Asabar 16 Mayu 2026 - 22:49
Maƙiya Ba su da Ƙarfin Tsayawa Gaban Iran

Hauza/ Hujjatul Islam wal Muslimin Abdullah Haji Sadeghi, wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), bayan ziyarar duba kan iyaka a gundumar Baneh ya bayyana cewa yau a iyakokin Kurdistan, akwai ƙaƙƙarfan niyya ta kare tsarin Musulunci, sannan akwai kayan aiki, ƙwarewa da cikakkiyar shiri domin tunkarar duk wata barazana da ka iya tasowa.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza Hujjatul Islam wal Muslimin Abdullah Haji Sadeƙi, wakilin Jagoran Addini a Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), bayan ziyarar duba kan iyaka a gundumar Baneh ya bayyana cewa yau a iyakokin Kurdistan, akwai ƙaƙƙarfan niyya ta kare tsarin Musulunci, sannan akwai kayan aiki, ƙwarewa da cikakkiyar shiri domin tunkarar duk wata barazana da ka iya tasowa.

Wakilin Waliyyul Faƙih a rundunar IRGC ya kara da cewa: "Da farko ina son mika gaisuwa da godiya ga al’umma, mayaƙa da duk waɗanda ke aiki domin tabbatar da tsaron ƙasa a waɗannan yankuna, musamman a lardunan Kurdistan da Azarbaijan ta Yamma."

 Hujjatul Islam Sadeƙi ya ci gaba "Abin da muka gani a yau a waɗannan yankuna wata babbar alama ce ta ƙarfi, shiri da ƙwarewar dakarun da ke kare iyakokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ruhin jajircewa."

Da yake bayani kan imani da sadaukarwar al'ummar Iran da jami'an tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuwa cewa ya yi: "Tsaron da ƙasar ke morewa a yau sakamakon sadaukarwar dakarun tsaro da kuma jama’a ne. Muna gode wa Allah da Ya tarbiyyantar da al’ummar Iran da irin wannan ruhi; al’umma masu ƙwazo, masu ƙarfin hali da kuma shirye-shiryen kare addini da juyin juya hali da dukkan ƙarfinsu."

Hujjatul Islam Sadeƙi ya kara da cewa: "A ziyarar da muka kai a yau, mun ga ƙaƙƙarfan niyya a tsakanin dakarun da kuma cikakken shirin gudanar da aiki. Samun ƙarfi wani bangare ne kawai, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne niyyar amfani da wannan ƙarfi idan lokaci ya yi, kuma a yau wannan niyya tana akwai a cikin dakarunmu."

Ya ci gaba: "A cikin shekaru 47 da suka gabata, maƙiya sun sha gwada ƙarfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, amma Iran ta kasance mai nuna haƙuri da dattako, kuma ta nuna ƙaramin ɓangare ne kawai na ƙarfinta a lokuta daban-daban."

Da yake magana kan har yanzu Iran ba ta nuna dukkan karfinta ba ya ce: "Idan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yanke shawarar amfani da dukkan ƙarfinta da damar da take da su, maƙiya ba za su iya tsayawa a gabanta ba. An riga an ga wasu misalai na wannan ƙarfi a lokuta daban-daban wajen kare muradun ƙasa."

A ƙarshen jawabinsa ya bayyana: "Da wannan matakin na kasancewa a shirye, ƙarfi da cikakken tsaro, ina ganin maƙiya ba za su taɓa samun ƙarfin hali ko jarumtakar kai hari ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga wannan yanki ba, kuma tsaron da ake da shi a yau a iyakokin Kurdistan sakamakon wannan shiri da jajircewar dare da rana ne."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha