A cewar rahoton wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Sayyid Muhammad Sa'eedi, a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a babban masallacin Quds na birnin Qom, ya mika ta'aziyyarsa na kwanakin juyayin Shahadar Shugaban Shahidai Imam Husain (AS), inda ya kawo jawabi kan manufar juyin juya halin na Imam Husain (AS) daga wasiyyar da ya rubuta wa Muhammad Hanafiyya na cewa: "Ban fito domin yin barna ko girman kai ba, na fito ne domin neman gyara a cikin al'ummar kaka na Muhammadu (SAWA). Ina son in yi umurni da kyakkyawa, in yi hani da mummuna."
Biyayya Ga Mutum Nagari (Abdus-Salih)
Shugaban Haramin Sayyida Fatima Ma'asuma (SA) ya ƙara da cewa, Imam Sadik (AS) a cikin Ziyarar Hazrat Abbas (AS) yana cewa: "Aminci a gare ka ya kai bawan Allah nagari, mai biyayya ga Allah, da ManzonSa, da Amirul Muminina, da Hasan, da Husain (AS)." Wannan yana nuna tsarin alaƙar biyayya ta Hazrat Abbas wadda ta samo asali daga Allah har zuwa ga Imam Husain (AS).
Ya jaddada cewa akwai babban darasi a yau ga al'umma wajen gudanar da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna, da kuma yin biyayya ta tsagwaran gaskiya ga Waliyyul Faƙih a lokacin gaibar Imam Mahdi (AF).
Matsayar Jagora Kan Yarjejeniya Da Amurka
Limamin na birnin Qom ya yi ishara da saƙon da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya aika wa al'ummar Iran game da tattaunawar da aka yi, inda Jagora ya bayyana cewa: "A asali, ina da wata mahangar daban, amma domin alkawarin da Shugaban Ƙasa (kamar yadda yake Shugaban Majalisar Tsaron Ƙasa) ya yi min na kare haƙƙoƙin al'ummar Iran da rundunonin Gwagwarmaya (Jabhul Muƙawama) tare da ɗaukar nauyin hakan, na ba da izini. Kuma ya bayyana cewa idan ɓangaren Amurka yana son nuna fin ƙarfi ko ƙwazo na zalunci, ba za su amince da shi ba."
Ayatullah Sa'eedi ya jaddada cewa: "Duk da sanin cewa Amurka ba amintacciya ba ce, muna girmama matakin Jagora. Sannan kuma muna godiya ga bangaren shari'a na ƙasa wajen yaƙi da 'yan leƙen asiri da masu cin hanci da barna."
Darussa 4 Daga Suratul Fathi (Ayah ta 25) Domin Rayuwar Yau
A cikin hudubar farko, Ayatullah Sa'eedi ya karanta aya ta 25 a cikin Suratul Fathi wadda ke bayani kan Sulhun Hudaibiyyah, inda kafiran Makka suka hana musulmai shiga dakin Ka'aba, amma Allah ya kawo sulhu domin kare rayukan maza da mata muminai da ke ɓoye a cikin Makka waɗanda idan yaƙi ya ɓarke za su iya mutuwa. Ya fito da darussa guda huɗu kamar haka:
Darasi na Farko: Muhimmancin Kare Jinin Musulmi: Kare rayukan muminai ya fi karkashe kafirai muhimmanci. Ko da kare rayukan zai jinkirta samun nasara ta soja, kiyaye jini shi ne gaba. Wannan yana nuna Musulunci addinin zaman lafiya ne, ba na neman iko ba.
Darasi na Biyu: Auna Dukkan Bangarori Kafin Shiga Yaƙi: Dole ne jagorancin al'umma ya auna dukkan sakamako da tasirin da zai biyo baya kafin ba da umurnin yaƙi.
Darasi na Uku: Muhimmancin Yaƙin Yada Labarai (Yakin Riwayoyi): Kada musulmai su bar makiyansu su zama su ne ke fara ba da labari na karya ga duniya. Ta hanyar Sulhun Hudaibiyyah, Annabi (SAWA) ya nuna wa duniya cewa musulmai ba masu son yaƙi ba ne, ko da yake sun iya yaƙin.
Darasi na Haɗu: Nuna Kyawun Musulunci Ga Duniya: Jagoranci na hikima na Manzon Allah (SAWA) ya nuna lokacin da ya kamata a zare takobi da kuma lokacin da ya kamata a ajiye shi domin Musulunci ya yi kyau a idon duniya.
A ƙarshe, ya bayyana cewa a yau ma, jagoranci na hikima na Sayyid Ali Khamenei ne ya kawo mana nasara a gaban manyan azzaluman duniya, kuma muna ci gaba da jiran nasarar ƙarshe ta hanyar biyayya gare shi.
Ra'ayinka