A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da jerin bahasoshin Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, da nufin yaɗa koyarwa da ma’arifa da suka shafi Imam Mahdi (AJ) gare ku masu ilimi da fahimta.
Daya daga cikin barazanar da ke fuskantar ma’arifar Mahdawiyya shi ne bayyanar masu iƙirarin ƙarya a wannan tafarki mai tsarki. A tsawon shekarun Gaiba (ɓoyuwa) na Imam Mahdi (AS), wasu mutane sun yi iƙirarin ƙarya cewa suna da alaƙa ta musamman da shi ko kuma an ba su matsayin wakilci na musamman daga gare shi.
Imam Mahdi (AS) a wasikarsa ta ƙarshe zuwa ga wakilinsa na huɗu, Ali bin Muhammad al‑Samari, ya bayyana cewa:
«یَا عَلِیَّ بْنَ مُحَمَّدٍ اَلسَّمُرِیَّ أَعْظَمَ اَللَّهُ أَجْرَ إِخْوَانِکَ فِیکَ فَإِنَّکَ مَیِّتٌ مَا بَیْنَکَ وَ بَیْنَ سِتَّةِ أَیَّامٍ فَاجْمَعْ أَمْرَکَ وَ لاَ تُوصِ إِلَی أَحَدٍ یَقُومُ مَقَامَکَ بَعْدَ وَفَاتِکَ فَقَدْ وَقَعَتِ اَلْغَیْبَةُ اَلثَّانِیَةُ فَلاَ ظُهُورَ إِلاَّ بَعْدَ إِذْنِ اَللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ وَ ذَلِکَ بَعْدَ طُولِ اَلْأَمَدِ وَ قَسْوَةِ اَلْقُلُوبِ وَ اِمْتِلاَءِ اَلْأَرْضِ جَوْراً وَ سَیَأْتِی شِیعَتِی مَنْ یَدَّعِی اَلْمُشَاهَدَةَ أَلاَ فَمَنِ اِدَّعَی اَلْمُشَاهَدَةَ قَبْلَ خُرُوجِ اَلسُّفْیَانِیِّ وَ اَلصَّیْحَةِ فَهُوَ کَاذِبٌ مُفْتَرٍ.»
“Ya Ali bin Muhammad al‑Samari! Allah Ya ƙara wa ‘yan’uwanka lada game da kai. Lallai za ka rasu cikin kwanaki shida. Ka tattara al’amuranka, kuma kada ka yi wasiyya ga kowa ya maye gurbin ka bayan rasuwarka. Domin lallai Gaiba ta biyu ta tabbata, kuma babu bayyana sai da izinin Allah Maɗaukaki. Wannan kuwa zai zo ne bayan tsawon lokaci, taurin zukata, da cikar duniya da zalunci. Kuma nan gaba wasu daga cikin Shi’ata za su zo suna iƙirarin sun gan ni (ko suna da alaƙa ta musamman). To, duk wanda ya yi iƙirarin ‘ganawa’ kafin fitowar Sufyani da ƙarar sama, to shi maƙaryaci ne mai ƙirƙira ƙarya.” (Kamal al‑Din, juzu’i 2, shafi 516)
Da wannan bayani, ya wajaba ga kowane Shi’a mai hankali ya ƙaryata masu iƙirarin alaƙa ko wakilci na musamman, ya kuma rufe hanyar da waɗannan masu son duniya da damfara ke bi don yaudarar mutane.
Wasu daga cikin waɗannan maƙaryata sun zarce iyaka; bayan iƙirarin wakilci, sai suka yi iƙirarin cewa su ne Mahdi, suka kafa ƙungiyoyi da mazhabobi masu ɓata hanya. Ta hanyar wannan iƙirari na ƙarya, sun jawo mutane da dama cikin karkacewar aƙida. Tarihin waɗannan ƙungiyoyi ya nuna cewa da dama daga cikinsu sun samu tallafi daga hannun masu mulkin mallaka, kuma da wannan tallafi ne suka rayu da ci gaba.
A bayyane yake cewa samuwar waɗannan ƙungiyoyi masu ɓata hanya da amincewar mutane da su, ya samo asali ne daga jahilci da rashin sani.
Ƙaunar ganin Imam (AS) ba tare da isasshiyar ma’arifa da fahimta ba, tare da sakaci da kasancewar ‘yan damfara a wannan fage, na iya kai mutum ga fadawa hannun masu iƙirarin ƙarya.
Saboda haka, Shi’awa masu jira (muntazirun) dole ne su ƙarfafa kansu da ilimi mai inganci game da ma’arifar Mahdawiyya, su kare kansu daga tarkon masu yaudara, kuma su bi tafarkin malamai nagari masu kishin addini domin tafiya a kan hanya madaidaiciya ta mazhaba.
Bayani:
(1) Ma’anar “ganawa (mushahada)” a nan shi ne iƙirarin wakilci (wato ya ce shi wakilin Imam ne), ba kawai ganin Imam ba.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba…
An ciro daga littafin “Negine Afarinish”, tare da ɗan gyara.
Ra'ayinka