ رِجَال صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَیهِ فَمِنهُم مَّن قَضَیٰ نَحبَهُۥ وَمِنهُم مَّن یَنتَظِرُ وَمَا بَدَّلُواْ تَبدِیلا}

اَلسَّلامُ عَلَی الْحُسَیْن وَ عَلی عَلَیِ بْن الْحُسَین وَ عَلی اَوْلادِ الْحْسَیْن وَ عَلی اَصحابِ الْحُسَین

Abin da ya faru a Iraki da kuma biranen Najaf da Karbala wajen jana'izar tsarkakkar gangar jikin Shahidin Jagora kuma Jagoran Al'umma, Imam Khamene'i (QS), ya kasance alamar zurfin imani, ikhlasi, sadaukarwa da kuma ƙwazon al'ummar Iraki masu jaruntaka.

Girman halartar al'ummar Iraki, manyan ƙabilu, mata da maza, matasa masu jihadi, malamai, jami'o'i, ƙungiyoyin gwagwarmaya daga Iraki, Lebanon da sauran ƙasashe, tare da ƙungiyoyi daban-daban na zamantakewa da siyasa, da kuma rawar da gwamnatin Iraki, al'ummarta, Haraman Ahlul Baiti (AS) na Najaf da Karbala, musamman Hashdush Sha'abi, suka taka wajen sauƙaƙa da tallafawa wannan taro, sun nuna irin zurfin alaƙar tarihi tsakanin al'ummomi da ƙasashen Iran da Iraki.

Wannan gagarumar jana'iza ta zama wata alama ta haɗin kan al'ummar Musulmi a ƙarƙashin manufofin Allah, 'yanci daga ikon masu girman kai na duniya, da ƙoƙarin kuɓuta daga kangin mulkin Amurka, tare da 'yantar da ƙasashen Musulmi da Falasɗinu mai daraja daga mamayar Amurka da yahudawan sahayoniyya masu ƙwace.

An gudanar da wannan taro mai haske ne a ƙarƙashin albarkar hubbaren Amirul Muminina Imam Ali bn Abi Talib (AS), Imam Husain bn Ali (AS), Hazrat Abul Fadl al-Abbas (AS), sauran Haramai masu tsarki na Ma'asumai (AS), da kuma kaburburan manyan malamai da shahidan Iraki. Wannan al'amari ya rusa tsare-tsaren maƙiyan al'ummar Musulmi, ƙasashen Iraki da Iran, da ƙungiyoyin muƙawama, tare da shimfiɗa sabbin tsare-tsare na farkawar Musulunci, gwagwarmayar al'ummar Musulmi ta duniya, haɗin kan al'ummai domin gina sabon tsari na Musulunci mai cin gashin kansa a yankin da kuma kuɓuta daga mulkin mallaka da girman kai. Da yardar Allah Maɗaukaki da kulawar Imam Mahdi (AJ), tasirin wannan motsi zai kasance mai ƙarfi kuma mai ɗorewa.

Saboda wannan babbar ni'ima da wannan gagarumin tashin tsayen al'ummar Iraki, kungiyoyin muƙawama da al'ummomin yankin, wajibi ne mu yi godiya ga Allah Maɗaukaki. Ina miƙa godiya ta ga al'ummar Iraki, gwamnatinsu da jami'anta, kungiyoyin muƙawama, al'ummomin yankin, da dukkan waɗanda suka halarci wannan gagarumar jana'iza, da kuma waɗanda suka ba ta goyon baya a kwanakin alhinin Sayyidus Shuhada Imam Husain (AS) da Imam Sajjad (AS).

Har ila yau, wajibi ne in yi godiya ta musamman ga jami'an Haramai masu tsarki, manyan malamai, malaman Hauza, tsohuwar Hauzar Najaf Ashraf, ɗalibai da malamai daga Iran, Iraki da sauran ƙasashe, da kuma manyan malaman Hauzar Qum, Ƙungiyar Malaman Hauza (Jami'atul Mudarrisin), Majalisar Koli ta Hauzozin Ilimi da sauran cibiyoyin Hauza daga Qum. Haka kuma ina miƙa godiya ta musamman ga babbar Marja'iyya ta Najaf Ashraf.

Ina fata, ƙarƙashin shiriyar manyan Maraji'ai a Najaf Ashraf da Qum mai tsarki, alaƙar Hauzozin Najaf da Qum za ta ƙara ƙarfi, haka nan haɗin kan al'ummomin Musulmi, kungiyoyin muƙawama da al'ummomin Iraki da Iran zai ƙara ƙarfi wajen cimma manufofin Musulunci. Hakan zai hanzarta tafiya zuwa ga sabon wayewar Musulunci da fitowar hasken Wilayar Imamul Hujjah (AJ), tare da samar da wani sabon babi mai muhimmanci a tarihin haɗin kan al'ummomin biyu, musamman a Arba'in din Imam Husain (AS) da kuma fuskantar hare-haren maƙiya.

Ina da cikakken yaƙini cewa, ƙarƙashin jagorancin Waliyyul Faƙih da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci (Allah Ya tsawaita rayuwarsa), tare da sadaukarwar al'ummomin Musulmi, musamman al'ummomin Iran da Iraki da ƙungiyoyin muƙawama, za mu shaida faɗuwar ikon azzaluman duniya da fitowar ƙarfin Musulunci, tare da nasarar al'ummar Musulmi a Iran, Iraki da kuma duniya baki ɗaya. Ina kuma fata dukkan Hauzozin Ilimi da al'ummomin Musulmi za su ci gaba da kasancewa masu cika alkawarinsu ga Waliyyan Allah, shahidai, manyan malaman addini, Maraji'ai, Imam Khumaini (QS), Imam Shahid Khamene'i (QS), da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci (Allah Ya tsawaita rayuwarsa).

Alireza A'arafi 

Shugaban Hauzozin Ilimin Ƙasar Iran 

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha