A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da wannan jerin darussan na Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimomi masu alaka da Shugaban Zamani (Imam Mahdi) – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da gaggauta bayyanarsa – zuwa ga ku masu daraja da ilimi.
Daga cikin mafi muhimmancin hujjojin tabbatar da Wilayatul Faƙih akwai hadisai (nassosi). A fitowa ta baya, mun yi ishara da wata wasika (Tawƙi'i) da ta fito daga Imamin Zamani. A cikin wannan fitowar kuwa, za mu tattauna akan wata hujjata ta nassi daban.
Karbabben Hadisin Umar bn Hanzalata (Maqbulah)
Daya daga cikin hadisan da malaman fiƙihu suka dogara da su wajen tabbatar da Wilayatul Faƙih shi ne hadisin da Umar bn Hanzalata ya ruwaito.
Ya bayyana cewa: Na tambayi Imam Sadiƙ (AS): "Idan mutane biyu daga cikin mabiya (Shi'a) suka sami saɓani ko jayayya akan wani bashi ko gado, shin ya halatta su kai kararsu ko neman hukunci gurin sarki [azzalumi] ko kuma alkali [wanda sarki azzalumi ya nada]?"
Imam Sadiƙ (AS) ya amsa da cewa: "Duk wanda ya koma gare su domin neman hukunci... lallai ya koma gurin dagutu ne ya kuma amshe shi a matsayin mai yanke hukunci. Kuma duk abin da wannan sarkin ko alkalin nasa ya hukunta, haramun ne (ga wanda aka ba wa), ko da kuwa mutumin yana da gaskiya; domin ya amshi abin ne da hukuncin dagutu; wato wanda Allah ya yi umarni da a kafirce masa, kamar yadda Alkur'ani mai tsarki yake cewa:
«یرِیدُونَ أَنْ یتَحَاکَمُوا إِلَی الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ یکْفُرُوا بِهِ.»
"Suna son su kai hukunci gurin dagutu, alhali an umarce su da su kafirce masa." (Suratul Nisa'i/ 60)
Umar bn Hanzalata ya ce: "Yayin da na ga yadda Imam ya yi tir da kuma hana mabiya komawa gurin shugaban zalunci da alkalin sa da tsanani, sai na tambaya: "To me mabiya (Shi'a) za su yi a irin wadannan lokuta?"
Imam (AS) ya ce:
«یَنْظُرَانِ إِلَی مَنْ کَانَ مِنْکُمْ مِمَّنْ قَدْ رَوَی حَدِیثَنَا وَ نَظَرَ فِی حَلَالِنَا وَ حَرَامِنَا وَ عَرَفَ أَحْکَامَنَا فَلْیَرْضَوْا بِهِ حَکَماً فَإِنِّی قَدْ جَعَلْتُهُ عَلَیْکُمْ حَاکِماً فَإِذَا حَکَمَ بِحُکْمِنَا فَلَمْ یَقْبَلْهُ مِنْهُ فَإِنَّمَا اسْتَخَفَّ بِحُکْمِ اللَّهِ وَ عَلَیْنَا رَدَّ وَ الرَّادُّ عَلَیْنَا الرَّادُّ عَلَی اللَّهِ وَ هُوَ عَلَی حَدِّ الشِّرْکِ بِاللَّهِ.»
"Su dubi wanda yake a cikinku (mabiya) wanda ya kasance yana bayyana hadisanmu, yana duba cikin halal dinmu da haram dinmu, sannan yana sane da hukunce-hukuncenmu; sai su yarda da shi a matsayin mai yanke hukunci a tsakaninsu. Domin lallai ni na sanya shi a matsayin "Shugaba" (Hakim) a kanku. Idan kuwa ya yi hukunci da hukuncinmu amma ba a amsa daga gare shi ba, to lallai an walakanta hukuncin Allah ne, kuma an mayar da martani ne a gare mu. Kuma wanda ya mayar da martani a gare mu, ya mayar da martani ne ga Allah, kuma hakan yana matakin shirka da Allah). (Al-Kafi, Juzu'i 1, Shafi na 67)
A cikin wannan hadisi mai albarka, akwai muhimman batutuwa da suka shafi asasi kamar haka:
1. Haramcin Koma wa Azzalumi: A lokacin jayayya, bai kamata a koma gurin shugaban zalunci ko alkalin da ya naɗa ba; domin Alkur'ani da Sunnah sun haramta hakan.
2. Koma wa Masani: Imam Sadiƙ (AS) ya ce: "A irin wadannan lokuta su koma gurin mai ruwaito hadisi kuma masanin hukunce-hukuncenmu." A bayyane yake cewa babu wanda yake da cikakken ilimi na gaba-daya da hukunce-hukunce na Aimma (AS) face faƙihi (malami mai bincike da tace ilimi).
3. Faɗin Hukunci na Gaba-daya: A cikin wannan hadisi, asalin tambayar ta shafi jayayya ce tsakanin mutane biyu; amma Imam Sadiƙ (AS) a ƙarshen hadisin ya fadi wata ƙa'ida ta bai-daya da cewa: "Gaba-daya na sanya shi a matsayin shugaba (Hakim) a kanku." Da wannan bayani, Imam ya sanya faƙihi a matsayin "Shugaba" ga mabiya. Shugaba kuwa shi ne wanda yake da iko da gudanarwa a kan wasu da kuma tafiyar da al'amuransu.
4. Wajibcin Bin Umarni: Imam (AS) ya kara da cewa idan wannan shugaba da Imam ya naɗa ya faɗi hukunci, lallai ne a miƙa wuya kuma a amshe shi. Idan aka ƙi amsa, an ƙi amsar umarnin Imam ne, ƙin amsar umarnin Imam kuma ƙin amsar umarnin Allah ne. Da wannan faffadan bayani na Imam, ya mayar da faƙihi ya zama hujja ga mutane a cikin dukkan hukunce-hukunce – na daidaiku, na al'umma, na shari'a da ma wadanda ba na shari'a ba.
Shahararren malamin fikihun Shi'a, Muhammad Hasan al-Najafi, wanda aka fi sani da Sahibul Jawahir (ya rasu a shekara ta 1266H) ya ce: "Naɗin da aka yi wa faƙihi na bai-daya ne ya shafi dukkan al'amura; ta yadda duk abin da yake na Imam ne, to na faƙihi ne shima. Kamar yadda fadin Imam (Lallai ni na sanya shi a matsayin shugaba a kanku) ke nuna cewa faƙihi shi ne mai ikon gudanarwa a harkar shari'a da sauran al'amura na shugabanci. Kamar yadda ya zo a cikin wasika mai daraja ta Imamuz Zaman (A.F) cewa: (Lallai su hujjata ce a kanku). Ma'anar hakan ita ce faƙihi hujja ne a kan dukkan abubuwan da ni nake hujja a kansu, sai dai idan akwai wata hujja ta musamman da ta fitar da wani abu daban." (Jawahir al-Kalam, Juzu'i na 21, Shafi na 396 da 397).
Babban malamin fuƙaha, marigayi Sheikh al-Ansari (ya rasu a shekara ta 1281H) ya ce: "Abin da muke fahimta daga kalmar 'Hakim' (Shugaba) a cikin hadisin Umar bn Hanzalata, shi ne 'mai cikakken iko'. Wato fadin Imam: (Lallai ni na sanya shi a matsayin shugaba a kanku) yayi daidai da fadin 'Sarki ko Shugaba' lokacin da zai ce wa mutanen gari: 'Na sanya wane ya zama shugaba a kanku'. Daga wannan bayani ana fahimtar cewa sarki ya ba wa wannan mutum cikakken iko akan dukkan al'amura na gaba-daya da na ɗaiɗaiku na mutanen garin da suka shafi gudanar da gwamnati." (Qada wa Shahadat, Sheikh al-Ansari, Juzu'i na 22, Shafi na 8 da 9).
Daga abubuwan da suka gabata, a bayyane yake cewa "Faƙihi" ya amshi shugabancinsa ne daga Imam ma'asumi; domin a cikin wasikar Imamin Zamani (AS) da kuma hadisin Umar bn Hanzalata, Imam ne ya sanya faƙihi ya zama hujja da shugaba akan mutane. Don haka, faƙihi yana da ikon jagoranci ne da izini da umarnin Imam akan mutane.
Haka ne; karɓuwar faƙihi a gurin mutane da samun damar aiwatar da wannan jagoranci a aikace, ya dogara ne akan goyon baya da amincewar mutane gare shi da kuma karɓar shugabancinsa.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An ciro ne daga littafin "Negine Afarinesh" (Lu'u-lu'un Halitta), tare da ɗan gyara kaɗan.
* Umar bn Hanzalata yana ɗaya daga cikin sahabban Imam Baƙir da Imam Sadiƙ (A.S), kuma yana ɗaya daga cikin fitattun masu ruwaito hadisai waɗanda manyan malamai kamar Zurara da Hisham bn Salim da Safwan bn Yahya suka karbi hadisi a gurinsa. Kuma ma'anar "Maqbulah" (Karbabbe) ita ce hadisin da dukkan malamai suka yarda da shi kuma suka amshi ingancinsa.
Ra'ayinka