A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da jerin darussa na mas'alolin Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimi mai alaƙa da Imamin Zamani – Allah ya gaggauta bayyanarsa.
A cikin bayanan da suka gabata na fa'idojin Ɓoyayyen Imam (Imamul Gha'ib), an tattauna kan tasirin wajibcin kasancewarsa, inda aka yi bayanin cewa dawwamar duniya da rayuwar dukkan halitta ta dogara ne da samuwar wannan babban mutum. A wannan karon kuma, ana magana ne kan alamomin soyayya mara iyaka ta Ɓoyayyen Imam, wacce ta bayyana ta fuskoki daban-daban, domin ya bayyana ga kowa cewa Imam mai alheri da jinkai ne, duk da ɓoyuwarsa (gaibarsa), hasken tausayinsa ya bazu ko'ina kuma ya shafi kowa gwargwadon ikonsa da damarsa, kuma alherinsa da kulawarsa kamar maɓuɓɓugar ruwa ce mai gudana babu tsayawa.
Daga cikin mafi muhimmancin siffofi na mumini shi ne tausayawa da taya 'yan'uwa na addini juyayi. Muminai a cikin al'ummar Musulmi kamar jiki guda suke, inda ciwon kowane sashe ke zama sanadin radadin sauran sassan, sannan jin daɗi da farin cikin kowannensu ke zama sanadin farin cikin sauran, domin su 'yan'uwa ne kamar yadda Alƙur'ani ya bayyana.
A cikin hadisai da dama, Imamai (AS) sun bayyana irin juyayi da damuwarsu ga mabiya (Shi'a), wanda wannan kyakkyawar siffa ke zama sanadin natsuwa da sanyaya zuciyar masoyansu, kuma wani ƙarfin gwiwa ne da ke ba su kwarin gwiwa a cikin fadi-tashin rayuwa, tare da ƙarfafa juriyarsu da jaddada juriya.
Imam Rida (AS) yana cewa:
«مَا مِنْ أَحَدٍ مِنْ شِیعَتِنَا یمْرَضُ إِلَّا مَرِضْنَا لِمَرَضِهِ وَ لَا اغْتَمَّ إِلَّا اغْتَمَمْنَا لِغَمِّهِ وَ لَا یفْرَحُ إِلَّا فَرِحْنَا لِفَرَحِه.»
"Babu wani daga cikin mabiyanmu (Shi'a) da zai yi rashin lafiya face mun yi rashin lafiya saboda rashin lafiyarsa, kuma ba zai shiga damuwa ba face mun damu saboda damuwarsa, kuma ba zai yi farin ciki ba face mun yi farin ciki saboda farin cikinsa." (Biharul Anwar, Juzu'i na 65, Shafi na 167)
Sakamakon haka, Imam saboda tsananin tausayinsa da soyayyarsa ga mabiyansa, yana da mafi girman sadarwa da alaƙa da su, kuma saboda wannan soyayya ce yake zama abokin tarayya a cikin baƙin cikinsu da radadinsu. Kazalika, Imam Sadik (AS) ya bayyana cewa:
«وَ اللَّهِ إِنِّی أَرْحَمُ بِکُمْ مِنْ أَنْفُسِکُم.»
"Wallahi, lallai ni mafi tausayi ne a gare ku fiye da yadda kuke tausayawa kawunanku."(Basa'irud Darajat, Shafi na 265)
A taƙaice, jinsin soyayyar Imam ya bambanta da sauran soyayya. Soyayya ce sahihiya, babu gori, kuma mara iyaka, wadda ba a baki kawai take ba, a'a tana can cikin tsakiyar zuciyarsa da ransa, kuma saboda haka yake a kowane lokaci da jiki da rai ya ke haɗe da mabiya.
Ɗaya daga cikin bayyanannun misalai na wannan soyayya ta Ubangiji a cikin samuwar Imam na Zaman (AF) ita ce yadda ya siffanta lamarin a cikin fadar sa cewa:
«إِنَّهُ أُنْهِی إِلَی ارْتِیابُ جَمَاعَه مِنْکُمْ فِی الدِّینِ وَ مَا دَخَلَهُمْ مِنَ الشَّکِّ وَ الْحَیرَه فِی وُلَاه أَمْرِهِمْ فَغَمَّنَا ذَلِکَ لَکُمْ لَا لَنَا وَ سَأَوْنَا فِیکُمْ لَا فِینَا لِأَنَّ اللَّهَ مَعَنَا فَلَا فَاقَه بِنَا إِلَی غَیرِه.»
"Lallai labari ya iske ni cewa wata kungiya daga cikinku ta fada cikin shakka a cikin addini, kuma shakka da rudani ya shiga zukatansu game da shugabanninsu (Waliyyul amr), saboda haka wannan abu ya sa mu baƙin ciki saboda ku, ba don kanmu ba, kuma ya bata mana rai a kanku, ba a kanmu ba, domin Allah yana tare da mu, saboda haka ba mu da buƙatar wani ba Shi ba." (Biharul Anwar, Juzu'i na 53, Shafi na 178)
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An ɗauko daga littafin "Negin-e Afarinish" tare da ɗan gyara kaɗan
Ra'ayinka