Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa jerin darussan Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, ana gabatar da shi ne domin yaɗa koyarwa da ma’arifofi da suka shafi Imam Mahdi (AJ) ga masu ilimi da masu sha’awar wannan fanni.
Lokacin ɓoyuwar (Gaiba) Imam Mahdi (A.S) lokaci ne na fitintinu, haɗari da karkacewa. Mabiyan Imam ɗin da yake Gaiba dole ne a cikin dukkan wahalhalu da sauye‑sauyen wannan zamani su kasance masu kare akidarsu, sannan su kula da halayensu kada su fita daga tafarkin bin Imam, su kuma fada cikin tarkon shaiɗanu.
Daya daga cikin muhimman hanyoyi shi ne addu’a da ƙara dangantaka da Allah, da kuma dangantaka da Imam, domin kada su manta da shi, kuma su ci gaba da haɗuwa da shi ta hanyar zikiri, addu’a da ziyara.
Imam Sadiƙ (A.S) ya ce:
«سَتُصِیبُکُمْ شُبْهَةٌ فَتَبْقَوْنَ بِلاَ عَلَمٍ یُرَی وَ لاَ إِمَامٍ هُدًی وَ لاَ یَنْجُو مِنْهَا إِلاَّ مَنْ دَعَا بِدُعَاءِ اَلْغَرِیقِ قُلْتُ کَیْفَ دُعَاءُ اَلْغَرِیقِ قَالَ یَقُولُ یَا اَللَّهُ یَا رَحْمَانُ یَا رَحِیمُ یَا مُقَلِّبَ اَلْقُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِی عَلَی دِینِکَ.»
“Za ku fuskanci wani shakku wanda zai sa ku kasance ba tare da wani jagora bayyananne ko Imam mai shiryarwa ba. Babu wanda zai tsira daga wannan shakku sai wanda ya roƙi Allah da Addu’ar Gariƙi (addu’ar wanda yake nutsewa).” Mai ruwaya ya tambaya: “Yaya wannan addu’a take?” Sai Imam ya ce: “Ka ce: Ya Allah! Ya Mai Rahama! Ya Mai Jin ƙai! Ya Mai juya zukata! Ka tabbatar da zuciyata a kan addininka.” (Kamal al‑Din, juzu’i na 2, shafi 351)
A cikin wannan addu’a an jaddada cewa a lokacin gaibar Imam wanda yake ɗauke da tutar shiriya, ya kamata mu yi addu’a domin tsayuwa da ƙarfi a kan addinin Allah, kuma wannan yana nuna muhimmancin addu’a sosai.
Imam Hassan Askari (A.S) ya ce:
«وَ اللَّهِ لَیغِیبَنَّ غَیبَةً لَا ینْجُو فِیهَا مِنَ التَّهْلُکَةِ إِلَّا مَنْ یثَبِّتُهُ اللَّهُ عَلَی الْقَوْلِ بِإِمَامَتِهِ وَ وَفَّقَهُ لِلدُّعَاءِ بِتَعْجِیلِ فَرَجِه.»
“Wallahi zai yi Gaiba mai tsawo, wadda babu wanda zai tsira daga halaka a cikinta sai wanda Allah ya tabbatar da shi a kan imani da imamancinsa, kuma ya ba shi ikon yin addu’ar gaggauta bayyanarsa.” (Bihar al‑Anwar, juzu’i na 52, shafi 23)
Ta wata fuskar kuma, yin addu’a domin Imam Mahdi (A.S) wani muhimmin nauyi ne ga masu jiran bayyanarsa, wanda Imamai (A.S) suka ba shi muhimmanci sosai. A cikin ruwayoyi an ruwaito cewa Imam Ridha (A.S) ya kasance yana umartar mutane su yi addu’a ga Sahibul Amr (Imam Mahdi), yana cewa ku yi masa addu’a da wannan lafazi:
«اللَّهُمَّ ادْفَعْ عَنْ وَلِیکَ وَ خَلِیفَتِکَ وَ حُجَّتِکَ عَلَی خَلْقِکَ….َ وَ احْفَظْهُ مِنْ بَینِ یدَیهِ وَ مِنْ خَلْفِهِ وَ عَنْ یمِینِهِ وَ عَنْ شِمَالِهِ وَ مِنْ فَوْقِهِ وَ مِنْ تَحْتِه….َ أَیدْهُ بِنَصْرِکَ الْعَزِیزِ وَ أَیدْهُ بِجُنْدِکَ الْغَالِبِ …..وَ وَالِ مَنْ والاهُ وَ عَادِ مَنْ عَادَاهُ…»
“Ya Allah! Ka kare waliyyinka kuma khalifanka da hujjarka a kan halittarka… Ka tsare shi daga gaba da baya, daga dama da hagu, daga sama da ƙasa… Ka taimake shi da nasararka mai ƙarfi, ka ƙarfafa shi da rundunarka mai rinjaye… Ka so duk wanda yake son sa, ka kuma yi gaba da duk wanda yake gaba da shi.” (Bihar al‑Anwar, juzu’i na 92, shafi 330)
Saboda haka, yin addu’a da ƙulla alaƙa ta ruhaniya da Imamuz Zaman na daga cikin ka’idojin halayen ƴan Shi’a a lokacin gaiba, kuma yana da fa’idodi da tasiri masu yawa.
Ana iya raba addu’o’i da ziyarorin Mahdawiyya zuwa kashi biyu:
• Na farko: Addu’o’i da ziyarori da aka ruwaito daga Imam Mahdi (A.S) da kansa, waɗanda suka iso ga Shi’a a lokacin (Gaiba Sughra) ta hanyar wakilan Imam na musamman; kamar Ziyarar Aal‑Yasin da Addu’ar Faraj.
• Na biyu: Addu’o’i da ziyarori da aka ruwaito daga sauran Ma’asumai (A.S) game da Imam Mahdi; kamar Addu’ar Ahd da Ziyarar Sahib al‑Amr (A.S) a Sardab mai tsarki na Samarra.
Yin addu’a ga Imam Mahdi (A.S), yin tawassuli da shi da kuma ziyartar wannan babban Imam ba su da takamaiman lokaci ko wuri. Shi’a da masu jiran bayyanarsa na iya yin magana da shi a kowane lokaci da kowane wuri, su aika masa da salati da gaisuwa, su kuma sabunta alkawarinsu da shi. Duk da haka, a cikin ranakun mako, ranar Juma’a – bisa ruwayoyi – an danganta ta musamman da Imam Mahdi (A.S). Saboda haka an ruwaito wata ziyara ta musamman domin wannan rana, wadda ake kira Ziyarar Imam Mahdi (A.S) a ranar Juma’a.
A cikin littattafan addu’o’i da ziyarori da manyan malamai na Shi’a kamar Sayyid Ibn Tawus, Allama Majlisi da Sheikh Abbas Qumi suka rubuta, an ruwaito addu’o’i da ziyarori masu yawa game da Imam Mahdi (A.S). Wasu daga cikinsu sun samu kulawa ta musamman daga waɗannan malamai kuma sun fi shahara a tsakanin Shi’a.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba…
An ɗauko daga littafin “Nagin Afrinesh”, tare da ɗan gyara kaɗan
Ra'ayinka