Lahadi 10 Mayu 2026 - 20:18
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (26) | Wasu Daga Cikin Siffofin Raj’a

Hauza/ Ga dukkan muminai da masu jiran bayyanar Imam Mahdi (AS) na gaskiya waɗanda suka rasu kafin bayyanarsa, akwai yiwuwar su dawo duniya domin su taimaki wannan Imami.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, ana gabatar da jerin tattaunawa kan Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, da nufin yada koyarwa da ma’arifa da suka shafi Imam Zaman (AJ), ga ku masu daraja.

Daga cikin riwayoyi masu yawa ana iya bayyana waɗannan bayanai game da raj’a:

1. Raj’a na daga cikin manyan ranaku masu muhimmanci na duniya, waɗanda ake kira “Ayyamullah” (Ranakun Allah).

Imam Ja'afar as‑Sadiƙ (AS) ya ce:

«أَیَّامُ اَللَّهِ ثَلاَثَةٌ یَوْمٌ یَقُومُ اَلْقَائِمُ عَلَیْهِ السَّلاَمُ وَ یَوْمُ اَلْکَرَّةِ وَ یَوْمُ اَلْقِیَامَةِ.»  

"Ranakun Allah guda uku ne; ranar da Qa’im (Imam Mahdi) zai tashi, ranar raj’a, da ranar Kiyama." (Bihar al‑Anwar, j. 53, sh. 63)

2. Imani da raj’a yana daga cikin alamomin mabiyan Ahlul‑Baiti (AS).

Imam Ja’afar as‑Sadiƙ (AS) ya ce:

«لَیْسَ مِنَّا مَنْ لَمْ یُؤْمِنْ بِکَرَّتِنَا.»  

"Ba ya cikinmu wanda bai yi imani da komawar mu (raj’a) ba." (Bihar al‑Anwar, j. 53, sh. 92)

3. Raj’a ba ta shafi kowa ba, kamar yadda Imam Ja’afar as‑Sadiƙ (AS) ya ce:

«إِنَّ اَلرَّجْعَةَ لَیْسَتْ بِعَامَّةٍ وَ هِیَ خَاصَّةٌ لاَ یَرْجِعُ إِلاَّ مَنْ مَحَضَ اَلْإِیمَانَ مَحْضاً أَوْ مَحَضَ اَلشِّرْکَ مَحْضاً.»  

"Raj’a ba ta shafi dukkan mutane ba; tana keɓanta ne ga waɗanda suka tsarkake imaninsu gaba ɗaya ko kuma waɗanda suka tsarkake shirka gaba ɗaya." (Bihar al‑Anwar, j. 53, sh. 39)

4. Daga cikin muminan da za su dawo duniya akwai Annabawa da Imamai masu tsarki (AS), kuma Imami na farko da zai dawo duniya a lokacin raj’a bayan Imam Mahdi (AS) ya kafa gwamnati ta adalci ta duniya shi ne Imam Hussain (AS), wanda zai yi mulki na shekaru masu yawa. Imam Ja’afar as‑Sadiƙ (AS) ya ce:

«أَوَّلُ مَنْ یَرْجِعُ إِلَی اَلدُّنْیَا اَلْحُسَیْنُ بْنُ عَلِیٍّ عَلَیْهِ السَّلاَمُ فَیَمْلِکُ حَتَّی یَسْقُطَ حَاجِبَاهُ.»  

"Na farkon wanda zai dawo duniya a raj’a shi ne Husain ɗan Ali (AS), kuma zai yi mulki har sai saboda tsufa gashin girarsa ya sauko ya rufe idanunsa." (Bihar al‑Anwar, j. 53, sh. 46)

5. Ga dukkan muminai da masu jiran bayyanar Imam Mahdi (AS) na gaskiya waɗanda suka rasu kafin bayyanarsa, akwai yiwuwar su dawo duniya domin su taimake shi.

An ruwaito daga Imam Ja’afar as-Sadiƙ (AS) cewa duk wanda ya karanta Dua al‑Ahd na kwana arba’in zai kasance daga cikin mataimakan Qa’im ɗinmu (AS), kuma idan ya rasu kafin bayyanarsa, Allah zai fito da shi daga kabari domin ya kasance a hidimar Imam Mahdi (AJ).  

(Mafatih al‑Jinan, gabatarwar Dua al‑Ahd)

Wani ɓangare daga Dua al‑Ahd:

«... اللّٰهُمَّ إِنْ حالَ بَیْنِی وَبَیْنَهُ الْمَوْتُ الَّذِی جَعَلْتَهُ عَلَیٰ عِبادِکَ حَتْماً مَقْضِیّاً فَأَخْرِجْنِی مِنْ قَبْرِی ...»  

"...Ya Allah, idan mutuwa wadda Ka sanya a kan bayinka a matsayin hukunci tabbatacce ta shiga tsakanina da shi (Imam Mahdi), to ka fitar da ni daga kabarina, alhali ina sanye da likafina." (Mafatih al‑Jinan; Bihar al‑Anwar, j. 99, sh. 111)

6. Kafurai da munafukai ba za su dawo duniya da son ransu ba, sai dai za a tilasta musu raj’a; amma raj’ar muminai tana da alamar kasancewa bisa zabinsu.

Imam Ja’afar as‑Sadiƙ (AS) ya ce:

«إِذَا قَامَ أُتِیَ اَلْمُؤْمِنُ فِی قَبْرِهِ فَیُقَالُ لَهُ یَا هَذَا إِنَّهُ قَدْ ظَهَرَ صَاحِبُکَ فَإِنْ تَشَأْ أَنْ تَلْحَقَ بِهِ فَالْحَقْ وَ إِنْ تَشَأْ أَنْ تُقِیمَ فِی کَرَامَةِ رَبِّکَ فَأَقِمْ.»  

"Lokacin da Imam Mahdi (AS) ya tashi, manzannin Allah za su zo wa mumini a cikin kabarinsa su ce masa: “Ya bawan Allah! Ubangidanka ya bayyana. Idan kana so ka bi shi ka same shi, ka je; idan kuma kana so ka zauna cikin ni’imomin Ubangijinka (na barzahu), ka zauna.” (Al‑Ghayba, Shaykh Tusi, j. 1, sh. 458)

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ɗauko daga littafin “Negine Afarinesh”, tare da ɗan gyara kaɗan.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha